Tashin Farashi Ne Ya Sa Mu Shiga Yajin Aiki



Download 141,07 Kb.
bet3/6
Sana02.03.2017
Hajmi141,07 Kb.
#3696
1   2   3   4   5   6

Nau’o’in Dinosaurs:

Halittun sun kasu ne zuwa manyan nau’o’i 2; Megalosaurus daIguanodon. A siffar jiki kuma, fasalin kadangare ko kuma damo, Allah ya musu; kuma manya-manya ne ainun. Don girman jikin ko wane daya a cikinsu, ya kai girman mota tanka mai tayu goma sha wani abu din nan, ko kuma, gwari-gwari, a ce tirela. Hakwaren Iguanodon, bisa tsari da kuma siga, sun nuna cewa dabba ce da abincin ta tsirrai ne; yayin da na Megalosaurus kuma, ya alamta cewa cimakanta, nama ne.

Gabakidaya dai, an samu jinsunan dinosaurs a fadin duniyar wancan lokacin, har guda 5, kamar yadda al’ummar bani Adama ta kasu zuwa jinsuna da dama a yau. Wadannan jinsuna kuwa, su ne; Ornithischia, da Saurischia, sai kuma theropods; kazalika kuma an yi jinsin ankylosaurs; sai kuma jinsin pachycephalosaurs, da ceratopsians. A cikinsu, masu tu’ammali da nama a matsayin zaunannen abincin su. Suna kuma taushe masu cin tsrrai din nan ne don kau da ’yar gusau. Akwai kuma wani jinsin wadannan halittu da siffar su ta fi kama da ta jemagen da aka sani a yau. Wannan jinsin dinosaurs din, duk kasancewar su damfara-damfara ne ainun, da ko wane daya daga cikinsu ya yi tsawon mita 12, nauyinsa kuma kimanin tan 5, yana tashi sama. Sannan kuma yana da zaka-zakan kumbunan da sun fi na mikya, nesa ba kusa ba. Su ma dai, maciya nama ne don maganin ta-bahuwa.

Har ila yau kuma, a wancan zamanin, an yi wani nau’in dinosaurs da a kimiyyance ake ce da su POSAUROPODS.


Manufar Rayuwa: Kyauta da Rowa

Mai karatu a wannan makon zan tabo wasu muhimman abubuwa guda biyu, wadanda ke kishiyantar juna. Kuma dukkaninsu na da alaka da rayuwarmu ta yau da kullum.

A baya hankali na bai taba zuwa kan wadannan abubuwa ba, saboda ko kadan kwakwalwata ba ta salwanta min muhimmancinsu da kuma tasirinsu a rayuwa ba. Wasu lokuta baya mu na darasi, sai malaminmu ya shigo da batun ‘Kyauta da rowa’, ya yi mana dogon bayani (wanda shi a wurinshi ya takaita). Har ma ya sha alwashin in Allah ya yarda zai yi nazari a kan kyauta da rowa.

Kafin na ci gaba da bayani, akwai wani abu mai sarkakiya wanda ya kamata mu warware shi. Shin kyauta ko rowa a na yin gadonsu ne, ko kuwa koyonsu a ke yi?

Wannan tambayar ba ta da wani bambanci da tsohuwar tattaunawar nan dangane da dabi’ar dan Adam, wanda wasu ke hakikancewa a kan cewa ai dabi’a ta na tattare ne a cikin jininmu, daya bangaren kuma su ka ce, a na koyon dabi’u ne a cikin al’umma.

Idan mutum na da yawan kyauta, za ka ji hausawa na cewa ya na da jinin kyauta. Sai dai wannan karin magana kadai bai isa madogara gare mu ba, mu yanke hukuncin cewa ai in dai mutum ya hada jini da masu kyauta babu makawa shi ma zai zamo mai kyauta.

Wannan rusasshen zance ne, idan za mu yi la’akari; misali akwai tagwaye (twins) wadanda a ka haifa a garin Kaduna. Sunansu Hasan da Husaini, tun bayan kwana bakwai da haihuwansu, sai mahaifinsu ya yanke shawarar zai raba su wurare daban daban a hannun kannenshi.

