‘’Balaraba kinga shekara da shekaru bamu samu haihuwa ba, amma tunda yanzu Allah ya nufe mu wannan shekarar har kin samu ciki to sai mu yi wa Allah godiya



Download 75,59 Kb.
bet1/6
Sana02.03.2017
Hajmi75,59 Kb.
#3698
  1   2   3   4   5   6


KARON BATTA

‘’Balaraba kinga shekara da shekaru bamu samu haihuwa ba, amma tunda yanzu Allah ya nufe mu wannan shekarar har kin samu ciki to sai mu yi wa Allah godiya. Saboda haka ina son in sheda miki da cewar zan d’auki azumi na kwana uku don nuna godiyata ga ubanginji mad’aukakin sarki,idan asuba tayi kusa kiyi kokari ki dafa mini shinkafa domin in yi sahur’’. To malam Abubakar,Allah ya nufe mu da muga jinjiri ko kuma jinjira lafiya.

‘’Amin Balaraba’’. balaraba tace. ‘’ kodan malam Abubakar nasan idan so samu ne baka ki yazama jinjiri ba!’’ To Balaraba wane namiji ne baya son ya samu magaji? suna kare zance Abubakar yanufi gidan iyayen sa domin ya sheda masu cewar yanzu fa matar sa ta samu ciki.

Salamu alaikum! ‘’Amin wa alaikumus salam’’ baban Abubakar ya amsa sallama. Baba ina yini ina fatar gidan lafiya kalau? Kalau muke yau kaga damar ziyarto mu don munce kayi wani aure domin wanan yar gaban goshin taka bata samu haihuwa ba, yaro kawai sai ka dauke kafafun ka daga zuwa ganin mu.Abubakar ya durkusa yana sauraron baban sa dake zaune a karaga yana cin goro.

Abubakar yace, a a baba ba haka bane kasan yadda yanayin aiki na yake, yau ina gida gobe ina wani gari domin aikin kwangila ba wuri daya akan tsaya ba. Wallahi baba wata na uku ina tsakanin Lagos da Kano,domin wasu kayan gini da na ke son in samu don gwamna ya matsa da in kareta nan da wata daya. ‘’To yanzu kasamo ko?’’ Haka kuwa baba domin ma har na kare,har ma ya yaba da aikin kwarai da gaske.

Baba ina inna Sa’a take, naji gidan shiru? ‘’Taje ta karbi kudin adashen ta da zata kwasa,kasan innar taka bata gajiya da shiga adashen rikici.ke ish ish.... kai! Wadannan awaki sun cika damuwar da mutane, ai duk aikin Sa’adatu ce sai da nagaya mata ta barsu cikin gidansu amma ta bude su yanzu gashi sun zubar da garin tuwo, tazo ta kwashe shi. Yawwa! Abubakar naga kudin da ka aiko mana, kai baka gajiya da dawainiya gashi kana ta fama da wanan aikin kwangilar?

‘’Salamu alaikum! A a yau Abubakar a gidan mu? Jiya muke maganar ka da babanka cewar ka gujemu ka dai ka zo ka ga lafiyar mu, yau wata biyu kenan’’. Balaraba maganar da kika iske inayi da shi kenan yace aikin yawon kwangilar sa ya hana shi duk kwanakinnan yana Ikko gari. Allahu akbar, Abubakar yanzu har ka bunkasa zuwa kasuwanci a Lagas. Kai dannan rufa mana asiri ka daina zuwa lagas garin da nake ji ana yawan yakan kanun mutane da yawan tashin hakali kulum inaji ga rediyon malam ana cigiyar mutane sun bata kamar awaki.

Yawwa kin tuna mini ga garin tuwon ki can awakin sun barar kya kwashe kayanki. ‘’ a a baba bari na kwashe mata garin, ai wakin ne sun cika buruntu. Abubakar yana murmushe sai yace to baba tun da gashi inna ta dawo dama abin da yakawo ni shine in sheda muku cewar yanzu Balaraba ta samu ciki yanzu watan sa biyar.

Nan take balaraba tayi takabira tace Allahu akabar, Allah kaine mai girma abin bautawa da gaskiya kuma kowa ya roke ka baya rashi,yanzu dannan Balaraba ciki gareta, ni Sa’a ina nan ina zagin diya cewar bata haihuwa yau shekara bakwai da auren ka gashi duk tsaranka sun kai ga yaya biyar. To Allah ya sauke ta lafiya, ya nuna mana jika ko jikanyarmu. kai nayi murna kwarai dagaske, sa annan ka tabatar da wata biyu ma su zuwa kamayar da ita gidan iyayen ta domin ta samu kulawa kuma ta haihu a can. Ina fatar kana jina? Ta na kuwa zuwa antanata asibita kuwa? E inna ina jinki ai tana zuwa awon ciki antanata.

