FITATTUN MATA: Lata (Didi) Mangeshkar
Ko Kun San?
Mangeshkar a matsayin fitacciyar mawakiya, ta fara waka tun a shekarar 1942? Ko kun san cewa mawakiyar yayar fitacciyar mawakiya, Asha Bhosle, wadda wannan shafi ya taba kawo tarihinta?
Har ila yau, Lata ta kasance mawakiya ta biyu a tarihin Indiya, wadda a ka taba bai wa lambar yabon ‘Bhara Ratna,’ sannan ta yi wakokin finafinan Indiya sama da dubu daya!
A duk yayin da a ka ambaci sunanta, babu abin da ke fitowa a bakunan masu yaba wa da fasaharta a fagen waka, illa dimbin yabo mara misaltuwa, don komai ba, sai domin jinjinar baiwa da kwarewarta a fagen na waka. Lata Mangeshkar ta shahara ne bisa zalakar da take da shi a muryarta, musamman yadda take wakoki da yarukan Hindi daban-daban, kama daga na finafinai, rubatattu da sauransu. Fitacciyar mawakiyar tana daga cikin manyan mawakan da a ka fi girmamawa a ciki da wajen masana’antar shirin fim na Indiya da al’ummar kasar baki daya.
Ganin irin daukakar da ta samu a fagen waka, Marubuta littafin kundin tarihin fitattu a duniya mai suna; ‘Guiness Book of World Records,’ suka rika jera bajinta da kwarewarta a jere, babu fashi, tun daga 1974 har ya zuwa 1991, duk shekara sai an kara sabunta sunanta a ciki, saboda irin yadda ta gagari tsararrakinta a fagen na fasihanci.
Ko Mene Ne Tarihinta?
An haifi Lata a ranar 28 ga Satumbar 1929 a kauyen Marathi cikin kasar Indiya. Masu hikimar zance kan ce, ‘Barewa ba ta gudu, danta ya yi rarrafe...,’ mahaifinta, Pandit Deenanath Mangeshkar babban mawaki ne a zamaninsa, kuma jarumin finafinai. An nuna cewa goyon bayan farko da ta samu wajen fara waka, daga mahaifinta ne, sannan daga bisani mahaifiyarta, Shebanti, ita ma ta bayar da nata gudunmawar.
Kasancewarsa kwararren mawaki, Pandit ne ya fara koya diyarsa waka, alhali tana da shekaru biyar haihuwa. Kafin ta tsunduma gadan-gadan a fagen waka, ta fara ne da fitowa a matsayin jaruma cikin wadansu kebabbun finafinan da mahaifin nata yake shiryawa. Sabili da samun irin wannan damar ne daya daga cikin ‘yan’uwanta, Asha Bhosle ita ma ta zama fitacciyar mawakiya.
An nuna cewa a lokacin da ta fara koyon waka a wajen mahaifinta, Lata ta fara koya wa yara wake-wake a makarantar boko, amma da malaminta ya hana ta, sai ta fara zuwa makarantar da ‘yar’uwarta Asha Bhosle domin su ci gaba da bibiyar darusan wakoki. A haka ta fara dora rayuwarta a fagen waka. Haka kuma a yayin da malamin nata, ya hana ta zuwa da karamar yarinya makaranta, sai ta jingine karatun nata baki daya.
Haka ta rika koyon salo iri daban-daban na rera waka, har lokacin da mahaifinta ya bar duniya a shekarar 1942, sakamakon ciwon zuciya. A daidai lokacin ne ta kara kaimi wajen ganin ta raya sana’ar da ta gada a wajensa.
Ta ci gaba da daukar darasi daga wajen kwararren mawaki, Ustad Amanat Ali Khan, inda ta fara da wata waka, mai suna, “Paa Lagoon Kar Jori,” wadda a ka sanya a cikin fim din ‘Aap Ki Seba Mein,’ a shekarar 1946.
