Burin Zuciya: Sako Ga Maigida:
Me Za Ka Aikata Idan Matarka Ta Bata Maka
Daga Abban Umma
Masu karatu da membobin wannan majalisa mai albarka, a yau na dan tsakuro muku wata tsaraba daga shafin ‘Zauren Fikhu’ a dandalin ‘Facebook’ domin amfaninmu baki daya.
Zauren ya shahara, inda malamai ke bayanai da dama da suka hada da dukkanin al’amuran rayuwa a addinance. Misali, ko ka san abin da zai same ka idan matarka ta bata maka rai? Maza karanta wannan ka sha mamaki:
Ko kasan cewa duk lokacin da matarka ta ‘bata maka rai in dai kayi hakuri domin Allah, akwai wasu alkhairai da zasu sameka kamar haka:
1. Idan Matarka ta bata maka rai, nan take matanka na gidan Aljannah su mayar da martani a gare ta (sai dai ba za ku ji ba). Ta ce: “Ke da kike ta bata masa rai, ai ya kusa dawowa zuwa gare mu, inda zai dauwama cikin farin ciki.”
2. In har ka yi hakuri domin Allah sai Allah ya rubuta maka lada mai dimbin yawa, ba tare da lissafawa ba. Kamar yadda Ya ce, “Ana bama masu hakuri ne ladansu ba tare da lissafi ba.”
3. Idan ka yi hakuri domin Allah, to nan take Allah zai zama naka. Wato Allah yana tare da masu hakuri.
4. Idan ka yi addu’a, Allah zai amsa maka a lokacin. Domin Allah yana saurin amsa addu’ar wanda aka zalunta. (Ka ga za ka iya rokon Allah ya canza halayenta, ko kuma ya canza maka wacce tafi-ta alkhairi).
5. Allah zai daukaka darajarka a duniya da lahira saboda albarkacin hakurinka. (Hakuri, afuwa, ba su kara maka komai sai dai girma a wajen Allah).
6. Ubangiji zai kara maka yawan matan da za a ba ka a gidan Aljannah. Tun da za ka samu karin daraja a Aljannar, kenan za ka samu karuwar ni’imah a cikinta
7. A ranar lahira Allah zai kira ka a gaban dukkan halittu, sannan ya ce maka: “Ka shiga Aljannah ta duk kofar da kake so.” (Haka Manzon Allah (saw) ya ce: “Duk wanda ya danne fushi, alhali yana da ikon zartar da shi, Allah zai kira shi a ranar Alkiyamah a gaban dukkan halittu, sannan ya ce masa ‘Shiga Aljannah ta duk kofar da kake so,’”).
Manzo (saw) ya kara da cewa, “Ku rika yin hakuri da mata.” Ya san cewa su mata wasu irin halittu ne. Ba za ka rayu cikakkiyar rayuwa ba dole sai da su. Idan kuma kana tare da su sai sun rika muzguna maka. Mafi yawansu akwai su da rashin godiyar Allah, rainin wayo, rainin hankali, ga taurin kai, ga tsananin kishi, ga Hayaniya, da sauransu.
*Mun dauko muku wannan Daga Zauren Fikhu
•’Yan Damfara Ta Hanyar GSM
Zan yi amfani da wannan damar wajen kira ga dukkanin membobi, musamman wadanda ke aiko mana da sakonni a wannan farfajiya ta ‘Burin Zuciya,’ da su kasance masu la’akari da ‘yan damfarar zamani, wadanda ba su da wani aiki illa su kwafi lambar da suka ga dama a cikin jarida, su rika bin masu su, suna yi masu barazana ko zamba cikin aminci da sunan wani jigo a majalisar nan.
Wannan irin ta’adin yana yaduwa ne ta hanyar yawaitar hanyoyin sadarwa a yau kuma ba daidai ba ne. Don haka nake ba wa membobin wannan majalisar, har ma da masu karatu shawarar da su kasance masu sa idanu da lura. Duk mutumin da aka fahimci yana kokarin aikata wani abu, to a gaggauta sanar da hukuma mafi kusa.