Abubakar ya bude jakar da yazo da ita yace, baba ga shaddar da nakawo maka daga kano, ke kuma inna ga atamfar ki yar dakar. ‘’To madalla dannan Allah ya yi maka albarka kuma ya baka dan da zaya kula da kai kamar yadda ka kula damu’’.Amin baba, zanje gida sai na sake juyowa.

To Abubakar, amma roko na dakai shine idan zaka sake yin irin wanan dogowar tafiya karika sheda mana. Ka kuma mika gaisuwar mu ga Balaraba, sai na samu lokaci na ziyarce ku domin in ga lafiyar ta. Ka tabbatar da kana saya mata maganin jini kaji ko.

Abubakar ya tuka motar sa zuwa gida sai yaji sitayarin motar sa tana ja gefe daya ashe tayar motar ce tayi faci ne. Abubakar yace ‘’kai nagode Allah, yau da a ce ina gudu ne fiye da kima da karyata ta kare. Kai gashi bani da sifiya taya yaya zanyi kenan’’ sai yafito yana hangawa yaga ko zai ga masu faci kusa da wurin amma bai hango ko daya ba.

‘’Yau kuwa akwai tsiya, kaga illar bin hanyar bayan gari kenan kai bypass ba kyau. Yanzu kafin kasamu tasi ko wanda da zai rage maka hanya zuwa wurin masu faci cikin gari shine hidima’’. To Allah mai iko, ga Alhaji Sani nan zuwa kila kuwa da iyalansa yake. Abubakar yana kan juyayi sai yaji sani yace ‘’Abubakar,lafiya dai ko, ko yau ana jin nishadi ne ake hutawa a by pass don nasan halin ka da yawon rashin dalili’’

Haba Alhaji sani! Baka ga tayar motar ce ke da faci,kuma tsiyar bani da sifiya ban san inda na yar da ita ba. Sai Alh sani yace abu mai sauki bari in ara maka tawa amma ka maida mini ita kada in shiga halin da kake yanzu. Abubakar yace to madallah nagode Alhaji sani manyan gari Allah ya saka maka da alhairi.

Malam, lafiya kayo latin dawo wa gida bayan kace kafin karfe bakwai zaka dawo?gashi abincin naka ma har yayi sanyi. Abubakar yace kai Balaraba babu laifi wallahi maotar nan ne tayi mini faci a kan hanyar bypass. Su inna sun ce a gaida mai ciki. To ka fara ke nan ko ba a son mai ciki ne mujiya tun yanzu,wato har ka sheda masu cewar an samu juna biyu. To ke ai ya zame mani dole insheda musu domin sune farkon samun irin wannan labari, kar kuwa kiga yadda suka ji dadi domin tace insheda miki tanan tana shirin zuwa ganin yadda kike kokari.

Suna cikin ba’a da annashuwa sai kawo masa abinci gaban sa ta bude mishi. ‘’a a Balaraba kina nufin mai ciki na da kokarin dafa abinci irin haka ga balain dadi kamar haka kiji yadda kamshi ya game ko ina cikin falon nan. Balaraba tace mishi kadai kasani maigida. Wash! Malam wallahi cikin nan yana matsa mini da murda gafe dama kila kuwa namiji ne domin kawata Mairo ta ce idan kana jin yawan motsi da gafen dama insha Allah zai kasance na miji

To Allah yasa amin, amma mata kuna da yawan canfe-canfe,a’’a yaya kina murde murde haka ko in kai ki asibiti,indai ba haihuwar ce ba. Haba malam tun yanzu,bari dai har gobe dama ranar awo na ce, yanzu bari inje daki in kwanta nasan zan samu sauki.

Balaraba taje ta kwanta shikuwa gogan ya shiga zurfin tunanen zucci, cewar idan Allah ya nufe shi da haihuwar da namiji yadda zai rika fita yawo da shi. Bayan ya shekara shida ya sa shi a makarantar furamare,kwaleji da jimi’a. Yana wanan tunanen har sai da yakai yana furta abin dake zuciyar sa kamar haka. ‘’kai! Kodan nafi son ya shiga jamia’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, domin ya koyi aikin likita idan ya kammala sai in buda masa Asibiti lokacin yasamu horo na shekara uku da baban Asibitin gwamnati’’.

