Musa Muh’d Danmahawayi
email:musaleadership@gmail.com 0816196 4340
ADABI: Ire-Iren Abincin Hausawa Na Gargajiya Da Wasu Da Suka Aro (2)
Daga Ishak Guibi
28. Alkubus. Hausawa sun aro alkubus ne daga larabawa. Da fulawa ake yin sa.
29. Algaragis ma, abinci ne na larabawa da ake yin sa da fulawa, da yis, da suga. Za a samu rushin wuta, a sa kwanon suya, sai a rika mulmulawa ana sa shi yana gasuwa kamar burodi. Ba kamar su cincin da ake soyawa shi da mai ba. Ana cin shi da su kunun aya, ko su jinja, wasu ma su sha shayi da shi.
30. Alkaki. Alkaki ma da jin sunansa an aro shi ne daga larabawa. Ana yin sa da alkama wacce ita ma aro ta aka yi daga larabawa, sai a barza, a kwaba, sai a nada shi kamar gammo, a sa shi a cikin mai, sai a dafa suga da lemun tsami ko tsamiya, in an gama soyawa sai a dauko a zuba ruwan sugar da ruwan lemun tsamin a zuba a kan alkakin. Shi alkakin bayan an nada shi sai a sa a cikin mai a soya.
31. Burabusko. Burabusko abinci ne na barebari da Hausawa suka ara. Ana yin sa ne da tsakin surfaffiyar masara. Sai a wanke shi ya dan sha iska kadan, sai a dora ruwa a wuta, idan ya tausa sai a sa dan mangyada kadan, sai a zuba tsakin, idan aka zuba tsakin a wuta aka rufe, ba da dadewa ba zai tsotse. Ana cin burabusko da miyar tumatir, ko miyar taushe. A garin barebarin suna ci har da miyar kuka.
32. Kato da lage. Dawa tsaba ake dafawa da wake. A dafa gero da wake kamar yadda ake dafa shinkafa da wake. Ana ci da mai da yaji.
33. Dankali. Abinci ne cikin mabunkasa kasa. Ana dafa shi ko soya shi, ana ma yin faten dankali, da alalen dankali. Wasu kan ce masa dankalin Hausa.
34. Walahan. Wasu kan ce mata makani ko gwaza. Ana dafa dankali a ci da kuli, ko da mai da yaji, wasu su hada shi da miya.
35. Doya. Ana gasa doya, ko dafa ta, ko soyata, ko yin fate da ita, ko alalen doya, ko a rangada sakwara da ita. Ana hada shinkafa da doya, ko wake da doya, ko taliya da doya, ko kosai da doya.
36. Awara. Ana yin sa da waken suya. Ana jika waken ne, idan ya jiku sai a markada, sai a tace shi kamar kullu. Sai a sa a wuta idan ya dahu zai dundunkule. Sai a kara zuba shi a cikin abin tatan kamu, a matse shi sosai, idan aka gama matse shi, sai a yanyanka shi, a sa shi a cikin mai a soya.
37. Dantamalele. Da shasshaka ake yin sa. Ana yi da tsakin masara, wasu kuma suna yi da kamun koko. Aka sa a wuta aka talga, idan ya dahu, sai a zuzzuba a faranti, sai a zuba masa mai da yaji, sai a yanka kayan miya a kai.
38. Shasshaka. Ana yin shasshaka da tsakin masara ko tsakin shinkafa. Idan aka sa tsakin a wuta, ya nuna, zai yi kauri, sai a dinga debowa da ludayi, ana zuzzubawa ana jejjerewa a faranti. Sai a sa ludayi ana masa dan rami a tsakiya, sai a zuba mai da yaji.
39. Kalallaba. Wasu suna ce mata wainar fulawa. Ana yin ta ne da fulawa, da kwai da ake sa wa a cikin kwabin fulawar. Idan aka gama kwaba shi ruwa-ruwa, sai a sa tattasai, da magi, da albasa, da tattasai, da gishiri, sai a samu abin soyawa. Soya shi ake yi da mangyada ko manja.