Shakka babu batagarin sun yawaita, don haka ya zama tilas mu rika fadakar da jama’a a kullum don gudun fadawa cikin tarkonsu. Duk da Allah Ya saukaka hanyoyin sadarwa a yau, bai kuma dace ba, wasu su rika cin zarafin al’umma ta wadannan hanyoyin ba.
Mun sami rahotanni bila-adadin yadda ake ci wa mata masu aiko mana da sakonni zarafi, a wasu lokutan ma har tsorata su ake yi da barazana daban-daban.
Don haka nake kara ba masu karatunmu hakuri da su kasance masu sa ido da lura da irin mutanen za su rika hulda da su ta hanyar GSM ko wasu kafafen sadarwar zamani.
Su kuwa masu irin wadannan halayen, muna kira gare su da su shiga taitayinsu, domin duk wanda dubunsa ya cika, tabbas zai yi nadamar aikata hakan, domin hukumomi sun tsaurara matakai daban-daban da salo iri-iri wajen yaki da ‘yan damfara. A huta lafiya.
Daga Abban Umma (B/014/Z/KAD).
Sakonnin Masau Karatu Da Membobi
•Kwamared Kabir Allah Ya Mayar Da Alheri
Assalamum alaikum da fatan alheri. Zuwa ga wannan majalisa mai tarin albarka, tare da membobinta da shugabanninta baki daya, ina kira ga Abban Umma da ya ba ni dama in isar da sakona ga wannan majalisa domin jajantawa da kuma yi mana ta’aziyya.
Wasu batagari ko kuma barayi sun fasa shagon Kwamared Nasir Kabir suka gwashi kayayyakin da ake sayarwa wadanda suka hada da talbijin irin na zamani, da wasu abubuwa da daman gaske.
Muna fatan Allah ya mayar masa da alheri. Ga lambarsa: 07037083228. Sai kuma ni, Umar Adamu M/Shugaban Jihar Nasarawa Allah ya yi wa kanwata rasuwa a gidan aurenta a Zariya Allah ya ji kanta amin.
Daga Umar Adamu Karu M/Shugaba (B/911/Z/NASS). 08065302576.
•Duk Jihohi Akwai Wannan Kungiya?
Salam Abban Umma da ‘yan majalisar Burin Zuciya, fatar kowa lafiya, ina da tambaya duk jihohi 36 Nijeriya akwai wannan kungiyar? Don ina son a yi min rijsta.
Daga Ibrahim Garba Shuni, Sokoto. 08066163063.
-Malam Shuni, ka ba ni dariya da wannan tambayar! Amma amsar ita ce duk jihohi muna da membobi har da Abuja, da ma wasu kasashen daban, wadanda suka hada da Nijar, Kamaru, Ghana, Libya, Saudi-Arebiya, China da Mali, duk suna bibiyar harkokin wannan majalisa ta Burin Zuciya.
Abin ya ba ni dariya shi ne, yawan jama’a suke birge ka, ko kuwa muradun kungiya? A zatona za ka tambayi manufofinmu tukunna kafin ka nuna ra’ayin shiga. Amma ba matsala idan yawan jama’a ke birge ka, to muna da jama’a sosai wadanda ba za mu iya lissafawa ba. Sai na ji ka.
-Abban Umma (B/014/Z/KAD).
•Me Ya Sa Ka Ke Shiga Hancin Kanawa Da Kudundune?
Salaam, gare ka Abban Umma, ko za ka fada min kai dan wanne gari ne? Don na lura a kullum shiga hancin Kanawa da kudundune kake yi!
Daga Fatima Bichi.
-Hajiya Fati, duk da dai diya ki ke a wajena, amma bari na dan ba ki amsa: Ni dan garinmu ne! Garin da kowa ke shaukin zuwa... Garin da kafin ka shige shi marmarinsa yake kara kusantoka! Garin da ko bisa jirgin sama ka ratsa kansa, sai ni’ima ta mamaye ilahirin zuciya da ruhinka... Hakika garinmu nagge dadi goma ne!!
