Tashin Farashi Ne Ya Sa Mu Shiga Yajin Aiki


Ana yi wa Gwamna Ganduje kallon wanda ke tafiyar wahainiya aharkar mulki, shin ya kuke kallon wannan batu?



Download 141,07 Kb.
bet6/6
Sana02.03.2017
Hajmi141,07 Kb.
#3696
1   2   3   4   5   6

Ana yi wa Gwamna Ganduje kallon wanda ke tafiyar wahainiya aharkar mulki, shin ya kuke kallon wannan batu?

Duk inda ka ji gaggawa daga shaidan take, saboda haka iya salon mulki ne wannan, domin dole sai ka yi wa dukkan sassan dake jihar Kano kallon tsanaki, kafin ka afka masu da aiki, don gudun yin aikin baban giwa. Wanda duk ya san Ganduje ya san horon Kwankwaso ne, mutun ne mara tsoro, mai taka tsantsan da dukiyar al’umma sannan kuma yana yin duk mai yiwuwa wajen kara fito da hanyoyin samun kudaden shiga.

Wannan tasa mu Karamar hukumar Takai muke inganta harkar tattara kudaden shiga, muka bayar da umarni ga dukkan dagatan da suka san akwai gonakan Karamar hukumar a garuruwansu su kawo kididdigarsu don sanin yadda za a inganta harkar samun kudin shiga ta wannan bangaren.

Kuma da kake batun tafiyar wahainiya ina tafiyar wahainiyar take, gwamnan da dare baya hana shi fita don gudanar da ayyukan ci gaban al’umma, baya fita daga ofis sai ya tabbatar da sallamar dukkan takardun da suka je gabansa, kuma kace ana tafiyar hawainiya.


Wace irin rawa kuke takawa domin tallafawa ayyukan gwamnatin Ganduje?

Da farko dai ka san Kano ne kadai jam’iyyar adawa ta PDP bata da koda kujera guda, tun daga kujerar Kansila har zuwa shugaban kasa, wannan tasa mu a matakin kananan hukumomi muke yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da gudanar da ayyukan ci gaba, sannan kuma muke kara wayar da kan al’ummarmu muhimmancin biyayya tare da inganta harkar zaman lafiya, kuma matasan mu ana bakin kokari wajen samar masu da sana’o’in da zasu dogara kansu.

Wannan kungiya na samun cikakken goyon baya da hadin kan shugabannin kananan hukummomin jihar Kano 44, don ganin gwamnatin Ganduje ta aiwatar da abubuwan da ta sa gaba.
Jama’ar Karamar hukumar ka na yima kirari da ka ci gaba da yi, mene ne sirrin hakan?

Ni abinda na dauka shugaban al’umma shi ke yi masu hidima, saboda haka bani da wani aiki a gabana da ya wuce biyawa jama’ar da suka zabeni bukata, wannan tasa muka kashe bakin duk wani dan adawa a Takai domin kowa ya gani a kasa, muna tare da jama’armu ba ma gudunsu, kuma suma basa gudunmu, kila wannan ce tasa suke irin wancan kalamai. Kuma ina godiya kwarai da irin gudunmawar da iyayen kasa irin su mai girma hakimin Takai, Dagatai da masu unguwanni, shugabannin Jam’iyya da daukacin al’ummar Takai, sannan kuma ina kara jaddada masu cewar layarsu tayi kyan rufi, kuma shukar da suka dasa fari bai hana ta yabanya ba.

Ina kuma kira da babbar murya cewar mu ci gaba da bayar da hadin kai ga Gwamnatin Ganduje domin samun sukunin yiwa jama’a yayyafin alhairi tare da kwankwadar romon demokaradiyya.
Ya ya batun dangatarka da sauran ma’aikatan karamar hukumar Takai

Wallahi ina matukar godiya da irin gudunmawar da ma’aikata ke bani domin sauke nauyin da Allah ya dora mana, musamman manyan ma’aikata wadanda muke tare, da kuma uwa uba zababbun Kansilolina da kuma kansiloli masu gafaka, ko shakka babu wadannan bayin Allah na yin abinda ya kamata domin ganin an gudu tare an kuma tsira tare, ina mika godiya ta musamman ga manyan jami’an gudanarwar mulki na karamar hukumar Takai, bisa gagarumar gudunmawr da suke bani don cimma nasarar da ake fata.