40. Dansululu. Ana yin sa ne da garin alubo. Ana kwaba shi da magi, da gishiri sai a mulmula shi, a zuba a cikin tafasasshen ruwa ya dahu. Idan ya dahu aka tsame, ana cin shi da mai da yaji, ko da miyar tarugu.
41. Gurasa. Ana yin gurasa da fulawa da yis a kwaba. Idan ya tashi, sai a samu tukunyar da ake yin gurasa. A sa a rushin wuta, sai a rika dibar kwababbiyar fulawar ana mannawa a jikin tukunyar. Har ta gasu. Ana gama gasawa, sai a ci shi da ko miya, ko kuli.
42. Dantsirku. Ana yin sa ne da kifi. Ana tafasa kifin, sai a gyara shi, a cire kayar, sai a jajjaga shi da tarugu, da magi, da albasa, da gishiri. Sai a samu kwai, sai a rika dibar wannan kifin, ana mulmulawa, ana sa shi a cikin ruwan kwan, a sa a mai, a soya.
43. Madi. Ana yin sa da dinya, da barkono, da citta, da kanumfari, da suga.
44. Hanjin ligidi. Ana yin sa ne da suga, da tsamiya ko lemun tsami. Idan ya dahu, sai a nada takarda, ana diba da cokali, ana zuzzubawa. Sai a sa tsinke a tsakiya.
45. Garin bididis. Ana yin garin bididis da kwallon kukar fulani. Idan aka samu kwallon sai a soya shi, idan ya soyu, za a ji yana kamshi. Idan aka gama soyawa sai a daka shi. Idan aka daka shi, sai a tankake a sa masa suga. Sai a dinga sha.
46. Garin kuka. Ana yin sa ne da kukar fulani, sai a daka kukar, a tankade, a zuba mata suga. Shi ke nan sai a dinga sha.
47. Tuwon madara. Ana samun madara da suga, sai a dafa suga, a zuba a kan madarar, sai a tuka, in an gama tukawa sai a juye, a yanyanka shi.
48. Gullisuwa. Ana yin ta ne da madara da suga. Ana kwaba madara da suga a mulmula shi. Idan aka mulmula sai a dinga zubawa a cikin mai, ana soyawa.
49. Kanwar Shagari. Ana yinta ne da suga da madara.
50. Balle kwabo. Wasu suna ce mata alewar gyada. ana yin ta ne da suga da gyada.
51. Mandula. Akwai wata alewa da ake ce mata alewar mandula. Ana yin ta ne da suga, da madara, da tiri.
52. Zogale. Ana masa kirari da zogala gandi ana dibarka kana tsaye. Zogala na cikin abincin Hausa dangin ganyayyaki na kayan lambu da ke matukar amfani bangaren a ci a koshi da kuma magani. Ana dafa shi, bayan ya dahu ana kwadanta shi da kuli, da kayan miya.
53. Dinkin. Dinkin ma na cikin ganyayyaki. Shi ma ana dafa shi ne, a kwadanta shi da kuli da kayan miya.
54. Rama. Ita ma rama ana kwadanta ta ne da kuli, a kara mata kayan miya don armashi da magani.
55. Yakuwa. Ana dafa ta ne, a kwadanta ta da kuli da kayan miya. ‘ya’yan yakuwa su ne zobo.
56. Tafasa. Ana kwadanta tafasa kamar yadda ake yi wa zogale.
57. Lansir. Ana kwadanta shi ne da kuli, sai a zuba masa kayan miya.
58. Latas. Shi ma ana yayyanka shi a kwadanta shi da kuli.
59. Kabewa. Ana kwadanta kabewa da kuli.
60. Kabeji. Ana kwadanta kabeji.
61. Goji. Ana kwadanta goji, kuma ana cinsa a cikin abinci.
62. Alaiyahu. Wani ganye ne da ake yin miya da shi, ko a dafa abinci da shi. Ana yin miyar taushe da shi, da miyar alaiyahu.