Da fatan diyata Fatima ta gamsu.
-Abban Umma (B/014/Z/KAD).
•Abba, Ka Hada Ni Da Yarinyar Nan...
Ina fatan kana lafiya Abban Umma, na ga hoton wata yarinya da ka sanya ta a shafi na 27, don Allah ina son lambarta, ko ma daidaita kanmu...
Daga Usman Kaduna. 07068975045.
-Malam Usman, hoton da muka sanya a wanan shafin na wata yarinya ce mai suna AISHA ALIYU (TSAMIYA), wadda jaruma ce mai tasowa a harkar finafinan Hausa. Ba na jin zan iya aiko maka lambarta kai tsaye, har saina tuntube ta. Idan ta amince da tayinka, sai a aiko maka da lambar. Na gode.
Na ka, Abban Umma (B/014/Z/KAD). 08033225331.
•Mata Goman Nan Duk Suna Da Illa
Salaam, lallai haka na a cikin matan nan goma ba wadda ba ta da illa sai dai shawara dai da zan basuwa ga masu irin wanga hali, in sun ji su gyara. Allah ya mana jagora.
Daga Basiru Gidandala Sokoto. 07038823412.
•Abu Uku Masu Daraja Da Akasinsu
Salam, Manzon Allah (SAW) ya ce: Abu uku yana halakarwa, abu uku yana tseratarwa, abu uku yana kankare zunubai, abu uku yana kara daraja. Bari mu kalli kowanne a mizani.
-Abu uku mai halakarwa: a) Rowa da ake biye mata. b) Bin son zuciya. c) Jiji da kai.
- Abu uku mai tseratarwa: a) Yin adalci a cikin fushi da yarda. b) Tsakaitawa cikin talauci da wadata. c) Tsoron Allah a fili da boye.
- Abu uku masu kankare zunubai: a) Sauraron sallah bayan an yi sallah. b) Cika alwala, a lokacin sanyi. c) Da halattar Sallah a jam’i.
- Abu uku masu kara Daraja: a) Ciyar da abinci. b) Yada Sallama. c) Sallah da daddare, mutane suna bacci. An samo wannan ne daga littafin ‘Sahihul Jami’i.’ Allah ya sa mu dace, ameen.
Daga Adam A.Adam Gashua.08189941495
•Gaisuwa Ga Aminaina...
Salam Abban Umma ya aiki ya aka ji da jama’a ina so ka mika min gaisuwata ga aminiyata Rukaiya Ja’far Kano, ina taya ta murnar aure da ta yi, Allah ya ba su zaman lafiya da Rukayya Rabiu da Hafsat Baba aminiyar asali, Badiya Katsina amarya a gidan Alhaji Jabir.
Bayan haka zan mika gaisuwata zuwa ga Angona lbrahim Iliyasu (Yariman Matasan Bichi) da fatan za kadawo lafiya, ameen.
Daga ‘Yar’uwarku, mai kaunarku Sailuba S. Yusha’u. 08136571215
•Godiya Gare Ku Baki Daya
Salam Abban Umma barka da yamma yaya aiki da fatan ka wuni lafiya, godiya ga ‘yan’uwa da abokan arziki game dimbin sakonninku game da abin da ya faru da ni. Na ji dadi kuma nagode. Allah ya bar zumunci. Sanarwa ga ‘yan’ uwa da abokan arziki na wannan majalasi mai albarka, ina neman Allah ya hada ni da matar aure tagari.
Bissalam, na ku Usman M. Sani, Ikara, Jihar Kaduna. 07036785053.
•Jaridarku Ba Ta Wuce Ni A Nan Kwara!
Ina yawan bibiyar wannan shafi na Burin Zuciya domin jaridar ba ta wuce, duk sati sai an kawo min har gida. Bisa hakan nake son a yi mani rajista don zama memba.Na gode.
Daga Maman Nana (amma a sakaya lambata don Allah), Kwara.