A yayin da a ka raba kasar Indiya da Pakistan a 1947, Ustad Ali Khan, ya tattara iyalinsa ya koma sabuwar Pakistan din, Lata ta koma wajen wadansu fasihan domin ci gaba da koyon sana’a.
An shaidi cewa jajircewar da mawakiyar ta ke da shi ne suka sanya har ta ciri tuta a wannan fage na waka, ta kuma kasance babbar jaruma, wadda a ke kwaikwayo, a ke kuma alfahari da ita a ciki da wajen Indiya. Ta samu lambobin yabo marasa adadi. Muryarta daban ne a cikin muryoyin mawakan kasar Indiya.
Har gobe sunan Mangeshkar na ci gaba da jan ragamar a wannan fagen a cikin kasar Indiya.
Tare da Al-Amin Ciroma
(08033225331)
ciroma14@yahoo.com
Madubin Dubawa: Kallon Da Ake Yi Wa Marubuta Masu Bata Tarbiyya, Yana Hana Ni Bacci — Turau
A ci gaba da shirin zauren ‘Gidan Marubutan Hausa’ da ake gabatarwa a dandalin sadarwar ‘WhatsApp’ wanda Fadila A. Aliyu Kurfi ta kirkiro, yau ma za mu gabatar muku da daya daga cikin bakin da ake tattaunawa da su a zauren.
Kada dai a manta zauren wani dandali ne na marubuta litattafan Hausa, wadanda suka hadu domin ci gaba da raya adabin Malam Bahaushe. HAJIYA MARYAM NUHU TURAU ce babbar bakuwar zauren a ranar Talatar wannan makon, inda aka tattauna da ita kan batutuwan da suka shafi harkar rubuce-rubuce da yadda take gudanar da nata. MADUBIN DUBAWA ya dan gutsuro muku wani bangare na hirar kamar haka:
•Fatima Danborno Zariya (08179441065):
Bakuwarmu ta yau ita ce Hajiya Maryam Nuhu Turau, kuma tana tare da mu a yanzu, ko za ki gabatar mana da kanki?
•Hajiya Kanden Kauye (0708 713 5757):
Fatan alkhairin Allah a gareki Maryam
•Maryam Nuhu Turau (803 950 0702):
Yauwa, ina amsawa mutan kauye!
•Rabiu Abu Hidaya (08065025820):
Sannu da zuwa Hajiya Maryam ya hanya?
•Maryam Nuhu Turau (803 950 0702): Yauwa Abu Hidaya, hanya alhamdulillah
•Fatima Danborno Zariya (08179441065):
Gare ki malama Turau
•Maryam Nuhu Turau (803 950 0702):
Sunana Maryam Nuhu Turau, an haife ni a Rafindadi, Jihar Katsina. Na yi karatun Firamare a Makarantar Waziri Zayyana Science Model Primary School daga shekarar 1991 zuwa 1996. Na zarce zuwa Kwalejin ‘Yan Mata na Katsina, wato W.T.C. na yi shekaru uku a makarantar, na koma Makarantar Unity Girlsa Jibia, inda na ida a karatun sakandarena a shekarar 2002.
Bayan na kammala wannan, na yi karatun N.C.E a F.C.E Katsina, bayan na kammala na fara digiri, amma na bari sakamakon rikicin da akai ta fama da shi a garin Yobe.
Na yi makarantar Allo da Islamiyya na sauke Alkur’ani mai girma ba adadi, da sauran wasu ‘yan littattafai na addini. Wannan shine tarihina a takaice.
•Fadila Aliyu Kurfi (08039493637):
Ya zuwa yanzu mene ne adadin littattafanki?
•Maryam Nuhu Turau (803 950 0702):
Na rubuta littattafai guda biyar, amma biyu suka shiga kasuwa na ukku na kan hanya in sha Allahu.
•Fatima Danborno Zariya (08179441065):
Me ya ja hankalin ki kika ga ya dace ki zama babbar malama me wa’azantarwa? Wato marubuciya?