Da a ka tashi sai a ka kai Hasan kasar Ingila, shi kuma Hussaini a ka kai shi garin Gombe. Har zuwa lokacin da su ka girma su ka fara aiki. Abun lura a nan shi ne, idan Hasan da ke kasar ingila ya taso tare da mutane masu ra’ayin turawa na cewa taimakon talaka kuskure ne, saboda idan yau ka taimaki talaka ba zai mike ya nemi na kanshi ba. Shi kuma Husainin ya taso a wurin mutanen Gombe, wadanda za su iya sadaukar da dukkan abun da ke cikin aljihunsu domin yin hidima ga bako, ko kuma mutanen da ke fito da abinci kofar gida a taru a ci.

Wannan ya nuna mana a fili cewa Hasan zai koyo rowa matsananciya, shi kuma Husaini zai koyo yadda a ke kyautata ma mutane. Wannan dan gajeren misali kadai ya isa mu gane karfin ikon wurin da mutum ya taso ga halayyenshi, musamman halin kyauta ko rowa.

Tun a rayuwarmu ta yau da kullum mu kan ga alheran da ke tattare da kyauta, haka kuma mu kan ga sharrrukan da ke tattare da rowa. Mutumin da ke da kyauta, ya kan zama mafi soyuwa a tsakanin mutane, sannan mutane ba za su aminta a hada kai da su wurin cutar da shi ba.

Akasin haka ga marowaci. Idan mai gida (oga) ya kasance marowaci, babu makawa da yaranshi (ma’aikata) za a hada baki a halaka shi ko a gurgunta al’amuranshi. Saboda ai tsaro ba ya na nufin mai gadi da bindiga ba ne kawai, mafi girman tsaro shi ne tsaro wanda mutum ya samarwa kanshi ta hanyar mallakar zukatan wadanda ya ke tare da su. Idan kai mai arziki ne, amma ma’aikatanka ko da yaushe su na cikin matsanancin wahala. Kenan watan wata rana makiya za su iya ba mai dafa mishi abinci (kuku) guba ya zuba mishi don ya ci ya halaka.

Sirrin cin moriyar rayuwa na tattare da kyauta. A wasu lokutan ma kyautar da mutane ke yi kanana su na ganinsu ba a bakin komi ba, amma wannan abun alheri zai ci gaba da binsu har ‘ya ‘ya da jikoki.

Idan kuwa halin ka kenan rowan tsiya, wannan tabon na marowaci, ya yi ta binka kenan. Har ma idan a ka ci sa’a cikin ‘ya ‘yanka ko jikoki a ka samu wani mai halin kyauta, sai ka ji jama’a na cewa Allah sarki mahaifinshi ko Kakanshi marowaci, amma shi kuma mai kyauta.

Abubuwa biyu ne masu karo da juna. Sai dai ya na da kyau mu gane cewa wadannan halaye guda biyu, al’umma na da hakkin koya wa mutum su. Idan mu ka kasance masu halin kyautatawa, ‘ya ‘yanmu da wadanda ke tare da mu za su taso da wannan hali. Shi ya sa masana halayyan jama’a da zamantakewa su ke cewa al’umma ne ke gina dabi’ar mutum. Mu hadu a mako mai zuwa.



Tare da

ISB Daurawa

GSM: 07036666850

isbdaurawa@yahoo.com

Dandalin Ma’aurata:

Shin Kishiya Laifi Ce?

Subhanaka ya Allah!

Allah Subhanahu wa Ta’ala yana fada a cikin Alkur’ani, Suratul Nisa’i, Aya ta Uku: “Ku aura daga abubuwan da suka muku dadi na daga mataye bibiyu ko uku uku ko hurhudu, amma in kun ji tsoron rashin adalci, sai ku auri daya ko abin da hannunku ya mallaka (kuyanga)...”


Ina yan’uwana mata, yau filin naku ne ku kadai. Yau dai kam na san zan maku laifi! Yau na san za ku ji maganata ba dadi, amma ku yi duba cewa ita gaskiya daya ce kuma mu sani cewa Allah ya fi mu son kanmu da kanmu. Don haka ma ya ce ba ya dora wa wata rai abin da ba za ta iya ba.

Maganata a kan mata yan’uwana a wannan satin kan wannan abar ne da ba’a so wato, Kishiya.

Tambayata a nan ita ce: Shin Kishiya Laifice? Da farko dai bari na bayyana mene ne laifin? Sannan wace ce Kishiya?

Kishiya tana daukar abokin tarayya a wasu al’amura na rayuwa. Ko kuma a ma’ana kyakkyawa ta bangaren auratayya wato abokiyar zama mataimakiya a al’amuran zamantakewar aure.