•Jinjinar Fatan Alheri Ga Sarkin Nasarawa
Salam Abban Ummah da fatan kana nan lafiya tare da daukakin membobi baki daya. Ina son ka ba ni dama domin na isar da sakon taya murna da jinjina ta ga mai martaba Sarkin Lafiya, Alhaji Dakta Isa Mustapha Agwai (1) Shugaban majalisar sarakunan Jihar Nasarawa, bisa cikarsa Shekaru Arba’in da daya 41 a kan karagar mulkin masarautar Lafiyan Bare-Bari. Muna yi masa fatan alheri da samun nasara hade da yawancin kwana a bisa wannan karaga ta masarautar Lafiyan Bare-bari. Da fatan Ubangiji ya kara masa yawancin kwana da rayuwa masu albarka, hade da jinkan talakawarsa da ma kasa baki daya.
Gaba dai, gaba dai, Majalisar Burin Zuciya! Gaba dai, gaba dai Masarautar Nasarawa da Tarayyar Najeriya!!
Daga Hassan (Angon Beauty lafiya), a madadin Shugabannin majalisar, reshen Nasarawa. 08037548241
•Yaushe Za A Farfado Da Tashe A Kasar Hausa?
Tashe al’adace wacce yara ‘yan shekara goma zuwa sha-biyar ke yi cikin watan azumi a kasar Hausa kuma ana fara shi ne daga goma na Ramadan har zuwa karshen wata. Ana yin tashen ne dan nuna godiyar Allah an shekara lafiya, a wasu wurare yara ke tashe amma a kasar Bakori da Danja, ba yara kadai ke tashe ba, har da manya ‘yan sama da shekaru 40. Masu tashe na nuna wasu dabi’un na rayuwar Hausawa kamar tashen Mairama da Daudu inda ake nuna zamantakewar aure a kasar Hausa.
A da sadakar Hatsi ake ba ‘yan tashe amma yanzu kudi ake badawa. Babu wanda zai iya fadin nau’ukan tashe a kasar Hausa sai dai akwai ‘Mairama da Daudu,’ ‘ Danda- Dokin kara,’ ‘Malamar makarantar Boko,’ ‘Malama ga kudin toshina’ da sauransu. Akwai bambamci tsakanin tashen maza da tashen mata. Idan aka yi lura za a ga al’adar tashe ta samu tawaya ko koma baya saboda tasirin da addinin Musulunci ya yi kanta dan wani tashen sai an yi cin fuska kamar tashen ‘Malamar makarantar boko,’ inda ake nuna wata ta yi cikin shege, wani tashen sai an nuna tsiraici kuma duk Musulunci ya yi hani da yin haka, karatun boko ya yi tasiri kan tashe a kasar Hausa ta yadda ‘yan boko suka watsar da al’adarsu baki daya suka dauki al’adar turawa, suka bar gari cikin jama’a suka koma GRA, suka hana ‘ya’yansu hulda da yaran da za su koya masu tashe, dan kada wani ya ye gidajensu, ya yi hulda ko abota da ‘ya’yansu, sai suka kawo macizai da karnuka na yi masu gadin gidaje.
Yakamata hukuma ta yi gyara dan farfado da al’adar tashe a kasar Hausa, ta sanya tashe cikin manhajar karatu kuma ta yi doka kan dole sai yaran Hausa sun koyi yadda ake yin tashe a makarantu dan kada kyakkyawar al’adarmu ta tashe mai dadadden tarihi ta bace.
Nagode, Naku Amiru Bakori. 07068147933.
•Auren Nagari Dacen Rayuwa
Assalamu alaikum, Abban Umma barka da warhaka. Gaisuwa ga ‘yan majalisu ‘Burin Zuciya’ mai tarin albarka Allah ya dada assasa wannan majalisar ameen. Duk wanda ya yi dace da mace tagari, hakika ya auna arziki Dan mace tagari ita ce gida, amma fa ba a gane mazan balle matan. Abin da ya faru da kawata mai suna Nasara (Maman Amira), ta shaida min ta yi dacen rayuwa aurenta na farko me kudi ta aura, ya kaita Makka har sau uku, sai dai ba ta da kwanciyar hankali a cikin gidanta ga shi baya ibada, ganin halin da take ciki ta mikawa Allah kukanta dan neman mafita, shi kuwa Mabuwayi ya tallafa mata Alhaji ya shiga rudani ya sauwake mata.