63. Alewa. Ana yin alewa da suga, wata da tsamiya da lemun tsami. Akwai alewar dinya, wasu na ce mata alewa da kayan yaji. Akwai alewar da ake kiranta da amarya da lillibi. Akwai alewar gyada. akwai alewar madara.
64. Nakiya. Ana yin nakiya da shinkafa da suga. Ana soya shinkafa, sai a nika ta, a hada da citta, da kanumfari da barkono. An fi amfani da ita a wajen bikin Hausawa.
65. Rake. Wasu su ce kara ko takanda. ana shan rake haka nan don yana magani iri-iri, kamar ciwon hanta, da gyambon ciki da maganin yunwa, ga kuma wanke hakora da kashi kishi. Ana kuma yin suga rawar doki da rake. Da ake kira da mazankwaila. Sugar da aka ce komai yawanta, ba ta yi wa mutum illa kamar sikari. Akwai rake kwandagi, da takanda, da kwama, da farin rake, da jan rake.
66. ‘Yar yau. Ana yin ta ne da surfaffen gero, a nika shi, a zuba masa yis da kubewa, sai a soya.
67. Funkaso. Ana yin funkaso da alkama, ko fulawa, ko da garin samanbita. Ana cinsa da suga ko da miyar taushe.
68. Romo. In an dafa nama, akwai ruwan naman da yake zama romo. A nan ma ake samun farfesu. Akwai farfesun kifi, da farfesun nama.
•Guibi, sashen Harsuna na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Kaduna
guibi14@yahoo.com
08023703754.
adabi: Sharhin Littafin ‘Rundunar Sadaukai’
Sharhi na daya daga cikin fitattun shirin zauren ‘Gidan Marubutan Hausa,’ wanda Malama Fadila H. Aliyu Kurfi ta assasa kusan shekaru biyu da suka gabata a dandalin sadarwar ‘WhatsApp’. Zauren ya hada yawancin fitattun marubuta wadanda duniyar rubutun litattafan Hausa ta san da su a yau.
Marubutan su kan hadu ne su tattauna, su bayar da dukkanin gudunmawa kan harkar raya Adabin Hausa ta hanyar sadarwar zamanin ‘WhatsApp’. An ware ranar Asabar din kowane mako ta kasance ranar da ake gabatar da sharhi kan litattafan marubuta, wanda Malam Mohammad Zailani tare da Hajiya Amina Abdulsalam suke gabatarwa.
A makon da ya gabata, malaman sun yi fashin baki ne kan litattafan jagorar zauren, wato Malama Fadila Kurfi, inda suka yi sharhi kan wani littafinta mai suna ‘Rundunar Sadaukai’.
Farko dai jagoran shirin ya yi tsokaci ne da shimfida kan ainihin ma’anar SHARHI a sigar fashin bakin littafi.
•Muh’d Zailani (803887 0910):
Kafin mu ce komai, za mu yi shimfida kan ma’anar Sharhi - Sharhi na nufin yi wa wani abu karatun tsaf ko kallon natsuwa sannan mutum ya fadi raayinsa a kan wannan abin, amma a bisa ga ilimi da gamsassun hujjoji.
Don haka sharhin littafi a mahangar masana ya na nufin jerin tsararrun takardu da aka buga masu dauke da sako ko sakonni, wadanda aka hada su wuri guda tare da bango mai dauke da suna, Wanda yawan shafukansa ba su gazawa 49 ba. (Fassara ce daga Turancin masana irinsu UNESCO, Ayna, Sani 2013 da sauransu).