•Maryam Nuhu Turau (803 950 0702):
Teema abubuwan da suka jawo hankalina yawan karance-karance da na yi, musamman ma littafin ‘Magana Jari Ce,’ ‘Ruwan Bagaja,’ ‘Jiki Magayi,’ da sauransu, amma littafin da ya fi jan hankalina a wancan lokacin shine ‘Wa Zai Auri Jahila?’ Karance-karance ne suka kara min kaimin zama marubuciya.
•Mukhtar Kwalisa (0809 769 6912):
A wace shekarar kika soma rubutu?
•Maryam Nuhu Turau (803 950 0702):
A shekarar 2009 ne nake ji, Malam Kwalisa
•Zulfa Aliyu (0703 903 47):
Mene ne ya fi birge ki a littafin ‘Wa Zai Auri Jahila?’
•Maryam Nuhu Turau (803 950 0702):
Zulfa sadda na karanta Littafin ‘Wa Zai Auri Jahila?’ Ina firamare, don haka ba zan iya tuna takamaiman abin da ya birge ni ba, abin da kawai zan iya tunawa shi ne, na rika kwaikwayan littafin ina rubutawa a cikin littattafaina na makaranta da sunan ni ma marubuciya ce.
•Fadila Aliyu Kurfi (08039493637):
Mene ne ya fi birge ki dangane da harkar rubutu, har kike tunanin ke marubuciya ce tun kina karama?
•Maryam Nuhu Turau (803 950 0702):
Fadila yanda marubuta kan dauko wata rayuwa ko abin da ke faruwa cikin jama’a, su rubuta labari a kai, su baddala shi har ya fadakar da al’umma shi ya ja hankalina harkar rubutu.
•Fatima Danborno Zariya (08179441065):
Marubuta da dama suna kuka a kan ‘yan kasuwa, yaya abin yake a gun ki? Sannan me za ki ce game da taron ranar marubuta da ke tafe a yanzu?
•Maryam Nuhu Turau (803 950 0702):
Yanzun dai ban iya cewa komai saboda na kwana biyu littafina bai shiga kasuwa ba, amma da can matsalata da ‘yan kasuwa rashin bada kudi gaba daya, sai su rika karya marubuta, suna ba wa mutane kudi gutsul-gutsul.
Batun babban taron ranar marubuta kuwa, kira zan yi, Allah ya sa taron ya yi amfani ga dukkan marubuta, hadin kai da gyaran da ake fatar samu ga dukkan marubuta. Allah ya tabbatar da shi.
•Khadijah Mahuta (08036627395):
Salam, Malama Turau ga tambayoyina:
1. Wane ne gwaninki daga cikin marubutan da?
2 Wane amfani ko moriya kika samu a littafansu?
3 Ya za ki auna marubutan da, da na yanzun?
•Maryam Nuhu Turau (803 950 0702):
Mahuta, na fi son karanta littafin Maje el-Hajeej Hotoro, Rahma Abdulmajid, Anti Bilkisu Funtua da wasu da dama. Sannan Rashin ci gaban rubutun adabi da ba a samu yanzu, yana daga cikin matsaloloin da harkar rubutu ke ciki, da irin yadda ake kallo marubuta masu bata tarbiya, gaskiya Mahuta raina kan baci.
•Hajiya Halima Ummy (0803 488 14):
Tambaya - A matsayinki na tsohuwa kuma gogaggiya a fagen rubutu, shin a cikin wannan lokaci da aka sami yawaitar sabbin marubuta musamman mata, yaya kike kallon yanayi rubuce-rubucen da ake yi a halin yanzu, bambamcinsa da na da can baya, ci gaba ko ci baya aka sa samu?
•Maryam Nuhu Turau (803 950 0702):
Hajiya Halima, samuwar yawaitar marubuta mata da aka yi ya taimaka sosai wajen cunkushewar kasuwa ba kuma don komai ba, sai domin rashin samun wani tsari mai kyau da marubuta za su bi wajen fitar da littafinsu. Da a ce marubuta na da tsarin fitar da littafi da komin yawan marubuta ba za a samu cunkushewar kasuwa ba.