A nan, Allah ya kara hada ta wani bawan Allah fakiri ne amma mai ibada, ya san mutunci da kimar aure. Ya farfado da tattalin arzikin zuciyarta, ta sami natsuwa da farin ciki, shi ya sa ta ce min yanzu ta dace da rayuwa. Na shigo da tattaunawamu ga iyaye mata a dau darasi a kan nasarar zaman lafiya, ya fi zama dan sarki.
Daga ‘Yar Amanar ‘Burin Zuciya’ Huraira Jos. 08036325614.
•Jinjina Ga Masarautar Burin Zuciya
Salaam, jinjina ga MMasarautar Burin Zuciya, gami da nishadantarwa da suke ba jama’a. Bayan gasuwa ga mai martaba Sarki, Shugaban masarauta, Sarauneya mai Dakin Gabas, Gimbiya, da dai sauransu, gaisuwa ni keyi wannan fili na sada zumunci, mahawarar da aka yi na budurwa ko bazawara. Ni dai ya danganta da yanayin tarbiyya wajen iyaye. Wata budurwan ba ta jin kunya kowa ba ta jin tsuraran kowa wata matan gawaye za su hure mata kunne har ta zama bazawara, ko kuma halin yau da kullum, amma bazawara ta fi iya jan hankalin namiji sobo da gogaggiya ce da sanin rayuwa.
Daga Nuhu Muhammad Danja. 08050506669.
•Gaisuwa Gare Ku
Salam, ina gaisuwar ban girma ga shugabannin majalisar ‘Burin Zuciya’ da suka hada Mai martaba Sarki, Shugaban Masarauta, Sarauniya Mai Dakin Gabas, Gimbiyar Sarki, Bulaliyar Masarauta, Yarima, da dukkanin Membobin majalissa da fatan Allah ya kara zumunci.
Daga Is’haka Sarkin Fulani Dankama (B/1540/Z/KTN). 08100006858.
•Mahawara
Salam, Abban Umma da fatar kana lafia, yau kuma na bijiro fada ne don ni ma in gabatar da tawa makala ita ce tsakanin maza da mata wa ya fi iya kwarewa wajen satar kayan gwannati? Saboda sun ce duk abin da namiji yake yi, mace ma za ta yi daidai da na namiji. Ina fatar fadar masarauta za ta yi mahawara a kan wannan.
Daga Namadina B. Ymar (Sakataren ‘Burin Zuciya’ na Jihar Kebbi). (B/996/Z/KEB). 08135444494.
•Na Gaida Hajarun Sokoto Da Munaya Hotoro
Abban Umma, don Allah ina son ka gaya masu Munaya da kawayenta cewar Bazawara fa saboda daukar hankalinta wasunsu fa har aure suke yi ba a gane jawarawa ba ne, a matsayin budurwa ake daukarta wasu ma fa ba a ganewa. Haka za a yi ta tafiya, saboda daukar hankali na su a tambaya rman su Munaya da akwai wani daukar hankali da budurwa ke yi mai kama da wannan? Ina gaishe da Hajaru Sokoto da Aliyu Nadamar hannun Sarki da Abubakar Sarky da masarautar baki daya Abban Umma sannu da kokari.
Daga Habib Shattima. 08034273322
•Fatan Alheri
Salaam, ina mai mika gaisuwata ga membobin ‘Burin Zuciya’ na kowace jiha dake fadin Nijeriya da gani masoyin wannan kungiya ta ‘Burin Zuciya’ Abdulmalik Ibrahim Washo (Zamfara Gusau City). 07032176439.
•Ya Kamata A Gane Wannan...