Liafi: Ana kiran duk wani abu da yake ba a kan doron Shari’ah ba da laifi ko kuma duk abin da ya kaucewa addini.

To, mun ga kowanne bayaninsa. Bari mu je ga gundarin batun, shi ne me ya sa ‘yan’uwana mata muka dauki Kishiya da zafi kamar wani laifi, ko tashin hankali? A fahimtata akwai abubuwa kala kala da zan iya jero su.

1. Akwai karancin ilmin addini da rashin sanin wane ne Allah (SWT). Dalili da mace ta san wan nee Ubangijinta (SWT) ta san yadda yake sonta, da ko da wasa ba za ta dauki abin da ya halatta wani laifi mai tsanani ba da har za ta iya kowanne aiki don hanawa.

2. Rashin tarbiyya daga iyaye domin na lura yawancin mata masu tsananin kishi mara ma’ana sun samo shi ne daga iyayensu, wanda yawancin irin wannan matan za ka tarar iyayensu ba su kadai ba ne a gidan mahaifinsu.

3. Zugar Kawaye - Ita ma wata hanyace dake lalata wa mata tunani da hange a kan abokiyar zama har suna dauka in aka kawo masu ita to karshen rayuwarsu ya zo.

4. Rashin tawakkali da Allah domin da mace ta yarda da cewa duk wanda ya yi tawakalli gare shi, ya isam masa, to da ba Kishiya ba ko waye a fadin duniya ba zai ba ta tsoro ba.

5. Rashin hangen gobe da mace za ta rika duba da yanayin zamani da fadar Manzon Allah (s.a.w) cewa, ‘Karshen duniya mata za su fi yawan maza da ba za ta ki a kawo mata abokiyar zama ba, saboda in kin ki, ba ki tunanin yaranki da kannenki?’
Kishiya A Hangen Mata ‘Yan’uwana: Da yawa a yau mata musamman matasa, saboda dalilan da na zayyano a sama, sun dauki Kishiya wata bala’i wata annoba, mai kare dangi don haka suka ja damara suka daure kugu suka mata shirin ko-ta-kwana. Wanda wannan shirin ya jawo matsaloli da dama ga rayuwar mata, musamman na mu na Musulmi ‘yan Arewa. Daga cikin gurbataccen tunanin da wasu jahilan al’umma ke cusawa mata shi ne Kishiya fa in ta zo, za ta raba ki da mijinki da yaranki ne.

Abin mamaki sai ka ga mace ta yarda ta tashi tsaye wata tabi ta hanyar Shirka kamar yanda na san mun sha samun labaran irin wasu lamuran ma mun gani da idanunmu yadda mata ke asirce-asirce da Shirka kala-kala don hana namiji aure.

Misali babba shi ne wani faifan Bidiyo da aka gano wata mata ta yi binne-binne a makabarta har da rubuta “Allah ka raba mijina wane da matarsa wance, kamar yanda ka raba na cikin kabarin nan da rayuwarsa.” Wa-iyazubilillah.

Za ka tarar wata kuma ta haukata Kishiyar, ko ta jefe ta da wata cutar, wanda yawanci masu rukiyya shaida ne a kan irin wadannan abubuwan.

Akwai wata kuma da ni shaida ce a kan lamarinta. Mijin ta yi wa daurin baka in yaje ga amaryar, sai ya zama ba namiji ba, amma idan ya dawo gare ta, sai ya samu karfi. An dade ana dauki-ba-dadi kafin ya samu lafiya.

To irin wannan matan sun dade a duniya kuma ba yau aka fara ba, da yake tun da akwai masu karancin ilmin addini da karancin tauhidi kuma har yau akwai amsu matsalar.

To amma a yau fa da ilmi ya yi karfi wayewa ta yi yawa. Me ya jawo zafin kishi ya fi na da karfi? Eh ya fi na da karfi nesa ba kusa ba, domin mata a yau ba a asiri kadai suka tsaya ba, ta kai da cewar in mace ta ga mijinta da gaske yake auren nan ba fashi za ta yaye zani ta zira wando ta zage damtse ta zama namiji ta kowacce hanya karfi da yaji, sai ta hana mijinta aure ko kowa ya rasa.