Ta wata fuskar, an samu ci gaba saboda ana kokari sosai wajen bunkasa adabi. Ta wata fuskar kuma an samu ci baya saboda rashin ingantaccen tsari.
•Isma’il Muh’d Aliyu (0806 030 9617):
Ina kika samo sunan Turau?
•Maryam Nuhu Turau (803 950 0702):
Malam Isma’il sunan dangi ne, kowa kuma yana amfani da shi a dangin namu.
•Nura Sada Nasimat (0813 199 4808):
Hajiya Maryam sannunki da kokarin amsa tambayoyin malamai. Ga nawa: (1) Ta wace hanya kike ganin za a magance matsalar satar fasaha ta yanar gizo-gizo? (2). Ta wace hanya za a inganta rubutu, maimakon a rika yi don nishai, ya kasance ana yi don kawo gyara ga halayyar da matasanmu ke ci ta bangarorin rayuwa (misali, rikice-rikice)? (3) A matsayinki na marubuciya wace gudunmuwa kike ganin marubuta suna ba wa al’umma?
•Maryam Nuhu Turau (803 950 0702):
Nasimat hanyar da ni ke ganin za a bi don magance satar fasaha ta yanar gizo daya ce. Marubuta su kafa kungiya mai karfi, ya kasance akwai alkalai da lauyoyi, kuma su samu kundin da zaiyi magana a kan hukuncin da wadannan barayi za su fuskanta.
Ina ganin inhar hukuma ta shiga ciki ana kai wadanda aka kama ana hukuntasu to za a samu saukin wannan matsalar.
Gyaran rubuto da tsara labari ya zama mai inganci, kuma ya kasance Gwamnati ta shiga cikin marubuta, malamanmu na jami’o’i ma su daure suna saka littattafan a manhajar karatu, in har sun yarda da ingancin rubutun.
Gaskiya marubuta na ba al’umma gudummuwa ta fuskoki da dama, misali akwai kula da tarbiyyar yara, koya zamantakewar aure, gyaran aure, cusama mutane yawan ibada karatu da dogaro da kai da sauransu.
•Sa’adatu Kofar Marusa (0902 629 46):
Wace shawara gare ki ga marubun Jihar Kastina, mussaman yanzu da zabe ke tunkarowa?
•Maryam Nuhu Turau (803 950 0702):
Sa’adatu shawarar da zan ba marubutan Katsina game da wannan zabe shi ne, a yi komai cikin ilimi da hikima. Siyasa ba ita ta hada su ba, don haka kada su yarda ta yi sanadiyyar rabuwar kawunansu.
Domin Tuntuba:
08033225331
wasanni
Bidiyo: Me Ke Hana Matan Fim Zaman Gidan Miji?
Daga Aliyu Ahmad
Babu shakka duk wanda Allah ya yi wa daukaka, walau mace ko namiji, ya kan kasancewa wani madubin dubawa ga masoyansa ko kuma masu adawa da shi, ta inda ko da wani abin alheri ko na sharri ne ya same shi ko ya same ta, cikin lokaci kankani zai yadu a duniya. Duk da cewa shi ma wanda Allah ya yi masa daukakar mutum ne kamar kowa, amma sai ya kasance ya samu kwarjini na musamman, wanda koda tuntube ya yi sai duniya ta sani.
Hanyoyin samun daukaka suna nan da dama, amma sai dai na dauki fannin jaruman finafinan Hausa ne, domin tsokaci kan wani abu da ya jima yana ci min tuwo a kwarya game da jaruman fim din Hausa mazansu da matansu. Su ma dai kamar sauran mutane suke, amma kuma Allah ya yi musu wata daukaka ta musamman, wanda hakan ya sa komai ya faru da su walau na ci gaba ko akasin haka, za ka ji duniya ta yi saurin dauka. Babbar matsalar da ta jima tana ci min tuwo a kwarya game da ‘yan fim din Hausa ita ce, yadda wasu daga cikin jarumansu maza da mata ke yawan auri saki, inda za ka ji ba wuya jaruma wance ko jarumi wane ya yi aure, amma ba da jimawa ba sai ka ji auren ya mutu.