TATTAUNAWA: Dalibai Za Su Cigaba Da Samun Taimako A Kowane Fanni —Kwamared Danguda
Daga Abdullahi Mohd Sheka

Daya daga cikin masu fafutukar ganin an kyautata rayuwar dalibai, Alhaji Nasiru Danduga, ya bayyana cewar taimakon dalibai shi ne abin da ya kamata a mayar da hankali akai don tabbatar da ganin an kyankyashe shugabanni na kwarai.

Ya dai bayyana hakan ne a ranar Asabar da ta gabata, lokacin da Kungiyar Daliban ‘yan Asalin Jihar Kano suka Karrama shi tare takwaronsa, Alhaji Muntari Salisu.

Taron da aka gudanar a dakin taron makarantar horar da ilimin na’urar Kwamfuta dake garin Dambatta ya samu halartar masana da kwararru ta fuskar koyar da kuma nazari kn yadda harkokim dalibai ke gudana.

Da ya ke gabatar da Jawabin maraba, shahararren dan gwagwarmayar nan kuma Jami’im walwalar Kungiyar Daliban ta jihar Kano Kwamared Tijjani Nasir Dambatta, ya yiwa mahalarta taron maraba tare da bayyana makasudin wannan taro wanda ya ce sun shirya shi ne domin karrama wasu ‘yan kishin kasa da al’ummar Karamar hukumar Dambatta musamman a harkokin ilimi.

An karrama wadannan mutane biyu da lambar Jaruman da suka yi fice wajen talallafawa dalibai, (Grand Commander in Education)

Kwamared Tijjani Nasir Sulaiman Dambatta ya bayyana cewar kafin zakulo wadannan zaratan mutane cikinsu ba wanda ya san su, su ma ba su san su ba, amma bisa la’akari da abubuwan da suka gani na yawan daliban da wadannan mutane suka taimakawa da kudaden makaranta, samar da yanayin da ya dace domin samun ingantaccen ilimi, ya sa wannan kungiya yin duk mai yiwuwa don ganin an karamma wadannan mutane domin hakan ya zama abin koyi ga sauran.

Daga nan sai ya sanar da cewar wadannan mutane suna cikin mutanen da wannan kungiya zata karrama nan bada jimawa ba a fadar Gwamnatin Kano, ya ce “cikin wadanda za a karamma har da mai girma Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da sauran muhimman mutane.”

Shima shugaban kugiyar daliban ta kasa ‘yan asalin jihar Kano, wanda kakakin majalisar Sanatocin kungiyar Kwamared Safwan Iliyas ya wakilta, ya bayyana cewar ko shakka babu garin Dambatta na da jajirtaccen wakili, kuma dan gwagwarmaya a kungiyar Dalibai yan asalin jihar Kano dama kasa baki daya.

Ya ce ba kowacce karamar hukuma ake dauka ba, amma saboda jajircewar wannan matashi, ya kafe sai an bai wa karamar hukumar Dambatta mutun hudu wadanda za a karrama, bayan tsananin mahawara dole aka amince da ba shi mutum uku.

Ya ci gaba da bayyana nasarorin da Kwamared Tijjani Nasir ya samu musamman a lokacin da yake shugabantar kungiyar daliban Jami’ar Usman Dan Fodio, wanda a gabansu aka ba shi lambar karramawa saboda kwazonsa na hada kan daliban Jami’ar tare da kawo dawwamamen zaman lafiya a Jami’ar.