A yau ne da ilmi da wayewa suka bunkasa, amma za ka ji mace ta datsewa mijinta gaba, don zai yi aure, ko ta cinna masa wuta, ko ta ware makwogwaro tana zagin mijinta, ta uwa, ta uba. Ko suna dambe saboda kawai zai yi aure. Kar fa ku ce jahila ko mara ilmi, mafi yawan masu aikata hakan da ilminsu da komai, amma ta bari an gurbata mata tunani cewa wannan da za ta zo masifa ce a gare ta.


TO YAN’UWA MATA TAMBAYA TA BIYU GARE KU...

Shin Kishiyar da Allah ya halatta ya halatta ne don ya cutar da ku? Shin kuna ganin wanda ya samar da ku, Ya raya ku, Yake ba ku abinci, ya fi ku sanin abin da ya dace da ku zai cutar da ku? Shin ba ku yarda cewa komai na Allah yana da ma’ana ba? Shin kuna ganin auren da ya halattawa mazajenku bai da ma’ana?

To bari ki ji, ko kin ki ko kin so Kishiya mataimakiya ce a abubuwan rayuwarki da dama musamman, harkar auratayya domin wani namijin ba zai iya hakurin kwana uku ba mace kusa da shi ba. Mu mata masu matsaloli duk watan duniya, wata ta kan kai kwana bakwai tana al’ada wata inta haihu sai ta yi kwana arba’in jini, bai yanke mata ba, ina kike so mijinki ya je. Wannan cutuka na zamani dake yawo idan har ya dauko miki ita, ke da shi za ku mutu, yaranku ba lallai su samu ba, amma ki sani wallahi kin bar masu abin magana iyakar rayuwarsu.

In kina ganin in miji ya auro miki wata kin kaskanta shin kin kai matan Annabi (s.a.w) da suka fi kowace mace matsayi, wanda matsayinsu ya sa Ubangiji ya kira su iyayen al’umma bayan Annabi (s.a.w)bai halatta ga kowane namiji ya aure su ba amma suka zauna da kishiyoyi.

In sharrin sihiri kike tsoro Ubangiji (SWT) kafin Ya halicce ki, Ya san cewa akwai sihiri kuma yana yiwuwa ya same ki don haka Ya turo Annabinsa (s.aw.) gare ki domin ya koyar dake addu’o’in kariya kuma ya ce miki ki roke shi zai amsa miki.

Ki sani Ubangijinki (SWT) bai kaddara miki Kishiya ba face don ya jarrabe ki kuma jarabawar Allah karin girma ce ga bayinSa. Ki yi hakuri ki cinye jarabawar da ya miki a duniya domin a lahira ki samu babban rabo.


Tsaraba Ga ‘Yan’uwanmu Maza:

Maza ku ji tsoron Allah yayin karin aure domin ko da Allah ya halatta muku sai da ya kafa muku sharudda karawar, wadanda suka hada da ADALCI, adalci adalci!!! wanda shi ma adalcin fa abu ne mai fadi, ba wai kawai zan iya saya masu kaya ko ba su abinci iri daya shi ne adalci ba.

Malamai a taimaka mana da sanar da mazajenmu hakikanin adalci a aure. Ina fatan ubangiji ya ba mu hakurin zama da abokan zamanmu domin samun tsira duniya da lahira.

Tare da
Fatima Ahmad Buba (+989380996801)


Sana’a Sa’a: Mene Ne Sinadaran Karin Ni’ima Ga Mata?

Ganin yadda wannan shafin ya samu karbuwa gare ku ‘yan’uwana mata, kafin mu dora daga inda muka tsaya, za mu karasa tambayoyin da kuka aiko mana.

Ga wadansu daga cik...
Tambaya: Shin Allah ya faranta miki duniya da lahira, amin haihuwata biyu amma wallahi ba ki ga yadda nonona ya koma ba. Duk ya yamutse don Allah ki taimaka min da hadin da zan yi ya ciko ya yi kyau. Allah ya saka da alheri.

Daga Maman Latifa.



Amsa: Maman Latifa idan kina biye da mu a satin da ya gabata na yi bayanai da dama kan maganin gyaran nono. Amma yanzu ma zan kara maki wasu:

1. Ki samu albasa madaidaiciya ki yanyanka sai ki saka a tukunya da ruwaki ta fasa shi sosai har sai ruwan ya koma baki, sai ki juye ruwan ki sami zumar ki mai kyau inda yi daya, garin gero ludayi daya, madarar PEAK na gwangwani daya na ruwa sai ki juye su kan ruwan tafasashen albasan nan ki sha, amma fa kar ki bari ya wuce a wa 24 baki shanye ba, in Allah ya yarda in za a samu biyan bukata. Allah Ya sa mu dace.