Amma a wannan makalar tawa zan fi mayar da hankali ne a bangaren jarumai mata, domin na su ne ya fitowa fili. Ba komai ya jawo hankali ne ga rubuto wannan makala ba, sai irin yadda na yi kicibus da labarin mutuwar auren jarumai irin Rukayya Dawayya, Samira Ahmed, Sadiya Mohammed Gyale, Saima Mohammmed, Asma’u Sani da sauransu. Saidai a bangaren Dawayya ta nuna cewa ba ta taba tsammanin mijin da ta aura me yawan auri saka ba ne, domin kamar yadda ta ce tsohon mijin nata ya auri mata sama da ashirin da biyar yana sakarsu.
Ni a gani na Dawayya ta yi kuskure a wuri guda, inda ta ce a lokacin da ya neme ta da batun aure, ba ta tsayawa yin cikakken bincike sanin ko ya halin mijin da za ta aura din yake ba, sai kawai ta amince suka yi aure. Ta manta cewa aure abu ne wanda ake fatan idan an yi shi mutuwa ce za ta raba. Rashin binciken da ba ta yi ba ne ya sa wasu ke kallon kamar ta auri tsohon mijin nata ne saboda abin hannunsa, duk da cewa ba lallai ba ne hakan ya zama gaske, idan aka yi la’akari da cewa ita ma Allah ya hore mata arziki daidai rufin asiri. Yawan fitowa daga gidan miji da yawancin ‘yan matan fim suke yi, za mu iya cewa ba bakon abu bane ga masu bibiyar harkar finafinan Hausa.
Sannan kuma mutuwar auren ‘yan matan fim din ba ya tsaya kan ‘yan matan kadai ba ne, har da wasu daga cikin jarumai mata da suke fitowa a matsayin iyaye, inda za ka ga su ma sau da yawa idan suka yi aure ba su cika jima wa a gidan mijin ba. Don haka ne na ga ya kamata na dan yi jan hankali ga ‘yan matan fim din game da yadda suka dauki fitowa daga gidan miji ba wani abu ne mai wuya a gare su ba. Duk da na san cewa wasu daga cikin ‘yan matan fim din da ba su fahimce ni ba, za su iya cewa ai ba ‘yan matan fim kadai ba ne suke fitowa daga gidajen mazajensu, domin abu ne wanda za a iya cewa ya zama ruwan dare gama gari a akasarin kasashen Hausawa.
To amma su sani fa, ko da a yau za a ce an saki mata fiye da dubu wadanda duniya ba ta san su ba, babu wanda zai yi magana, amma da zarar an ce yau an saki jaruma wance, to na tabbata duniya za ta fi mayar da hankali a kai saboda daukakar da Allah ya yi mata. Babbar abar tambaya a nan ita ce, wai me ke jawo wa ‘yan matan fim ba sa jima wa a gidajen mazajensu? Matsalar daga ‘yan matan fim din ne ko kuma daga mazajen da suke aura ne?
‘Yan matan fim din ne ke zaben tumun dare ko kuma mazan da ke aurensu ne ke zaben tumun dare? Ko kuma son duniya ke rudars su har ta kai su ga ba sa iya zama a gidajen mazan idan sun yi aure? Ko zaman kulle ne ‘yan matan fim din ba za su iya jurewa ba, shi ya sa suke saurin fitowa daga gidajen mazan nasu, kasancewar a lokacin da suke masana’antar fim suna da ‘yancin su je duk inda suka ga dama sabanin idan sun yi aure?