Shugaban karamar hukumar Dambatta wanda ya samu wakilcin Sakataren mulki na karamar hukumar. Alhaji Nasiru Yaro, ya bayyana kokarin shugaban karamar hukumar musamman na daukar nauyin karatun wasu dalibai sama da 70 da suke karatu yanzu haka a Funtua, sannan kuma karamar hukumar ta amince da biyawa daliban karamar hukumar Dambatta kudaden Kwalifayin ga wadanda suka fadi, wanda biyan wadannan kudade ne zai ba su damar ci gaba da karatunsu, daga nan sai ya tabbatarwa da jama’ar Dambatta cewa za su ci gaba da hada karfi da wadannan zakakuran mutane masu kaunar ci gaban al’umma.

Alhaji Muntari Salisu wanda guda ne cikin wadanda aka karrama da wannan lambar yabo, ya bayyana cewar shi ba shi da abinda zai bayyana a wannan lokaci, ya ce a zatonsa abubuwan da suke bai taka kara ya karya ba, amma kuma sai gashi jama’ar Dambatta musamman kungiyar dalibai sun shirya wannan babban al’amari.

Daga bisani sai ya bukaci sauran mutane da Allah ya ba su dama su ci gaba da tallafawa matasanmu don samun ilimi da kuma dogaro da kansu.

Haka zalika shi ma Alhaji Nasiru Danguda wanda a lokacin taron ya bayyana farin cikinsa tare da godewa magabatan su kasancewar da bazarsu suke rawa, musamman irin gudunmawar da iyaye suka bayar, saboda haka sai ya tabbatarwa da al’ummar Dambatta aniyarsu ta ci gaba da tallafawa duk wata harka da za ta kawo ci gaba a karamar hukumar Dambatta.

Hakimin Dambatta Sarkin Ban Kano Alhaji Muktar Adanan wanda sakatarensa ya wakilta, ya bayyyana wasu daga cikin gudunmawar da wadannan zakakuran ‘yan kishin kasa ke bayarwa, haka kuma ya bayyana farin cikinsa bisa mukaman da ‘yan asalin Dambatta ke kansu a wurare daban-daban, haka kuma hakimin ya bukaci ‘yan asalin wannan masarauta da su kasance wakilai na gari a duk inda samu samu kansu.

Cikin wadanda suka halarci wannan muhimmin taro akwai wakilin Sa’in Kano Hakimin Makoda wanda wazirin Makoda ya wakilta, Sakataren karamar hukumar Dambatta da sauran muhimman mutane, kungiyoyin dalibai daga ciki da wajen Dambatta.
Wulakanta Marasa Lafiya:

Ya Kamata Gwamnatin Kano Ta Ji Wannan

Daga Mudassir Aliyu Yunusa


Kamar yadda yake a bayyane, Kano babban gari ne wanda ya shahara ta fuskoki da dama, kama daga yawan jama’a, harkokin ciniki da hadahadar kasuwanci, siyasa, cigaban al’umma, masana’antu da kuma sha’anin mulki. Jihar Kano na da kananan hukumomi 44 da ke kunshe da yawan mutane kimanin miliyan 15. A cikin kwaryar birnin Kano akwai kananan hukumomi takwas wadanda suka kunshi kusan kashi biyu cikin uku da daukacin jama’ar jihar. Wannan yawan jama’ar ya jawo abubuwa da dama masu kyau da marasa kyau; da suka hada da bukatun abubuwan more rayuwa irinsu: hanyoyi, ruwan sha, makarantu, asibitoci da sauransu.

Sai dai abin takaicin shi ne yadda ganin yadda asibitocin gwamnati masu kula da marasa lafiya musamman taimakon gaggawa da ‘yan hatsari su ka yi karanci a fadin jihar, a halin da ake ciki yanzu, kwaryar babban birnin Kano tana maleji da asibitocin gwamnati masu karbar ‘yan hatsari guda 5 ne kacal, wanda dole su gaza aiwatar da ayyukan taimakon gaggawa kamar yadda ya kamata. Asibitocin sune Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed, Asibitin Kwararru na MuhammaduA bdullahi Wase, Asibitin Sir Muhammadu Sunusi, Asibitin Sheikh Muhammad Jidda sai kuma Asibitin Zana (IDH).