Allah ya ja zamanin Mai Martaba Sarki, ina gaishe da ‘yan fadar Sarki baki daya. Jinjina ga Abban Umma jigo jagoran wannan tafiya. A gaskiya bajawara ta fi saurin saye zukatan maza, musaman idan kyakyawa ce, kai ko dama mumuna ce. Ni ina soyayya da kyakkyawar budurwa, amma bajawara ta dauke man hankali a hangena wata bajawarar ko da ta shekara 15 da aure, ba za a hada ta da budurwa ‘yar shekara 18 ba. Yadda budurwa take ji da budurcinta ta ga wata bajawarar to fa ta san an tsere mata da komai ma. Duk kyanta kuwa.
Ni budurwar ma da kanta da ta gane ina magana da wannan jawarar ta san ta gama yawo.
Daga Habib Shattima Katsina. 08034273322.
Burin Zuciya
Burin Zuciya
Dan Jarida A Bakin Aiki
Ba Na Yin Hira Da Kowane Harshe, In Ba Hausa Ba (3) — Getso
Mai karatu, yau muna mako na hudu ke nan da fara kawo maku wannan tattaunawa da muka yi da shahararren dan jaridar nan da ke Kano, Alhaji Halilu Ahmad Getso, wanda muka ce maku ya shugabanci gidan rediyon tarayya na Kaduna, daga bisani kuma kuma ya shugabanci na Legos, amma halin yanzu ya jingine komai na koma gona. Wakilinmu a Kano, Mustapha Ibrahim Tela ne ya yi hirar. Kuma in dai ana biye da mu, mun tsaya ne a inda masanin ke yi mana bayanin fitattun mutanen da ya yi hira da su.
A biyomu mu dora daga inda muka tsaya makon da ya gabata.
“Sai kuma Muhammadu Buhari, shi ma mun yi hira da shi a shugabancin kasar nan da ya yi na mulkin soja. Akwai ma wata hira da muka yi da shi, aka zarge ni da cewa na sa shi ya yi wata katobara, wacce maganar ta damu mutanen Arewa, musamman Hausa-Fulani a wancan lokacin. Sai kuma Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Sai kuma Shonekan. Shi Shonekan aiki ne na shekara daya ya hada mu da shi, wanda Marigayi Sani Abacha ya sa shi a matsayin Shugaban wani kwamati, wato kwamitin nan na bision 2010, bayan da Abacha ya karbi Mulki a hannun Shonekan.
Aka zabo mutum 150 ko 200 ne, a duk fadin Nijeriya, ni ma na samu kaina a cikin wannan kwamiti na Shonekan, kuma wannan kwamati ya kunshi manyan ’yan Nijeriya, kamar su Dantata. Kuma na san ba wai don na isa ba ne aka sa ni a wannan kwamiti, don dai kawai ana tunanin zan dinga ba da wata gudumawa ce. Kuma ko meye matsayinka, in ka ga taron nan, to sai jikinka ya yi sanyi. Domin idan ilimi kake takama da shi, to akwai Malamanka, ko masu gidanka. Haka kuma Shugaba Obasanjo ma a hawansa na biyu, na yi mamaki yadda shi yana matsayin Shugaban kasa, ni kuma ina Halilu dina, ya kira ni ya sa ni aiki.
Sai kuma Marigayi Yar’Adua, ban taba ganinsa ba, sai da Sarkin Daura ya daukeni ya kai ni wurinsa muka gaisa. Ya ce wannan wanene, ban san shi ba? Na ce wa Sarkin Daura, to kai ka kawoni, da ma bai san ni ba, ni ma ban taba ganinsa ba sai a hoto. Saboda haka sai Sarkin Daura ya ce masa ai wannan shi ne Halilu Ahmad Getso. Ya ce ba mu taba haduwa ba. Na ce ranka ya dade yau ga shi mun hadu.