2. Ki sami aya, gyada, ayaba (plantain) da alkama sai madara, zaki wanke ayarki sai ki hada da gyadarki ki markada su ki tashe, already kin yanyanka plantain dinki kin busar kin yi gari da shi kin tankade sai ki rika diban garin plantain din kina hadawa da ruwan ayaba gyadarki kina sa madarar PEAK ta ruwa kina sha, zai gyara nono da yardar Allah.
Tambaya: Aslam, malama Jummai ina da tambaya, idan mijina yana tarawa da ni ba na jin dadin shi ma baya in dadi. Ina neman taimako. Daga Zainab Adamawa.
Tambaya: Salam, malama don Allah ni matsalata mijina ba yi da kuzari kuma baya dadewa idan muna tarawa, ko mene ne maganin kara wa nami ji kuzari ko jimawa yayin jima’i da kuma yawan sha’awar iyali. Nagode Talatu Gombe.
Tambaya: Assalam malama Jummai, Allah ya kara miki albarka da fahimta don Allah ina da karancin ruwan gaba kuma duk lokacin da na sa du da miji na sai naga baya fita hayyacin sa kamar yadda na ke jin sauran mata suna fada a hira koma minasha idan muka sayi kayan da’a ni da kawayena sai dai na ji kowa na tofa albarkacin bakinsa, malama har na daina saye don Allah ki taimaka min da abin da zan yi daga Fatima Zamfara.

Amsa: Zainab, Fatima, da Talatu zan amsa maku amsoshinku gaba daya na baku a tare, ku sani cewa wadannan abubuwan da zan lissafo suna da matukar muhimmanci da amfani ga jikin mace hade da samun karin ni’imar sune kamar haka:

1. Tuffa (Apple) matsayinta a jikin ki zai kara miki ni’ima a jiki har kasauki kuma jikinki ya ringa laushi yana kyau ba kamar wasu matan ba inka taba jikinsu ka ji tauri.

2. Ruwan abarba: Shi ma yana da kyau mace ta rinka markadawa tana tacewa tana sha da sugar ko zuma.

3. Rake: shi ma yana karawa mace ni’ima kuma yanada amfani matuka a jiki, yanda yake da zakinan da ruwa to haka mace zata ringa jin ni’imarta na karuwa.

4. Aya: Shi ma duk tafiyar su daya da rake, ayar anaso irin bula-bulanan tana da matukar muhimmanci gurin mace tana da ni’ima kubar rainata hakama kunun aya idan yaji madarar peak.

5. Zaitun: man zaitun yana magunguna da yawa to anaso ki ringa shafashi ajikinki yana gyara fata dasaka sautsi jiki, hakama yanada kyauki dinga shafawa a gabanku, yana saka laushi hakama idan mai gida yana iya shafawa.

6. Bawon bagaruwa: Shi kuma wani sirri ne wanda idan mace na son ta zama kullum a tsuke kamar sabuwa ta dunga dafa bawon ta na shiga kamar yanda ake shiga ruwan dumi in kin haihu.

7. Tsumi: akwai tsimi mai kyau da mara kyau mara kyau yana tsinka jikin mace wata har jini yake sata na ba gaira ba dalili. Ga hadin tsumi ki yi da hannun ki yafi kyau ki nemi sasaken baure, kananfari, zuma, citta, mazarkwaila. Za ki tafasa sasaken baure ya dahu sosai sai ki daka kanumfari me yawa da citta yar kadan ki zuba akai, ki saka mazarkwailan da zuma amma zaki cire icen kafin ki zuba hadin, sai ki sauke ki dinga sha daidai kima idan ya huce.

8. Ku samu zogale ku wanke shi ku nika shi tare da dabino da kuma kwakwa sai ku tace kusa zuma tare da madara sai ku saka ya yi sanyi bayan kungama sallar mangarib sai ku sha.