Wadannan asibitocin sun kai makura wajen gazawa ta fuskar ayyukan taimakon gaggawa. Dalilin a nan shi ne, ni ganau ne ba jiyau ba, na dauki wata baiwar Allah da ta fadi sakamakon jininta ya hau ranga-ranga zuwa asibitin Nassarawa inda abun takaici mun tarar da marasa lafiya kusan 20; wasu a kan kujera mai tafiya, wasu a dandaryar kasa amma duka-duka likitoci biyu ne ke duba masu bukatar taimakon gaggawa da ‘yan hatsari. Muna zuwa likitan ya tabbatar mana da rashin gado ya tura mu asibitin kwararru na Murtala dake cikin birni a inda abun har ya fi na Nassarawan tabarbarewa. Tun da farko ma hana mu shiga da mota aka yi ga shi kuma akwai bukatar shiga ciki kasancewar mara lafiyar ba ta ma san inda kanta yake ba, a karshe dai sai aka bukaci mu bada wani abu (N300) don a bude mana mu shiga, na yi alkawarin zan bayar in an gama duba mara lafiyar. Muna shiga nan ma muka tarad da marasa lafiya fiye da 20 amma likita daya ne rak, a inda aka shaida mana ba gado sai dai gado mai taya (stretcher) amma ita din ma sai mun dan yi motsi sannan zamu samu. Kai! Allah ya sauwake, ba tausayi, ba kunya, ba tsoron Allah, haka dai dole muka fita saboda kafin ma likitan ya zo akwai matsala. Ba mu zame ko ina ba sai Asibitin Sheikh Muhammadu Jidda dake kuroda, nan ma da irin abin da muka taras a sauran asibitocin shi ne ya faru. A karshe sai asibitin koyarwa na mallam Aminu Kano muka je aka samu nasarar bata agajin gaggawa da misalin karfe 2 na dare.

A gaskiyar lamari wannan abun takaici ne kuma abun kunya musamman ga gwamnatin jihar Kano da take kuranta kanta wajen cigaban talakawanta musamman a bangaren kiwon lafiya, ni kam tabbas na gane cewar karya ce da yaudara ake yi wa mutane a kafafen watsa labarai akan harkar lafiya. Abinda ya sa na ce haka kuwa bai wuce lamarin da ya faru da ni na zahiri, kuma na gani da idona tabbas talakawa na shan bakar azaba, wulakanci, rikon sakainar kashi da kuma cusgunawa a asibitocin gwamnati musamman a ta fuskar taimakon gaggawa da kuma ‘yan hatsari. Na san da yawa za su ji haushin wannan ke ce gaskiya da na yi don wani dalili na su, amma ina so don Allah jama’a su ziyarci wadannan asibitocin musamman da dare matukar ba sun gyara bane na yi imanin da yawa za su zubar da hawaye ganin halin da talakawa ke ciki.

Tambaya a nan ita ce, me yasa asibitocin gwamnati ke fama da irin wannan rashin kulawar? Shin ko don masu kudi da wasu masu fada aji a gwamnati basa zuwa asibitin gwamnatin? Me yasa likitoci suka fi maida hankali a asibitoci masu zaman kansu fiye da na gwamnati duk da irin albashi da alawus da gwamnatin ke basu? Me yasa ake wulakanta marasa karfi a asibitocin gwamnati? A karshe me ya sa gwamnati take kururuta ayyukanta a kafafen watsa labarai ba tare da bin diddigin yadda al’amuran kyautatawa jama’a ke wakana a zahirance ba ?

Tabbas ya zama wajibi gwamnati ta farga ta kuma tashi tsaye wajen tabbatar da tsari mai kyau a asibitocinta musamman a wajen ‘yan hatsari da kuma dakin mata masu haihuwa, don su ne wuraren da sakaci da su ka iya jawo asarar rayuka cikin gaggawa.