Haka kuma manyan Sarakuna sun san ni. Kamar Sarakunan Kano, Zazzau, Daura, Katsina, Sultan na Sakkwato, Shehun Borno da dai sauransu, wasu ma na yi hira da su, kamar Sarkin Musulmi, Alhaji Ibrahim Dasuki, Sarkin Zazzau na yanzu, da kuma Lamidon Adamawa, duk wadannan mun yi hira da su. Saboda haka, a takaice dai, wannan aiki ya kai ni inda ba a zato.”
Tsawon shekaru sama da 30 da Halilu Getso ya yi yana aikin jarida, har Engila ya je, amma ba son hira da wanda ba ya jin Hausa, ko yin wani shiri da Turanci. Ko me ya sahaka?
Dalili na farko shi ne, ni ba na son in nakasa harshena na Hausa. Sannan kuma dalili na biyu, ban iya Turanci ba (ya yi dariya), ban ce na iya ba, wadanda kuma suka iya Turancin, Allah ya amfana abin da suka iya. Kuma na san komai kwarewarka da iya Turancinka, idan Mutum ya fadi abu da Turanci, zan ji abin da ya ce, ko da kuwa wane irin Bature ne.
To ni dai Hausa na iya, saboda haka ban ga dalilin da zai sa in nakasa harshena, in raya na wani ba, duk abin da zan fada, to Hausa ta isheni. Domin Hausa ta yi mani riga da wando, malum-malum, shakwara da jamfa, har,da hula girkan Nupe, hula ’yar Tofa. Ta yi mani habar kada, ta yi mani Zanna Bukar. Kuma da Hausa nake ci, nake sha, banga dalilin da zan saketa in kama wani harshe ba. Ba na so in zama hankaka, mai tafiya ba tsale ba, ba gudu ba.
Ko za ka iya tuna wasu alhairai da ya samu sanadiyyar aikin jarida?
Abin da nake so ka sani shi ne, duk abin da na samu, na samu ne a dalilin wannan aiki. Na je Hajji akalla sau 10, na je kasashen Amerika, China, India, Ghana, Afirka ta kudu, Engila, Chadi, Niger, Kwatano da sauransu masu yawa, na kusa da na nesa, kuma duk a dalilin wannan aiki. A dalilin wannnan aiki na samu alkairai masu yawa. Na goda wa Allah.
Kuma sha’awata da aikin gona shi ne, tun ina yaro nake da sha’awar aikin gona. Domin in ba ka manta ba, ai daga Kwalejin aikin gona na wuce na kama aikin rediyo. Kuma abubuwan nan guda biyu sun aureni na auresu, wato aikin rediyo da aikin gona. Domin ko wannan gonar da muke hira da kai, na san ba ka hango iyakarta, to na siyeta ne Naira 800 a shekarar 1980. Banda ita kuma inda gonaki daga guda 20 zuwa 30, a cikinsu akwai wacca na saya Naira Miliyan daya, akwai ta Miliyan biyu, akwai ta Miliyan uku, har ma da ta sama da haka. Amma wannan da muke hira da kai, ita na fi so, ita kuma na fi zama a ciki.
Me ya sa Alhaji Halilu Ahmad Getso bai shiga siyasa ba, tun da ya jingine aikin jarida?
Ka yi mani tambaya a kan Siyasa, me ya sa ban shiga ba, ko zan shiga nan gaba? To ita siyasa dai ba ta ba ni sha’awa, amma Allah ya kaddara ina da rabo mai yawa a cikinta, saboda ’yan siyasa sukan ba ni aiki in yi, kuma in samu alkairi. Amma dai ba ni da sha’awarta sam-sam. Saboda a iya sanina, babu wata harka ko wata sana’a da take rufa wa mai yinta asiri, da yi masa shatara na arziki kamar siyasa, amma kuma babu wani wanda yake bakanta sana’arsa ko aikinsa da kansa kamar dan siyasa.
Misali, kalleni da kyau, dubi rigar da ke jikina, ta kai shekara uku ina sawa. To amma da a siyasa nake, in ta yi datti in wanketa in fito fes-fes, sai ka ji ana cewa ‘dubi matsiyacin can, har ya sake riga. Dama dan gidan wane matsiyaci ne, dama haka.’ Kuma a dalilin siyasa ne za a ambaci sunan mahaifinka a zage shi, a aibata shi, ko a kaga masa wani sharrin da bai san hawa ba balle sauka. A dora masa wani laifin da bai taba yi ba.