Ko dai son duniya ne ya yi wa ‘yan matan fim din katutu a zuciya? Ko kuma irin abin nan ne da Hausawa ke cewa kuda wajen kwadayi yake mutuwa, ma’ana da zarar ‘yan fim din sun ga namiji da dan rufin asiri sai nemi ya aure su, inda shi kuma da zarar ya gama biyan bukatarsa sai ya sake ta? Wasu na ganin kamar ‘yan fim din ba su son zama a gidajen mazajensu ne idan sun yi aure, saboda sun saba da koda yaushe suna cikin sakewa na zuwa inda duk suka ga dama a lokacin da ba su da aure, yayin da wasun su kuma ake ganin sabo da samun abin duniyan da suka yi ne a dalilin fim ke hana su zaman gidan miji, inda wasun su kuma ake zaton sukan samu matsala ne daga bangaren ‘yan uwan mijin, inda za ka ga ana yawan muzguna mata tare da goranta mata na cewa dansu ya auro ‘yar iska, wanda kuma da zaran jarumar ta ga ba za ta iya jure wa ba, sai ta nemi mijin nata ya sake ta.
Haka kuma daga cikin ‘yan matan fim din, akwai wadanda ake zaton suna fitowa daga gidajen mazajen na su ne, bayan sun gano cewa wanda suka aura din ya yi musu karyar shi mai arziki ne, amma daga bisani bayan an yi auren sai su gano cewa shig-shigo ba zurfi aka yi musu, wanda bayan sun gano gaskiyar lamarin sai rashin fahimta ya yi ta shiga tsakaninsu har ta kai ga an ba su takardarsu. Domin wasu mazan bincike ya nuna cewa suna iya kashe ko nawa ne su auri jarumar fim, amma da zarar sun gama biyan bukatarsu, sai su sallamo ta.
Amma ba za a ga laifin mijin ba, saboda jama’a da dama sun fi ganin lafin jarumar fim a duk lokacin da aka ce aurenta ya mutu, koda kuwa tana da gaskiya. Maganar gaskiya, ko ma dai me ke jawo yawan mace-macen auren ‘yan matan fim, ya zama musu wajibi su yi karatun ta nutsu, su kuma gane cewa aure shine darajar duk wata ‘ya mace, sannan kuma su sani cewa rashin zaman gidan mijin da ba sa yi ya sa da yawan mutane ke tabbatar da zargin da ake yi musu na cewa ba su son zaman aure, domin a duk lokacin da aka ce auren wata ‘yar fim ya mutu, ba a taba tunanin cewa ta fito ne bisa wasu kwararan dalilai, ko da kuwa daga bangaren mijin ne aka samu matsala.
Sannan kuma kada giyar daukakar da Allah ya yi miki ya hana ki zama a gidan miji a duk lokacin da ki ka yi aure, inda a tunaninki an manta da kenan a masana’antar fim saboda kin yi aure. Ya kamata ki kasance mai hakuri da kuma danne son zuciyarki a duk lokacin da aka ce kin yi aure. Sannan kuma ya kamata a ce an samar da wasu dokoki da za su sa a duk a sanda auren wata jarumar fim ya mutu, ba za ta sake dawo fim ba idan har ba tare da wasu kwararan hujjujoji ba, wanda yin hakan zai sake wanke masana’antar daga zargi. Sannan kuma duk wata daukaka da za ki samu idan har ba a gidan mijinki ki ke ba, to da sauran rina a kaba.
Zan kuma yi amfani da wannan dama na mika jinjina ta musamman ga wasu ‘yan matan fim din da suka yi aure, wadanda tun daga lokacin, sun ci gaba da zama a gidajen mazajensu, ba tare da sun samu matsalar da har ta kai ga sun fito ba, wato irin su Aisha (Fatima) Ki Yarda Da Ni, Mansura Isah, Safiya Musa, Wasila Isma’il, jarumar fim din ‘Wasila’ ta yi aure yau sama da shekaru 13, tana zaune tare da mijinta (dan jarida ne kuma sananne), Safiya Musa, Fati Ladan, Fati K.K., Fati Karishma, Maryam Hiyana, sai Maijidda Abdulkadir, Maijidda Ibrahim, Zainab Idris, Bilkisu Jibrin, Khalisa Muhammad da sauransu da dama.