Shawara ga gwamnati da kuma masu hannu da shuni kai har ma da ‘yan siyasa ita ce su rika kokarin samar da wuraren karbar agajin gaggawa a unguwanni ba sai lallai a cikin manyan asibitoci ba don ceton lafiya da rayukan al’umma musamman a cikin birnin Kano da kewaye mai cike da yawan jama’a. Allah ya sa masu ruwa da tsaki kan harkar lafiya su ji wannan shawarar don tabbatar gaskiya da adalci ga talakawansu.

Mudassir ya rubuto daga NTA Zariya. Imel:mudassiray@gmail.com


nasiha: Zauren Fikhu

Tambayoyi Da Amshoshi Daga Membobin Zauren Fikhu

Masu Shan Miyagun Kwayoyi



-Tambaya:

Assalam Alaikum. Ina yiwa Malam fatan Alkhairi. Tambayata a nan ita ce, Malam kamar yanda ya zo a cikin Hadis.”Manzon Allah (saww) ya ce: “Mutane Uku An Dauke Alkalami Daga Kansu (Wato Ba’a Rubuta Musu Alhaki):

• Mai Barci har sai ya farka.

• Karamin yaro har sai ya balaga.

• Mahaukaci har sai ya yi hankali”.

(Ahmad da Nisa’iy da Ibnu Maajah da Abu Dawud duk sun ruwaitoshi. Kuma Hakim ya inganta shi). Toh Malam Tambayar a nan Itace, shin har da Mahaukatan da suka haukatar da kansu? Misali ta bangaren shaye-shayen muggan kwayoyi?

Daga Abba Ibrahim Dawaki

-Amsa:

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Acikin Alkur’ani Allah ya yi magana a kan giya a matsayinta na abun da ke sanya maye, ya ce “ita giya kazanta ce daga ayyukan shaidan.” Sannan kuma ya ce “Shi shaidan yana nufin ya haddasa kiyayya da gaba ne a tsakanin ‘Yan Adam ta hanyar giya da chacha, Kuma ya juyar da su daga (barin) Zikirin Allah da kuma Sallah.”

Sannan a cikin Hadisi, Manzon Allah (saww) ya ce, “Duk Abin Da Ke Sanya Maye, Giya Ne, Kuma Duk Abin Da Ke Sanya Maye Haramun Ne”.

Wannan ya hada da su wiwi, da miyagun kwayoyin da samari suke sha din nan. Duk da cewa su ainahin kwayoyin an yi su ne domin wani abu dabam, ba don asha a yi maye ba.

To duk Musulmin da ya yi watsi da dokar Ubangijinsa, har ya je yasha kwayoyi domin yin maye, kuma ya haukace ta dalilin haka, to tabbas ya aikata babban kuskure. Kuma ba zai samu ladan wannan jinyar haukan ba. Tunda ya sameta ne ta hanyar dabon Allah.

Kuma yana cikin laifi har sai ya samu hankali ya tuba zuwa ga Allah. Idan kuma har ya mutu a haka bai samu lafiya ba ballantana ya tuba ba, to al’amarinsa yana wurin Ubangijinsa (SWT).


-Tambaya

Salamun alaikum. Da fatan Mallam ya wuni lafiya, Mallam ina son a amsa mun tambayata, mahaifiyarmu ce suka samu sabani da mahaifinmu har ta kai ga ya ce dai saketa, to shi ne wani malami ya ce mun wai asiri kishiyoyinta da mahaifiyar babanmu suka mata, saboda haka wai za a bukaci kifi na Hausa da mai kankara da kaza, da akuya ne ko rago cikin biyun dai, sai a ambaci sunayensu wai a dafa da niyyar duk wanda ya mata abu ya koma kansa.Tambayata ita ce, hakan ya halasta ko kuma ya saba ma addini, Mallam ina so a bani shawarar hanyar da zan bi domin gudun saba wa Allah. Nagode



-Amsa:

Wa alaikis salam wa rahmatullah wa barakatuh. Hakika wannan maganar tana kunshe da kusakurai da yawa. Babban kuskure na farko shi ne wannan zargin da kuke yi. Domin shi zargi yana daga cikin mafiya miyagun laifuka.