Kai malam lafiya kana ta magar Asibiti kai daya kamar wanda ya tabu. Sau hudu kenan ina tambayar ka sai da na kai ga dafa kafadar ka,ka firgita kamar wanda kura ta rutsa da shi. Ke ai ni tunanen idan da namiji ne ki ka haifa... Sai Balaraba ta katse masa hanzari. To idan ‘ya mace cefa? Sai yace mata duk daya ance makafi sun yi dare.

Abubakar ya tashi daga tebur din da yake cin abinci, kafin ya shiga dogon tunane ya koma akan doguwar kujerar kushin a inda matar sa ke zaune, ya dora kafar sa ta dama bisa ta hagu yana karkada ta don nishadi sai ya ce ‘’ke ina kwan kazar da ki kace kin soya mini’’? Ta ce ‘’kai malam wallahi bata kwai ake ba ina tambayar ka yaushe za ka mayar dani gida domin haihuwa ne?’’ sai ya kada baki yace mata kiyi hankuri zan mai daki wata mai zuwa domin kisan nima zan je Ibadan wata kila ma har Legas. Ta ce to ‘’Allah ya kai mu amin’’!

Abubakar ya mayar da Balaraba gidan mahaifatan don ta haihu acan, daga nan ya kama hanyar zuwa Ibadan domin shaánin kwangilar sa daga nan ya nufi hotel din da ya saba sauka wanda ke da suna CHRISBO INTERNATIONAL HOTEL. Abubakar ya biya kudin kwana bakwai domin ya ji dadin harkokin kwangilar sa.

Bayan an nuna masa daki ya ajiye kayan sa, yayi alwala yana sallar isha sai yaji ana kwankwasa kofar dakin da yake. Bayan ya idar da sallar sai ya nufi kofar ya bude sai ya ga ashe wani inyamuri ne da suke haduwa wurin neman kwangila a legas da nan ibadan.

Abubakar yace ‘’Emeka! Daga ina, lafiya kazo nan ko dai kana bina ne a gindi a gindi?’’ ‘’Emeka yace bahaka ne ba ina neman daki wanda yaya namu ya soka ne wanda nazo nan a mitek ne, amma don Allah kayi hankuri mistek ne’’. Ba komi emeka ai kowa yana kuskure, kai har yanzu dai hausar ka bata nuna ba. Yayi dariya ya rufe kofa ya koma yayi kwaciyar sa.

Can tsakar dare da misalin karfe daya sai Emeka da wadansu inyamurai yan uwansa su biyu suka bude dakin da Abubakar ke ciki da wani mabudi daban. Ashe lokacin da Emeka ya kwankwasa dakin ya biyo sawun sa ne tun daga maaikatar lafiya ya zuwa wannan hotel din domin su yi masa lahani, shi kuwa gogan yana ta sharar barci domin wahalar tukin mota daga Gusau zuwa Ibadan.

‘’ke dan buru uba ki tashi shegiya’’ daya daga cikin su Emeka wanda baya da kyawon gani ga shi baki kakkaura mai katon tambo a kumatunsa ga hanci kamar an tabe daddawa. Ya dubi Abubakar, yasa kafar sa ya zunguri cikin sa. Abubakar ya tashi firgice ya bude idon sa, sai yaga wannan katon rike da aska mai kaifi tana kyalkyali. Can kuma Emeka ya janyo jakar takardun kwangilar da wasu mahimman takardu yana bincike, daya bayan daya. Bakin kofar dakin ga wani shi kuma yana jingine a kofar yana dariya irin ta keta.

‘’chukuma ku mare shi mani a koya mishi hankali mana ko za ya yo bayani game da wadannan takardun’’ Abubakar yace kai Emeka yaya zaka ce a mare ni bayan mun san juna kuma gaka abokin kwangila ta. Don Allah ka daina irin wannan muguyar wasa... kafin Abubakar ya rufe bakinsa an kwashe shi mari sai da yaga taurari ya fadi kan gado. Sai kuwa Emeka ya fashe da dariyar keta har yana faduwa.

Emeka yace da hausar sa da bata nuna ba ‘’kana tunani muna muku wasa ni ? yau zamu kashi kuni domin ka dame mu ka hana musamu kwangila duka inda mu kaje ana fada mana ka samu kwangila domin kai kana yi aiki mai kyau’’. Mu ba zamu yanda ba kagani kontrakt na magani a asibiti, naira miliyon dari biyu ka karbe, yaya zamu barka da rayuwa shegiya kawai.