Ina kuma yi musu fatan Allah ya sa mutuwa ce za ta raba su da mazajen da suka aura. Su kuma sauran yan matan fim din su ma Allah ya ba su mazaje nagari har ta kai ga su ma mutuwa ce za ta raba su da gidajen mazansu idan sun yi aure.
Gyara kayanka dai, ba ya taba zama sauke mu raba. Don haka a duk lokacin da na samu labarin auren duk wata ‘ya mace ya mutu musamman ma ‘yan matan fim da duniya take yawo da mutuwar aurensu a duk lokacin da hakan ta auku, na kan ji bakin ciki.
•Aliyu ya rubuto ne daga Abuja, za a iya samunsa a: 07069139120
Bidiyo: Saira Ya Fara Daukar Fim Din Da Ba A Taba Yin Kamarsa A Kannywood Ba
Daga Mubarak Umar
Shahararren kamfanin shirya finafinan Hausa, Sarai Mobies, ya fara shirya wani kayataccen fim wanda a tarihin masana’antar za a iya cewa ba a taba yin irinsa ba, domin ana sa ran za a dauki kusan wata shida kafin a kammala shutin dinsa gaba daya.
Shi dai wannan sabon shirin mai suna Labarina, ya samo asali ne daga kiraye-kirayen da manyan masana harkar fim na duniya ke yi na ganin Kannywood ta fara shirya finafinai masu dogon zango watau siris (Series), ta yadda za a rika goyayya da sauran masana’antun duniya.
Finafinan Siris, wanda a yanzu suke tashe a kasuwar fim ta duniya, ba a saba yin su bisa tsari na yadda za su dace a manyan finafinan kasashen duniya a masana’antar Hausa ba, shi ya sa ake ganin wannan shi ne karo na farko da wani darakta ya bugi kirji tare da kaddamar da shirin fim wanda mai kallo zai shafe kusan awa 24 yana kallo bai kare ba.
Da yake bayani game da makasudin yin fim din, kwararren darakta Malam Aminu Saira, ya ce ya yi wannan tunani ne bisa irin kiraye-kirayen da masana da kuma ‘yan kallo ke yi na son a yi fim mai dogon zango, inda ya ce, “duniya yanzu ta ci gaba, harkar fim gudun yada kanin wani ake yi, shi ya sa muka yi babban shiri ta hanyar bullo da irin wannan salo da zai canja tafiyar Kannywood.”
“Finafinan Siris suna samun karbuwa a duniya, tuni sauran masana’antu sun yi nisa da wannan tsarin tun shekrau aru-aru. Duk da cewa a baya an yi, amma wannan karo ba irin wanda aka saba gani ba ne.” In ji shi.
Har ila yau ya kara da cewa, fim din Labarina, ya samu kayatacce labari, wanda wata matashiyar budurwa ke bayar da labarin irin tashin hankali, matsaloli da kalubalen da ta fuskanta a rayuwarta.
Ya ce, “jaruman fim din suna da yawan gaske, lokaci ne zai bai wa ‘yan kallo damar ganin su daya bayan daya. Kasanewar labarin yana da tsayi, dole ne a ga jarumai kala-kala, da wadanda ake damawa da su a Kannywood da kuma sabbin fuska.
Haka zalika ya ce daga cikin manufar shirya irin wannan katafaren fim akwai batun bunkasa harkokin tattalin arzikin Kannywood. A cewarsa, fim irin wannan mai tsayi, da yake bukatar mutane da yawa, dole ne zai taimaka wajen samawa dimbin matasa ayyukan yi, tun da ba fim ne da za a yi shi na awa biyu ko uku ba.
“Yawan mutane shi ne kasuwa, kuma daga cikin burinmu akwai batun kara bunkasa tattalin arziki da kasuwancin fim. Saboda haka Labarina zai tattara mutane masu yawan gaske, wanda hakan zai kara janyo wasu sabbin mutane cikin masana’antar domin sama musu ayyukan yi.