Saboda haka za mu iya cewa; Sharhin littafi shi ne bibiya ko karanta littafin da wani ya wallafa ko kafin ya wallafa domin a fitar da kura-kurai, karawa mai rubutun karfin guiwa, auna daraja ko ba wa littafin matsayi da samar mashi da matsaya wadda ta ke daidai da fahimta tare da hujjojin wanda ya nazarci littafin.
-Masu Yin Sharhi - Kowa ne mutum idan yana da sha’awa, ilimin abu bisa hujja kan iya zamowa mai sharhi.
-Abin Lura - Ba lallai ba ne ba, masu sharhin littafi (koda kuwa lokaci, wurin zama, iliminsu ya zo daya ba), su kasance da ra’ayi iri daya wurin bayyana ra’ayinsu a kan littafin da su ka nazarta. Saboda haka, wani mutum kan iya yin sharhin littafi ra’ayinka bai zo daya da shi ba, saboda kilan maratayar da ya yi amfani da ita wurin rataye littafin, ba irin ta ka ba ce ba. Abin bukata dai shi ne kada mai sharhi ya sa (Personal interest) a kan littafin da zai yi wa sharhi, sannan kuma ya gina sharhinsa bisa hujjoji. Wannan shi ne somin tabi dangane da hikima da balagar da ke cikin SHARHI.
•Sunan Littafi: ‘Rundunar Sadaukai’
•Sunan Marubuci: Fadilah H. Aliyu Kurfi
•Shekarar Dab’i: 2015
•Kamfanin Da Ya Yi Aikin Buga Littafin: Fancy Printing & Pub. Co.
•Yawan Shafuka: 144 (na daya da biyu).
•Farashin Littafi A Kasuwa: N150 - N200 (na daya da na biyu).
•Jigon Littafi: Zalunci da Makirci
•Mai Sharhi: Kwamared Moh’d Zailani Sani (BLIS, NDE, PDE)
Littafin Rundunar Sadaukai, kirkirarren labari ne na yaki wanda a ka rubuta shi don masu sha’awar karatun littattafan jarumtaka, domin littafin ya zo da labarin wata annoba ce da duniyar wancan lokaci ta ke fuskanta a duk shekara, wadda idan annobar ta wanzu, ta kan haddasa mutuwa da jigatar halittun duniya kama daga mutane, aljannu, dabbobi, tsuntsaye da duk wasu halittun duniya (shafi na 1 da 2, cikin littafi na 1).
A wata shekara ne, bayan annobar ta wuce wasu sarakai uku, su ka tayar da rundununar sadaukai don neman maganin annobar. Rundunar Sadaukance kuwa ta samu nasarar kawo karshen annobar bayan abubuwan mamaki, al-ajabi, tsoro, firgitarwa, rudarwa, hargitsarwa, fargaba da razanarwa sun afku ga sadaukan rundunar, wanda suka yi amfani da karfin jarumtakarsu, tsafinsu, iliminsu, wajen yakar duk wata matsala ta aljani, dabba, mutum da maridai da suka ci karo da su.
Akwai soyayya mai rikitarwa, makirci, zalunci da tausayi a cikin labarin. Abin sha’awa ga littafin, shi ne yadda labarin ya nuna tsananin tasirin addinin Musulunci a kan sauran addinai
•Zubi Da Tsari - An tafiyar da labarin littafin bisa ga tsarin zube marar babi-babi ko kashi- kashi, a mike santal labarin ke tafiya ba kwana, ba kauce-kauce tun daga farko har karshe. Haka kuma, labarin littafin cike yake da tsari mai birgewa da ban sha’awa, ba ga wanda ya karanta kadai ba, har ga duk wanda ya bude shafukan littafin, domin an kawata labarin littafin da sakin layuka wadatattu masu daukar idanun masu kallo, an kuma kamanta sosai wajen amfani da wasu daga cikin ka’idojin rubutu.