Haba abokina Emeka! Allah ne yabani wannan, kaga a yau ne na zo daga Gusau, domin maaikatar lafiya suka aika mini da inzo kwangilar ta samu da ..... ‘’ka rufe muna bakinki shegiya’’! inji chukuma wanda ya sake kwashe shi da kazamin mari a baki sai da ya fashe da jini, sa annan ya yanki hannun Abubakar da askar da yake rike da ita.

Abubakar ya ga wadannan mutane da gaske suke sai kuwa ya d’aga hannun sa ya dankara wa chukuma kulli a tababbe hancin nan na sa, sai da askar da yake rike da ita ta fadi. Ya tashi a gigice yace wa chibuzo, ‘’doki wuka de sori kada ya doka’’. Amma ina, Abubakar yakai hannunsa sai chibuzo ya haure shi da kafa a hannun. Abubakar yayi ta maza ya kaiwa chibuzo k’ak’k’arfan k’ulli, amma ya kuskure shi sai da ya fadi.

Can kuma Emeka yayo tsalle kamar chines, ya diro akan cikin Abubakar, ya sa hannuwan sa ya shake wuyan sa. Shikuwa chibuzo ya jawo kujera dake gafen gado da nufin ya dankarawa Abubakar, amma ina Allah da ikon sa sai akan Emeka wan da nan take ya fad’i a some. Abubakar ya yunk’ura ya tashi sai chukuma ya cafke shi ta baya, bai san da cewar Abubakar yana rike da askar nan da fadi ba.

Chibuzo ganin an rike Abubakar ta baya, yayi tsammanin banza ta fadi, sai ya kinkimo wani katon kufin tangaran na kwaliyar fulawa zai dankara masa a kai. Nan take Abubakar yasan idan ya buga masa wannan kofin karyar sa ta kare, nan take ya yunk’ura da k’arfi ya harba kafafuwansa gaba daya a fuskar chibuzo wanda nan take ya kwala ihu ya ce da inyamuranci ‘’ewo cineke!’’ da k’arfi domin zafin harbin. Shikuwa chukuma nan take ya saki Abubakar domin lokacin da ya yunkura ya harba kafafuwansa ashe askar ta yanki chukuma a ciki. Ganin samun wannan galaba akan su, nan take Abubakar yayi waje a guje.

‘’Kai lafiya Alhaji kana gudu haka kamar wanda ake neman ransa’’? sai Abubakar, ya ansa wa musu kula da hotel din cewar wallahi b’arayi ne suke neman su kashe ni a dakin da na sauka, room 10. Masu kula da gadin hotel d’in kuwa basu warganta ba suna shiga d’akin sai su Emeka suka tsallaka ta tagar d’akin a inda mota marsandi ke jira da su tsere. Abubakar kuwa a ka d’auke shi zuwa asibiti daganan aka wuce da shi caji ofis din yansanda a inda ya rubuta sitatiman duk yadda al-amarin ya faru.





Download 75,59 Kb.

Do'stlaringiz bilan baham:
  1   2   3   4   5   6




Ma'lumotlar bazasi mualliflik huquqi bilan himoyalangan ©hozir.org 2024
ma'muriyatiga murojaat qiling

kiriting | ro'yxatdan o'tish
    Bosh sahifa
юртда тантана
Боғда битган
Бугун юртда
Эшитганлар жилманглар
Эшитмадим деманглар
битган бодомлар
Yangiariq tumani
qitish marakazi
Raqamli texnologiyalar
ilishida muhokamadan
tasdiqqa tavsiya
tavsiya etilgan
iqtisodiyot kafedrasi
steiermarkischen landesregierung
asarlaringizni yuboring
o'zingizning asarlaringizni
Iltimos faqat
faqat o'zingizning
steierm rkischen
landesregierung fachabteilung
rkischen landesregierung
hamshira loyihasi
loyihasi mavsum
faolyatining oqibatlari
asosiy adabiyotlar
fakulteti ahborot
ahborot havfsizligi
havfsizligi kafedrasi
fanidan bo’yicha
fakulteti iqtisodiyot
boshqaruv fakulteti
chiqarishda boshqaruv
ishlab chiqarishda
iqtisodiyot fakultet
multiservis tarmoqlari
fanidan asosiy
Uzbek fanidan
mavzulari potok
asosidagi multiservis
'aliyyil a'ziym
billahil 'aliyyil
illaa billahil
quvvata illaa
falah' deganida
Kompyuter savodxonligi
bo’yicha mustaqil
'alal falah'
Hayya 'alal
'alas soloh
Hayya 'alas
mavsum boyicha


yuklab olish