Bayani kan wanda basajin dadin saduwa

Ana so mace ta kula da gabanta domin Allah ya sa namiji ya kwallafa ransa gare shi. Barinsa ya lalace kamar zubar da kimarki ne a wajen sa kada ki bar shi ya yi wari, kada ki bar shi ya yi fadi. Domin masana sun ce duk lokacin da aka yi jima’i farjin mace yana karafadi shi kuma nasa yana rage girma to kinga nasa na rage girma na ki na fadi zai kuma ba kya kula da shi, ba zai rika jin gamsuwa ba. Don haka sai ya fara tunanin kin tsufa ke ma ki fara ganin ya za ma rago shi ya sa yawanci ba a samun gamsuwa. Kuma ba kowane namiji ba ne zai iya fadawa matarsa gabanta ya kara girma ba.Don haka mu kula.

Macen da takeso gabanta ya yi cif icf sai ta samu farar albasa, kanunfari, citta, balmo, barkono, rihatul hulbi. Sai ki hada su waje daya ki mayar da su kamar yaji kina zubawa cikin abinci kina ci kullum. Mijinki ma za ki iya masa hadi, ki sami muruci, saiwar haukufa, namijin goro, hanno, rihatul hubbi ki daka su gaba daya, ya dinga zubawa a nono mai kyau sha. Sannan ku nemi dabino a daka shi ya sa a cikin nono mai tsami sai ya rika kama ruwa da shi, amma fa bayan ya gama shafawa zai iya wanke wa da ruwa.

Insha Allah za a samu biyan bukata. Allah ya taimake mu amin.
Karin Bayani

Cuta daga Allah ne kuma ya aiko mana da maganin kafin ya sauko da cutar. Don haka mu san ba abin da ya fi karfin magani. Shawara ita ce a yawaita shan zam-zam, insha Allahu magani ne ba adadi. Allah ya ba mu lafiya baki dayanmu!


Tare da

Jummai Ibrahim
GSM: 08097160554 (tes kawai)
saasanaa@yahoo.com


sharhin adabi:

Tambihi: Alfijirin Da A Ke Jira

Duniya ce da bakin duhu ya mamaye ta ta ko’ina… amma wannan bakin duhu yana kunshe da wani haske da aka dade ana tsumayarsa… ga kuma cida na dauke da albishir na bayyanar sabon Annabi… cidar wannan albishiri ta kutsa ko’ina, tana kwankwasa kunnuwa da zukata, har sai da mutane masu yawa cikin garin Makka suka fara kitsa wa juna labarin wannan Annabi da ake tsumaya, suna kuma yi wa juna wasici da shi, suna cewa: “Muna horonku da ku yi gaggawa zuwa ga wannan Annabi da zarar ya bayyana, ku yi gaggawar zuwa gare shi, ku kuma yi imani da shi!”(11).

Dukan zukata suna zaman jira.. domin duk wani buri an riga an sanya wa wannan abin tsumaya.. Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam) karshe mai kuma tseratar da halittu daga halaka… iyaye maza da mata suna kwadayin a ce wannan Annabi ya fito daga tsatsonsu, don haka ne ma wasu da dama daga cikinsu suka sanya wa ‘ya’yansu suna “Muhammadu”(12). Amma fa sai dai dole ne wannan Annabi ya fito daga mafi kyawun tsatso; tsatson da zai fara da Annabi Ibrahim da Isma’il (Alaihimas Salam), ya kare da Abdulmudallabi zuwa Abdullahi… duka zukata suna tsumayar wannan haske ne ta wannan hanya, dukan kuma abubuwan da suke faruwa suna nuni ne da kusantowar lokacin zuwansa.. domin tsananin duhu alama ne na ketowar alfijir.

Mutum a wannan zamani ba ya dauke da wata kima da za ta sanya rayuwa ta zama tana da ma’ana, ta yadda rayuwa za ta zamo tana da manufa da ya kamata a rayu saboda ita, ayyukan mutane a wannan lokacin daidai yake da yadda Alkur’an mai girma ya bayyana da cewa: ((Lallai ayyukan wadanda suka kafirce kamar wani abu mai kama da ruwa da ake hange akan titi daga nesa (kawalwainiya ko fitsarin shaidan) da mai kishi yake zaton ruwa ne, har sai idan ya zo wurinsa ya ga ba komai ba ne)) [an Nur: 39].