•Salo - Littafin ya zo da wani sabon salo mai kayatarwa da jan hankalin mai karatu ta yadda zai yi wuya a ajiye littafin ba tare da an karasa karanta shi ba, idan har an fara. An yi amfani da salon nuna jarumtaka da soyayya ta yadda aka ringa amfani da kalmomi masu ma’ana wajen bayyana salon yaki iri-iri, da nuna jarumtaka a fagen fama. Haka kuma, an kawata labarin da kalaman soyayya masu gardi da sanya nishadi ga mai karatu.
•Jigon Littafi - Hakika marubuciyar ta yi namijin kokari wajen tafiyar da labarin littafin a kan jigonshi na Son rai da wani babban boka ya nuna na samun mallakar diyar wani mashahurin Musulmin Sarki, wanda tsafi ko asiri bai tasiri a cikin kasarshi, amma duk da hakan sai da wannan hatsabibin boka ya samu nasarar sato diyar sarkin, ya tsafance ta, tare da daukarta ya killace su (shi da ita) a wani kebantaccen kuma tsafaffen wuri. A sabili da wannan tsafi da kebancewar da boka su ka yi, ya janyowa duniya matsala, ta hanyar samar da wata annoba a duk karshen shekara wadda ke yin watanda da duk wasu abubuwan halitta da ke rayuwa a saman duniya, har ma da aljannu da ke rayuwa a duniyar boye. Kaf din labarin littafin an tafiyar da shi ne, akan kokarin ruguza tsafi/asirin da wannan boka ya yi don samarwa da duniya lafiya a bisa ga annobar da ke faruwa ta dalilin wannan tsafi na hatsabibin boka.
•Ka’idojin Rubutu - Hakika dole a yaba ma marubuciyar yadda ta kiyaye matuka (kusan kashi 70 a cikin 100) wajen amfani da ka’idojin rubutu, musamman doguwa da gajeruwar sassaukar nasaba. Abin a yaba mata ne, sai dai ire-iren kuskuren alkalami da kuma irin kura-kuren da ake kira ‘Typing/Computer error’. Misalan kura-kuren su ne:
- ko mai, a maimakon KOMAI
- inda, a maimakon IN DA
- aminta ce, a maimakon AMINTACCE. Da sauransu, da kuma sauran wasu yan kananan kura-kuran na ka’idojin rubutun (iyakar karamin sanina ne).
•Kammalawa da Shawara - Littafin ‘Rundunar Sadaukai’ littafi ne na fita tsara da nunawa a cikin Saanninshi na Jarumtaka, musammam yadda aka tuke labarin a 1 d 2 kadai (sabanin wasu da ke kai wa har littafi na 9)!
Ina mai bayar da shawara ga duk mai son karatun littafin jarumtaka/yake-yake da su garzaya a kasuwa su nemo littafin ‘RUNDUNAR SADAUKAI’.
•Shawara Ga Marubuciya - Ina mai kira da babbar murya ga marubuciyar a kan:
- Ta kara bada himma wajen ci gaba da samar da irin wadannan labarai.
- Ta kiyaye ambatar cewa wani zamani kafin zuwan Annabi (SAW) sai dai ta ce “Wani shudadden zamani da ya wuce ko a wasu shekaru masu yawa da suka gabata an yi wata...” da sauransu.
- Ta kiyaye kawo bakin kalmomi a cikin rubutunta, idan kuma an kawo su din to, a yi kokari wajen fassara su bisa ka’idar da ka’idojin rubutu su ka tanadar.
- Ta kiyaye kawo sunayen wasu taurari masu kama da juna, domin hakan kan iya rikita mai karatu, idan ba a yi sa’a ba, har da marubuciyar a yayin rubutawa (misali irin sunaye masu kama da ta yi amfani da su a littafin - Rahadun Nash, Rahadun Jush. Kuma fa ba ta alakanta su da juna ba).