Da yake amsa tambaya kan ko wata kwangila kamfanin nasa ya samu domin shirya shirin, Saira ya ce, sam abin ba haka ba ne, inda ya jaddada cewa fim din hadin guiwa da Saira Mobies da kuma Rainbow, watau kamfanin da zai yi dillanci da kasuwancin fim din.
Sai dai kamar yadda ya shaida mana, tuni wasu gidajen talabijin sun fara kai wa shirin farmaki ta hanyar bayyana sha’warsu na sanya hannun jari, amma Malam Saira ya shaida musu aikin gama ya gama, sai dai su tari gaba, domin wannan shiri kamfanin Rainbow ne zai yi kasuwancinsa.
Babban abin da yake jan hankali al’umma game da fim din shi ne, na har yanzu ba a fara bayyana jaruman da za su hadu a cikin shirin ba, duk kuwa da cewa tuni an yi nisa da daukar wasu sashen fim a birnin Kano, kafin daga bisani a koma Abuja.
Duniyar Halittu: Dinosaurs: Da Gaske Sun Zauna A Duniya Kafin Bil Adama? (2)
Daga Marigayi Tahir I. Gwantu
Amma fa wannan halitar ba dan Adam ba ce, a’a, akwai halittun da suka rigayi bil Adama zama a gidan duniya. Daga bisani, shi kuma ya zo. Wannan bayanin ma, kur’ani ya tabbatar da shi a sura ta 2 aya ta 30, tun kafin ma ci gaban ilimin dan Adam ya gano hakan.
Ruwayoyin tarihi, gami da kissoshin Musulunci dai, sun kawo cewa an yi wasu halittun da ake ce da su Bunna; bayan su kuma aka sake yin wasu da ake ce da su Jinna.
To, ta yaya aka gano cewa wadannan halittu sun taba rayuwa a doron duniya, kafin wanzuwar bil Adama? Ilimin nazarin kimiyyar guggbin halittun da suka mutu suka rududduge, kasusuwansu kuma suka daskare suka zama abin da, a Hausance, za a iya kira da takanda-ba-kashi ba, wacce a turance kuma ake kira da Fossils ne, ya bankado kasusuwan irin wadancan halittu a sassa da dama na duniya.
Sannan kuma, yana da muhimmancin gaske a san da cewa, kashin jikin halittar da ake magana a kai din, wani abu ne da kusan ana iya cewa, ba ya taba rubewa a ciki kasa ko a wajen ta, ta yadda za a neme shi kwata-kwata a rasa. Sabo da haka, ta wannan hanyar ce masanan suka gano kasusuwan halittun da suka gabaci dan Adam din zama a doron duniyar Subahana. Irin wadannan masana, a turance, ana ce da su PALEONTOLOGISTS. Shi ilimin kuma, PALEONTOLOGY (ana furta Kalmar da faliyontolojists da kuma faliyontoloji).
Su kuma halittun da aka gane cewa sun taba wanzuwa a wannan duniyar kafin bani Adama mu zo, a isdilahin wannan ilimin, an kira su da da DINOSAURS (dainosos). Wannan kalma dai ta samo asali ne daga harshen Girkanci, wato GREEK. Kuma tana da bangarori biyu ne; ‘DINO’, wadda ke nufin masifa. Sai kuma bangaren Kalmar na biyu, wato SAURS, wanda ke nufin kadangare.
Don haka ne ma, wasu masanan, Hausawa ke ce ma wadancan halittu “Kakan kadangaru.” In za fassara ta a haden ta zuwa Hausa kai tsaye, to ana iya cewa masifaffen kadangare.
Wadnnan masifafffun kadangaru, kamar yadda Girkawa suka kira su, sun wanzu a wannan duniyar ce shekaru miliyan 230 da suka gabaci zuwan bil Adama; kamar yadda wata ruwayar ilimin binciken ta nunar. Wata ruwayar kuma ta ce a’a, sun zauna a duniya ne suka shude da kimanin shekaru miliyan 65, daga bisani kuma dan Adam ya zo yana nasa yayin, a cikin ta, har zuwa yanzu.
Do'stlaringiz bilan baham: |