Bari in ba ka wani labara, ni ma da ba dan siyasa ba, wanda na ce maka ina da rabo a siyasa. Wata rana a ciki shirina na Dadalin Siyasa, wata mace da ake kira Gambo Sawaba da ke Zariya a wancan lokacin. Kuma dama na gaya maka a baya cewa akwai namiji Gambo Sawaba, akwai kuma mace. To ita macen, ta je wannan shirin nawa na Dalilin Siyasa ta zageni, ta ce Halilu Ahmad Getso dan iska, dan karuwa! A FRCN. Mahaifiyata ta ji wannan abu da kunnenta, a lokacin ma ta dora sanwa a tukunya za ta yi girkin abincin dare, aiki kuwa abincin da ba ta yi ba ke nan. Sai ta fadi ta fashe da kuka!
To ni kuma na san ba dan karuwa ba ne! Na san mahaifiyata tana da Mahaifiya akalla sama da hawa bakwai, wadanda duk a gida daya aka haifesu, wato kakar kakata ke nan. Haka kuma mahaifina da Mahaifinsa kakan kakana, duk a gida daya nake. Duk da wannan jerin na iyaye da kakanni, amma aka ce mani dan karuwa. Duk Mahaifana na da kanne da yayye da ’yan uwa. Haka ita ma Mahaifiyata. Kuma duk a gida daya aka haifesu, amma aka gaya mani haka, to ina kuma a ce ina ina siyasa? Sai dai kuma duk da an fada mani waccan magana, to yanzu ina tabo a jikina?
Saboda haka daga ba ya sai na samu mahaifiyata na ce mata kawai ta daina sauraron wannan shirin da nake gabatarwa, ta rika kashe rediyon. Kuma kar ka manta, ni ke gabatar da shirin fa, ni ne kuma na sa waccan magana da aka zageni a wannan shiri nawa na Dadalin Siyasa. To gaskiya saboda irirn wannan kazanta ta siyasa ya sa ba na sha’awarta.
Kuma ina gaya maka, da kanina da sauran ’yan uwana, da duk wanda zan gaya wa magana ya ji, zan ce masa kada ya shiga siyasa. Kai hatta kai da yau na fara ganinka, in zan gaya maka ka yarda, zan ce kada ka shiga siyasa, ka kyalesu dai kawai su yi ta gwabzar junanasu a siyasarsu da ake so ta gyaru.
Mun san Alhaji Halilu Ahmad Getso yana da burin kafa gidan rediyo ko Jarida. Ina aka kwana?
Allah ya sani ina da sha’awar kafa gidan rediyo, amma ba ni da kudi. Kuma yanzu haka ina studio a Kano, kuma cikin wannan studion nawa, har da ofis da komai da komai, amma na kan yi wata shida ko shekara ma ban shiga ba. Amma duk lokacin da na yi sha’awa, na kan je in shiga, in zauna in yi duk abin da zan yi, wasu su zo mu gaisa, in ci abinci, in wuni in dawo gida. Shi ya sa ma nake yi ma wannan Studio nawa lakabi da cewa ‘Hana Gori.’ Kamar yadda masu tallar dutsen nika a shekarun baya, kimanin sama da shekaru 40 kan yi kirari, na cewa ‘a sai dutsen nika mata, saboda duk matar da ba ta da dutsen nika sai ta ara.’ Kuma in ta saya, sai ka ji ana cewa ta sayi hana gori ke nan. To shi ne matsayin wannan ofis nawa.”
•Mai karatu muna da sauran muhimman bayanai da za su amfani jama’a a wannan tattaunawa da muka yi Alhaji Halilu Ahmad Getso. A biyomu mako na gaba don jin karashen wannan tattaunawa.
tare da
Do'stlaringiz bilan baham: |