•Kura-kuren Littafin - Duk da namijin kokarin da marubuciyar ta yi wajen ginawa da tsara littafin nata a bisa Jigo, zubi da tsari tare da salon yaki mai kayatarwa, hakan ba zai sa a gaza tsakuro wasu daga cikin kura-kuren da littafin ya kunsa ba kamar haka:-
•Saka Da Warwara- marubuciyar ta bayyana a cikin shafukan farko na littafin cewa wata annoba na faruwa duk karshen shekara, a fadin duniya wadda kan wargaza, jikkita tare da kashe rayukan mutane, aljannu, dabbobi, tekuna da koguna da dai duk wani abin halitta a doron duniya. Amma bayan tafiya ta yi tafiya, sai marubuciyar ta bayyana cewa wai duniyar kala -kala ce: akwai tsohuwa da sabuwa da wata can daban da ta taba shudewa.
•A cikin littafin an bayyana wani shahararen malami Islama da wani hamshakin Kafirin boko sun yi aikin bincike a tare. Anya kuwa wannnan ba kuskure ba ne ba? Cikakken malami Musulmi a ce ya na aiki tare da boka?
•An bayyana cewa an hada runduna ta jinsin halittun duniya, kowane jinsi dubu- dubu. Lissafin adadin yawan rundunar ya binkice ma marubuciyar (Shafi na 19, littafi na 1).
•An bayyana cewa mayakan su na haduwa ko wucewa ta wani ko hanya ce? Oho! Marubuciyar ta bayyana wadannan wuraren da wani harshe, wanda ba Hausa ba, kuma an ki fassara abin da Hausa (har na gama Mazarin littafin ban gane wane yare da fassarar abin da ta ke nufi ba.) Misalan abubuwan:
-Wadin Ma’u
-Wadin hayatun. Da sauransu.
•Yadda a ka rika bayyana wasu halittu da kowa ya san kamanninsu, aka nuna manya ne. Misali kunamu- an nuna wasu kunamu masu girma fiye da doki. Anya kau almarar ba ta wuce hankalin wasu masu karatun ba?
•An siffanta wani bakin duhu a wurare da dama, wanda har sadaukai ba su iya ganin tafin hannayensu, amma har suka rika yaki da wasu azabatattun halittu.
•An bayyana Sadauki Saif ya Musulunta tun a cikin littafi na daya, amma sai ga shi ya na rantsuwa da rana (shafi na 10-11, littafi na 2) sai kuma a can karahen labarin aka kuma bayyana cewa Sadauki saif din ya karbi Musulunci a ranar auransu.
•Akwai wata budurwa mai suna Kiran, wanda aka samo a wata duniya, wadda aka nuna tsakaninta da ‘Rundanar Sadaukai’ babu mai jin harshen wani, kuma har wai ta rika karanta wasu rubutu Sadaukan na amfani da karatun ba tare da an nuna akwai tafinta a tsakaninsu ba.
•Game Da Bangon Littafin - Tabbas, hotunan bangon littafin sun zanu radau, sun kuma nuna wani bangare daga cikin labarin littafi, uwa uba, tsarin bangon littafin ya bayyana ma’anar abin da ke cikin littafin (yaki).
Sunan littafin ma kau, tabbas ya bayyana ma’anar sakon littafin ko da kuwa mutum bai karanta ba, zai gane sunan littafin da tsarin hoton bangon cewa lallai labarin yaki ne. Sunan marubuciyar da ke rubuce a saman bangon littafin Fadila H. Aliyu Kurfi, wannan sunan an karya ka’idar suna, domin a Nijeriya suna guda uku ake amfani da shi, wato sunan farko, na tsakiya da karshe.
Bissalam, daga alkalamin Kwamared Moh’d Zailani Sani (BLIS, NDE, PDE) 803887 0910.
Bayan mai sharhi ya kammala, sauran malaman zaure suka fara tofa albarkacin bakinsu...