Tunanin mutane da ayyukansu wajen duhu ba su da wani bambamci da: ((…. Duffai a cikin teku mai duhu da kumfa ta lullube shi a samanta kuma akwai wata kumfar ta lullube ta, a samansa kuma akwai giragizai, duffai ne wani a saman wani, idan ya fito da tafin hannunsa da kyar zai gansa)) [an Nur: 40].
Sunan wannan zamani “Zamanin jahiliyya”, sai dai fa jahiliyya a nan ba kishiyar ilimi ba ne, abin da ake nufi, kalma ce da take rakiya ga kafirci, wanda yake kishiya na imani. Ba ina so ne –ko kadan- na bijiro da munanan abubuwan da suke a wannan zamani ba ne, domin ba na son na kawo maku wannan kazantacce shafi –ko na dan kankanin lokaci-. Kamar yadda suranta bata na iya bata kwakwale ya kuma batar da su, kai ni ina ganin ma haka laifi ne. amma duk da haka, idan muna son mu fahimci yadda wannan zamani yake, dole ne mu yi nuni zuwa ga wasu daga cikin al’adunsa, domin mu sami damar hararo falalar da Allah ya yi wa talikai, da kuma rahamar mai rahama da jinkai a gare su na aiko abin tinkahon halittu kuma shugaban Manzanni.

Lallai zuwan mai tsira da aminci babbar ni’ima ce ga talikai, kuma haka shi ne mafificin kyautatawarsa a gare mu, wannan shi ne abin da Alkur’an mai girma ya yi nuni a inda yake cewa: ((Lallai tabbas Allah ya goranta wa muminai; don ya aiko masu da Manzo daga cikinsu da yake karanta masu ayoyinsa, yake kuma tsarkake su, yake kuma sanar da su Alkur’an da sunna)) [ali Imran: 164].

Dubi irin wannan rahama da tausayi da kyautatawa daga Allah lokacin da ya aiko wa mutane da Manzo daga cikinsu, yana jin abin da suke ji, yana kuma tunani kamar yadda suke yi, ya kuma zamo masu jagora mai shiryatarwa zuwa ga hanyar da za ta kai su zuwa ga Allah Madaukakin Sarki.. Idan sun bukaci limami sai ya shige masu gaba ya zamo shi ne limaminsu, idan kuma suka bukaci mai huduba, sai ya hau minbari, ya yi masu huduba ta ban mamaki, mai kuma gamsarwa, idan kuma suka bukaci samun sarki, sai ya zamo masu sarkin da yake aikawa da wasiku zuwa ga sarakuna, yana kuma buga hatimi a yarjejeniyoyi, idan kuma suka bukaci kwamanda a wajen yaki, sai ya ja masu gaba, ya zamo suna da kwamandan da ya zarce dukan kwamandodjin da suka kware a fagen yaki.

Akwai wata gurbatacciyar akida a wajen Kiristoci, da suke imani da cewa lallai Allah Madaukakin Sarki ya sadaukar da Annabi Isah (Alaihis- Salam) domin ya zama fansa akan kuskuren dan adam na farko, ma’ana suna imani da cewa Allah Madaukakin Sarki ya sadaukar da dansa Almasihu –Allah ya wuce haka- domin ya yafe wa ‘yan adam baki daya, saboda haka ne aka rataye Almasihu a kuros kamar dai yadda wannan akida gurbatacciya ta nuna, da haka ne aka yafe wa ‘yan adam kuskurensu na farko da ya fara tun daga Annabi Adam (Alaihis- Salam), ya kuma zarce zuwa ga duk wani bil’adama, kuma wai kowane dan adam yana dauke da wannan kuskuren tun lokacin da ya zo wannan duniya, tun sanda aka haife shi.

Wannan imani kuskure ne ta wannan fuska, ta wata fuskar kuwa abin nema ne, domin za ta iya zama fassarar abubuwa masu yawa da suke yin ingantaccen nuni zuwa ga haka, wannan abu kuwa shi ne, lallai Allah Madaukakin Sarki ya aiko da mafificin halittarsa Muhammadu (Sallallahu alaihi wa sallam), -wanda ya fi so- zuwa ga mutane, duk kuwa da cewa ya san zai fuskanci cutarwa gami da musgunawa daga wasu, an yi hakan ne domin ya tsamo su daga bata da karkata da girman kai, saboda kada su bace a hanyoyi mabambanta da kwazazzabai, a’a manufa ita ce su daukaka zuwa ga matsayin cikakken mutum… kamar yadda bayanin fitaccen malami kuma sufi mawaki “Ibrahim Hakki” ya nuna, dole ne muminai su san Ubangijinsu a matsayin wata taska ne a cikin zukatansu.