Allah yana cewa: “Hakika Shi Zargi Ba Ya Wadatar Da Komai Da Komai Daga Gaskiya”. Kuma yace: “Hakika Wani Sashen Daga Cikin Zato, Laifi Ne”.Manzon Allah (saww) ya ce “Halaye Guda Biyu Babu Abin da Ya Fisu Muni: Mummunan Zato Ga Allah, Da Kuma Mummunan Zato Ga Bayin Allah”.

Don haka bai halasta ku rika zargin kishiyoyin mahaifiyarku a kan abin da ba ku gani da idanunku ba. Koda kuwa akwai yiwuwar hakan. Wannan laifi ne babba wanda zai iya kai ku zuwa ga hallaka. Kuskure na biyu shine zuwa wajen ‘Dan Duba da kuka yi. Domin bisa abin da wannan mutumin ya gaya muku, Kamar ya duba ne ya gano cewa asiri aka yi. Shi kuwa ‘Dan duba bai halasta a je wajensa har a yi wata hulda da shi ba. Manzon Allah (saww) ya ce :”Duk Wanda Yaje Wajen Boka Ko Dan Duba Kuma Ya Gaskatashi Akan Abin da Ya Fada, To Hakika Ya Kafirce Ma Abin da Annabi Muhammadu (Saww) Ya zo Dashi”.

Kin ga a nan kun aikata babban kuskure wanda zai iya kai ku ga kafirci. Wajibi ne ku tuba zuwa ga Allah Madaukakin Sarki tun kafin azabarsa ta riske ku!

Kuskure na uku kuwa shi ne wadannan abubuwan da mutumin ya umurce ku da su duk ba su halasta ku kai masa ba. Domin kuwa watakila shi zai yi amfani da su ne domin kulla nasa sihirin don cutar da kishiyoyin mahaifiyarku.

Koda da gaske ne sun yi mata sihiri, to ai bai halasta ku je ku yi wani sihirin domin ramakon gayya ba. Wannan duk bai halasta ba. Domin sihiri kafirci ne.

Zargin da kuke yiwa Matayen Babanku da kuma Kakarku, zai iya janyo muku rashin Shiri a tsakaninku. Kuma zai fusata Mahaifinku. Wannan zai janyo muku rashin albarka a rayuwarku.

Ina baku shawarar cewa ku kyale wadancan abubuwan ku rungumi addu’a da nafilfili cikin dare. Sannan ku yawaita fadin: “La Haula Wala Kuwwata Illa Billaahil ‘Aliyyil ‘Azeem”. (100) a gurbin kowacce sallah, ko kuma safe da yamma.

Manzon Allah (saww) ya ce LA HAULA tana toshe kofofin bala’i ko bakin ciki guda saba’in. Kuma ita kanta taskar Aljannah ce.

Ku rika yawan maimaita Falaki da Nasi. Ku rika tawassuli da su bisa niyyar karya sihirin (in ma akwai shi). Ku rika yiwa mahaifiyarku nasiha a kan hanyoyin da za ta bi domin faranta zuciyar Mahaifinku da kyautata masa a koyaushe.
Halaye Tara Da Za A Sifantu Da Su A Tsira Daga Sharrin Shaidan:

1. Kulawa da Sallolinka na farilla, tare da jin tsoron Allah a cikinsu.

2. Ka rika fitar da zakkar dukiyarka cikin farin ciki da neman yardar Allah (SWT).

3. Cikakken gaskatawa da ranar Alkiyamah da abubuwan da za su faru a cikinta. Tare da rungumar halaye nagari wadanda za su fishe ka a wannan ranar.

4. Tsananin jin tsoron azabar Allah, irin tsoron da zai nisantar da kai daga aikata abin da zai janyo maka Fushin Allah (SWT).