•Bashir Yahuza Malumfashi (0802 096 8758):
Comrade, sharhi ya yi kyau, kodayake ya kamata ka kula da ka’idojin rubutu. Misali, akwai inda na ga kana maida macen kalma namiji, akwai inda kake raba kalmar da ya kamata a hada, ko kuma ka hade inda ya kamata ka raba. Misali: Akwai inda ka ce: ‘samarwa duniya’ maimakon samar wa duniya. ‘Janyowa duniya’ maimakon janyo wa duniya. Akwai inda ka ce: ‘a wata shekara ne’ maimakon a wata shekara ce. Akwai inda ka ce ‘akan jigonshi’ maimakon a kan jigonsa. Akwai wasu kalmomi da kake rubuta su ba daidai ba. Misali: ‘raayi,’ maimakon ra’ayi. ‘Shaawa’ maimakon sha’awa. ‘Nazanarwa’ maimakon razanarwa dss.
Babu shakka ka yi matukar kokari amma abin sani shi ne, mai sharhi ya kamata ya kiyaye dokoki da ka’idojin rubutu, domin bayar da fa’ida sosai. Allah sa mu dace, amin.
•Rabi Yusuf Maitama (0806 554 9112):
Wannan sharhi ya kayatar da ni, zan nemi wannan littafi na karanta. Malama Fadila Allah ya kara basira.
•Shehu Harafi (0802 543 3394):
Na gamsu da wannan bayani Kwamared Zailani. Babbar matsalar wasu masu yin sharhin ba su san ma’an sharhi ko yadda ake yinsa ba. Haka kuma fito da gyara ko kura-kurai da suke cikin Littafi don a gyara dai-dai sabanin cin fuska.
Za Mu Ci Gaba.
Daga Gidan Marubutan Hausa ta ‘WhatsApp’
tattaunawa: Za Mu Wayar Da Kan Jama’a Batun Biyan Haraji A Kano —Yunusa Mai Karas
Alhaji Yunusa Abdullahi Danbazau (Mai Karas) Shugaban Karamar Hukumar Takai mai ci a yanzu, wanda shi ne mataimakin Shugaban Gamayyar Kungiyar Shugabannin Kananan hukumomin jihar Kano 44, a tattaunawarsa da wakilinmu Abdullahi Mohd Shekam ya yiwa gwamnatin Ganduje kallon tsanaki, musamman kan batun samarwa da jihar hanyoyin da zata dogara da kanta, ga yadda tattaunawar ta kasance.
Ranka ya dade ya kuke kallon matakin Gwamnatin Ganduje kan batun tattara haraji?
Alhamdulillahi! Kamar yadda na sha fada, ba canjin gwamnati aka samu ba, ci gaba kawai aka yi, saboda haka dorawa mai girma Ganduje ya yi kan ayyukan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Wannan tasa a jihar Kano mai girma Dakta Abdullahi Umar Ganduje yanzu haka ya bijiro da hanyoyin da jihar za ta ci gaba da dogara da kanta, musamman ganin yadda kasuwar man fetur ta fadi warwas a duniya. Kuma mu al’ummar Kano ba cima zaune bane, tarihi ba zai manta da cewar da arzikin gyada da auduga aka samu kudaden da aka hako man da wani bangare yanzu ke tinkaho da shi.
Saboda tsare-tsaren gwamnatin jihar Kano kan wannan lamari abin a godewa mai girma gwamna ne. Muna kira da babbar murya cewa jama’a su dauka wannan wani fage ne da ake son ganin kowa ya yi abinda ya kamata wajen bayar da tasa gudunmawar.
Amma wasu na ganin kamata ya yi a mayar da hankali kan batun karbar haraji ba…
Wannan hali da jama’a ke ciki ko shakka babu mu da muke tare da talakawanmu mun san haka, amma kamar yadda aka sani duk lokacin da aka tafka wata ta’asa wadda aka jima ana yin ta, idan aka zo batun gyara dole a dau lokaci, saboda haka jama’a muna fatan za a kara juriya, wannan haka lamarin yake, kuma muna da yakinin sauki zai biyo baya kamar yadda malamai suka ce bayan wuya sai sauki.