Zuciya mabubbuga ce ta taskoki, ta yadda Allah Madaukakin Sarki wanda sammai da kassai ba za su iya daukan sa ba, amma duk da haka yana yin tajalli a cikin wannan zuciya.. Babu wasu littattafai ko hankula ko tunane-tunane ko falsafa ko azanci da fasaha ko sammai da kassai, kai, ko dukan halittu gaba dayansu da za su iya gewaye Allah Madaukakin Sarki, dukan su sun gajiya wajen bayyana shi, zuciya ce kawai za ta iya yin bayani –ko kadan ne- game da shi.

Kai tabbas zuciya na da harshen da kunnuwa ba su taba jin wani bayani da ya kai nasa, ko azanci da ya kai azancinsa ba, in kuwa haka ne, to dole ne mutum ya yanke wannan tazara da take cikin zuciyarsa, ya bincika abin da zai bincika a cikinta, ta yadda zai isa zuwa ga Ubangijinsa ta ciki, ya narke wajen sonsa, dole ne mu sani cewa lallai Allah Madaukakin Sarki ya aiko Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam)sa Muhammadu (Sallalahu alaihi wa sallam) ne zuwa gare mu saboda wannan dalili.

Tabbas lallai an aiko shi ne zuwa ga bil’adama domin ya karanta masu ayoyin Ubangijinsa, ya kuma zo masu da mu’ujizozinsa su gani kuru-kuru, ya kuma sanar da dan adam ainihin hakika. Da falalarsa ne ‘yan adam za su tsarkaka ga barin daudar dabi’a, su zamo tsarkaka masu tsafta, su daukaka daga mukamin duniya da jikkuna zuwa babban mukamin rayuwar zuciya da ruhi, kuma tabbas sun daukakan.

Na’am, tabbas da sannu mutane za su san Alkur’an da sunna (Hikima), cikin hasken wannan littafi da na wannan hikima ne bil’adama za su sami kansu, su fadaka zuwa ga lahira, su waiwaya zuwa gare ta, hakan ya sanya su bi hanyar dawwamammiyar rayuwa, kuma tabbas wannan hanya kam an bita.

Akwai ranaku masu albarka da muhimmanci da karamci a wurinmu, wasu daga cikinsu idi ne ga muminai. A cikin kowane mako muminai sukan yi farin ciki da ranar Juma’a, muna kuma yin farin cikin da ya fi haka a karamar sallah da babba.



Tarihin Manzo (SAW) Daga Littafin ‘Dawwamammen Haske’ Na Fethullah Gulen

Download 141,07 Kb.

Do'stlaringiz bilan baham:
1   2   3   4   5   6




Ma'lumotlar bazasi mualliflik huquqi bilan himoyalangan ©hozir.org 2024
ma'muriyatiga murojaat qiling

kiriting | ro'yxatdan o'tish
    Bosh sahifa
юртда тантана
Боғда битган
Бугун юртда
Эшитганлар жилманглар
Эшитмадим деманглар
битган бодомлар
Yangiariq tumani
qitish marakazi
Raqamli texnologiyalar
ilishida muhokamadan
tasdiqqa tavsiya
tavsiya etilgan
iqtisodiyot kafedrasi
steiermarkischen landesregierung
asarlaringizni yuboring
o'zingizning asarlaringizni
Iltimos faqat
faqat o'zingizning
steierm rkischen
landesregierung fachabteilung
rkischen landesregierung
hamshira loyihasi
loyihasi mavsum
faolyatining oqibatlari
asosiy adabiyotlar
fakulteti ahborot
ahborot havfsizligi
havfsizligi kafedrasi
fanidan bo’yicha
fakulteti iqtisodiyot
boshqaruv fakulteti
chiqarishda boshqaruv
ishlab chiqarishda
iqtisodiyot fakultet
multiservis tarmoqlari
fanidan asosiy
Uzbek fanidan
mavzulari potok
asosidagi multiservis
'aliyyil a'ziym
billahil 'aliyyil
illaa billahil
quvvata illaa
falah' deganida
Kompyuter savodxonligi
bo’yicha mustaqil
'alal falah'
Hayya 'alal
'alas soloh
Hayya 'alas
mavsum boyicha


yuklab olish