5. Kiyaye al’aurarka tare da dukkan gabobin jikinka daga aikata dukkan abin da Allah ya haramta maka. Kamar Zina, Luwadi, Madigo, da kuma abubuwa masu cutarwa irin su Istimna’i (Masturbation).

6. Kiyaye amana tare da bayar da ita kamar yadda aka baka ba tare da tauye komai ba.

7. Cika dukkan alkawarin da ka dauka ba tare da yin yaudara ba.

8. Fadin gaskiya ko yaushe a cikin zantukanka. Tare da bayar da Shaida a kan dukkan abin da aka tambayeka ba tare da boye komai ba.

9. Bin iyaye tare da girmama duk wanda yake da hakki a kanka, da kuma kulawa da zumunci.

Ya Allah ka gyara halayenmu, Ka kyauatata dabi’unmu, ka sanya mu a cikin bayinka nagari, don falalarka da rahamarka. Amin.
Abubuwa Masu Saurin Rushe Ladan Ayyuka

Ko ka san cewar Istighfari guda daya zai iya janyo maka wankewar dukkan Zunubanka? Haka nan kuma mummunar kalma guda daya wacce ta fito daga bakinka za ta iya rusa maka dukkan ladan ayyukanka baki daya.

Daga cikin miyagun maganganun da za su iya rusa maka dukkan ladan ayyukanka ba tare da saninka ba, akwai:

1. Wulakantar da wani muhimmin abu na addini.

2. Kaskantar da darajar Manzon Allah (saww) a cikin zancenka, ko a aikace.

3. Kiran sunan Manzon Allah (saww) ba tare da girmamawa ba, kamar irin yadda kake kiran sunan abokinka.

4. Cira murya ko kuma yin hayaniya a cikin Masallacin Manzon Allah (saww) da ke Madina, ko kuma duk wani wajen da ake ambatonsa, ko kuma karatun Hadisinsa (saw).

5. Fifita wani abu na son zuciya fiye da hukuncin Allah da Manzonsa (saww).

6. Cutar da duk wanda idan an cuce shi zai zama tamkar an cutar da Manzon Allah ne (saww). Wato kamar Iyayensa Tsarkaka, Iyalan gidansa, Sahabbansa, Zuriyarsa da sauransu.

Ya Allah ka kiyayemu daga aikata



Don Karin Bayan:

Facebook/Dandalin Zauren Fikhu

GSM: 07064213990
Download 141,07 Kb.

Do'stlaringiz bilan baham:
1   2   3   4   5   6




Ma'lumotlar bazasi mualliflik huquqi bilan himoyalangan ©hozir.org 2024
ma'muriyatiga murojaat qiling

kiriting | ro'yxatdan o'tish
    Bosh sahifa
юртда тантана
Боғда битган
Бугун юртда
Эшитганлар жилманглар
Эшитмадим деманглар
битган бодомлар
Yangiariq tumani
qitish marakazi
Raqamli texnologiyalar
ilishida muhokamadan
tasdiqqa tavsiya
tavsiya etilgan
iqtisodiyot kafedrasi
steiermarkischen landesregierung
asarlaringizni yuboring
o'zingizning asarlaringizni
Iltimos faqat
faqat o'zingizning
steierm rkischen
landesregierung fachabteilung
rkischen landesregierung
hamshira loyihasi
loyihasi mavsum
faolyatining oqibatlari
asosiy adabiyotlar
fakulteti ahborot
ahborot havfsizligi
havfsizligi kafedrasi
fanidan bo’yicha
fakulteti iqtisodiyot
boshqaruv fakulteti
chiqarishda boshqaruv
ishlab chiqarishda
iqtisodiyot fakultet
multiservis tarmoqlari
fanidan asosiy
Uzbek fanidan
mavzulari potok
asosidagi multiservis
'aliyyil a'ziym
billahil 'aliyyil
illaa billahil
quvvata illaa
falah' deganida
Kompyuter savodxonligi
bo’yicha mustaqil
'alal falah'
Hayya 'alal
'alas soloh
Hayya 'alas
mavsum boyicha


yuklab olish