Shin ko’ina batun karashen ayyukan da tsohuwar gwamnatin Kwankwaso ta faro a baya?
Ba wata tababa a cikinsa, ko makaho ya shigo Kano ya san gwamnatin Ganduje da Kwankwaso abu guda ne, wannan tasa yanzu haka daukacin ayyukan da Gwamnatin Kwankwaso ta faro ana nan ana ci gaba da aiwatar da su, misali aikin gadar sama wadda ke kan titin Murtala Muhammad, haka ayyukan hanyoyin da ke kananan hukumomin jihar Kano 44, ana nan ana tattaunawa da ‘yan kwangilar domin kamo bakin zaren, dubi yaki da cutar polio wanda yanzu haka an yiwa cutar kurunkus ba sauran ta a jihar Kano.
Saboda haka Gwamnatin Ganduje ko shakka babu ‘yar manuniyace ga duk mai hankali, kasancewar ayyuka ake kokarin kammalawa bayan wadanda aka faro zuwan wannan Gwamnati.
Wane tabbas za ku iya bai wa jama’ar Kano cewar Ganduje ba zai ba su kunya ba?
Kasancewar Gwamna Ganduje bafilalcen asali ne mai kunya, shi yasa ka ji wasu ‘yan ihun ka banza masu baki da kunu ke ta wasu maganganu marasa tushe balle makama, amma duk wanda ya san Ganduje ya san ba kanwar lasa ba ce ta fuskar ayyukan kyautatawa al’umma, don haka ya taso a cikinsa kuma ya ci gaba da aiwatarwa gwargwardon iko. Zamu yiwa jama’a fashin baki sannan kuma mu warware zare da abawar garabasar dake cikin wannan gwamnati mai albarka.
Kafin mu je nan, wane karin haske zaka yi game da shugabancinka?
Gaskiya ne da bahaushe ke cewa kowanne tsuntsu kukan gidansu yake yi. Mu a Karamar hukumar Takai ayyukan da muka samarwa al’umma zamu iya cewar kwalliya ta biya kudin sabulu, kuma idan ka hada shi da ayyukan gwamnatin su waccanen ka, ai ina tabbatar maka ko ba a gwada ba linzami yafi karfin bakin kaza. Al’ummar karkara akwai abubuwa muhimmai da ya kamata duk wani shugaba ya fi mayar da hankali a kansu. Wannan tasa a Takai muka fara duban halin yadda zamu kyautatawa ma’aikata domin samun sukunin ci gaba da gudanar da ayyuka yadda ya kamata.
Wane hobbasa ka yi domin kyautata rayuwar matasa?
Ai duk kananan hukumomin dake jihar Kano mune a sahun gaba wajen kyautata rayuwar mata da matasa, wannanan ne ma ya sa bangaren CRC muka bayar da umarnin koyawa mata sama da dari uku sana’u daban-daban, tare da basu jarin naira dubu goma-goma kowaccensu, haka suma maza muka koyawa guda 100 sana’ar noma da sauran sana’u aka kuma basu garmunan shanu, aka koya wasu sana’ar wayarin, kanikanci da sauransu. Wasu kuma masu yawa muka sama masu karatu a makarantun harkar noma dake Danbatta, Koyon Harkar Raino, Nazari Kwamfuta, Makarantar Wasanni ta Karfi da kuma makarantar koyar da sana’u ta D/Tofa.
Sannan kuma ganin yadda aka fuskanci wani lokaci da abubuwan bukata suka shiga halin ni ’yasu, Karamar hukumar Takai ta dauki gabaren raba agaji ga mabukata, tallafawa wadanda suka gamu da ta’adin ruwan sama da sauran gudunmawar da ya kamata duk wani dan asalin karamar hukuma ya amfana.
Do'stlaringiz bilan baham: |