‘’Balaraba kinga shekara da shekaru bamu samu haihuwa ba, amma tunda yanzu Allah ya nufe mu wannan shekarar har kin samu ciki to sai mu yi wa Allah godiya



Download 75,59 Kb.
bet3/6
Sana02.03.2017
Hajmi75,59 Kb.
#3698
1   2   3   4   5   6

MUTUWAR ABUBAKAR


Yanzu zayyad ya kai shekara shida har kuma an sa shi a makarantar boko ajin sa d’aya bayan ta arabiya da yake zuwa da yamma. Haka kuma uwar sa da aka dabe kaunar haihuwa da farko, yanzu ga ta da ciki na biyu. Zayyad ya fara tambayoyin sa irin wadanda yake yi wa baban shi. ‘’Mama yaya cikin ki kato haka ko yana yi miki ciwo ne? Zayyad yana tambayar mamar shi. Zayyad mutum ke ciki waton jariri, zaka samu kani ko kanwa. Mama yanzu suna ciki ? e mana. To mama bari in shiga in gansu mana kila yan kanana ne kamar wadanda na gani fatima ko? Hakane zayyad amma kayi hankuri ka bari har in haife su. Amma mama kesan zasu hana mini shan cakulan da baba ke kawo mini da biskit. A a zayyad ai baban ka zai sayo maka cakulan. Kuma zai tafi da ni yawo kamar yadda muke zuwa? kwarai mana me zai hana.

Zayyad, baban ka yace zai dawo daga asibiti gashi har dare yayi bai dawo ba, ka shirya mu je ingani kila abin ba sauki. Sun fito kofar gida sai ga Abubakar ya dawo rai bace, kumar rigar shi jawur duk kura kamar wanda yayi aikin laka. ‘’Lafiya malam ka dade, tasi zamu tara muje asibitin in gani... ‘’Balaraba, ai baba ya riga ya cika domin ciwon zuciya yake fama da shi ba mu sani ba dama shi ke saurin kashe tsofaffi. Yanzu haka daga makabarta nake

Nan da nan matar shi naji wannan labari sai ta fashe da kuka. Dama surukin na ta yana yi mata alheri da bata shawarwari masu alfanu, kuma yau gashi Allah ya karbi abin shi. Zayyad ganin uwar shi na kuka nan take shima ya fara nashi. Ganin haka Abubakar yace ‘’ ke dubi nan kada ki tara mini mutane bisa titi kamar yan tasha. Dama mutuwa dole ce ga kowane mai rai, domin bashi ce wanda kowa sai ya biya kome dadewa. Kuma she karun baba a duniya casain, ai kuwa sai muyi mishi adduar samun aljanna, to mene ne na kuka. Da kyar mijin ya ciwo kanta ya samu tayi shiru ta daina.

Bayan an kare karbar gaisuwa hankali ya fara dawo wa sai Abubakar ya tuntubi matar sa da shawara a inda ya ke ce wa ‘’Balaraba shawarar ki na zo nema domin abin da kamar wuya ance gurguwa da aure nesa. Kega dai tunda baba ya rasu na tabbata da cewa inna saadatu, gidan nan zai yi mata girma. Saboda haka ina son don Allah kiyi hankuri in kai zayyad wurinta ko ta debe kewa, kuma ta samu abokin hira’’. Ai babu komi ko ni nayi wannan tunanen.

Da gari ya waye nan take aka shirwa zayyad kayan sa, a ka kai shi wurin kakar. Dama yaron ya fi son zama da ita domin wasannin da take yi masa da kuma tatsuniyoyi. Saannan abinci sai wanda yake so, domin kaunar da ke tsakanin kaka da jika. Bayan kwanaki biyu zuwa uku, Abubakar yakan je da matarsa domin ya shere mata kewa.

‘’balaraba ina son inje legas gobe domin in karbo kudin kwangilar da nayi shekarun baya, gashi kuma yanzu kina da juna biyu,ke ga ya kamata ace ina da isassun kudin da zamu yi buki da wasu bukatocin mu’’. To Allah ya kai ka lafiya, amma bukata ta ita ce ka kula domin kaga har yanzu halin nan da ake ciki yansanda basu samu kama wadannan yan banzan barayin nan ba. ‘’kada ki damu ba zan sauka wannan hotel din ba, kuma ke san yanzu fyantin motar na canza shi tun lokacin da dan taksi din nan ya goga mini mota a kasuwa. Sai dai idan lambar motar zasu gane, amma zan je da wata yar wuka domin kariyar kai

Da gari ya waye Abubakar ya je yayi sallami uwar sa, daga nan ya baiwa zayyad kudin makaranta shi kenan ya kama hanyar zuwa legas. Da ya isa ya je maikatar lafiya ya karbo cek din sa na kudin kwangilar da ya yi, sai ya wuce ya sauka a federal palace hotel legas. Amma kash! Aka ce rashin sani ya fi dare duhu, ashe a wannan ranar wani ya ga Abubakar wajen karbar cek din. Nan take su Emeka suka dunfari wannan hotel din kamar yadda suka samu labari. Suka duba duka inda ake ajiye motoci amma basu gane motar sa ba domin fyantin da ya canza, kuma ga su har jikin motar suna wasuwasin yadda zasu samu ganin Abubakar.

Suna tsaye cirko-cirko sai Emeka yace ‘’kunsan abin da zamu yi mu gane inda wannan mutumin yake?’’Aa, inji sauran tawagar barayin. ‘’to zamu je ne mu tambayi masu baiwa baki daki, muce muna neman Abubakar Alhaji daga garin Gusau, dan kwangila wanda ya sauka a nan hotel da rana’’. Gaskiya ne wannan dabarar taka tana da kyau, kai wayon ka yana da yawa inji chibuzo. ‘’A a chukuma tsaya kaji karshen dabarar mana kaji ko ya ka mata a karbe shi, idan mutanen sun gaya mana lambar dakin zamu je mu kwankwasa muce munzo mu bashi sabon tawul na wanka da kuma sababbin zannuwan gado daga house keeping. Yana budewa sai mu fada ciki da karfin tsiya, mu kashe shi mu dauke akwatin takardun.

Chukuma domin jin dadi wannan shawara nan take ya fashe da dariya domin yana jin haushin yadda ranar da suka yi bata kashi da Abubakar ya dambara masa kulli a tababben hancin sa. Emeka ya tambaya ko a kwai wani mai kari ga wannan dabarar. E, kamar kasani kuwan Emeka, idan muka dauki akwatin dole mu binciki dakin mu nemi makullin motar sa.... kai, to ai ba musan lambar motar ba. Kai lalurar ka rudani, kabari in kare ka katse mini hanzari. Ina yabon ka sallah ka kasa alwalla, ai idan muka dauki akwatin dole a ciki muga lasisin motar da kuma fatikulas na motar ka kuwa san dole muga lambar motar a nan. ‘’haka kuwa kaga daga nan sai mu tuka motar mu kai daji mu kona ta.

Nan da nan suka runtuma cikin hotel din kamar mutanen kirki suka gaida wanda ke kan kanta suka tambaye shi cewar suna neman wani abokin kwangilar su mai suna Abubakar Alhaji domin suna da wani muhimmiyar maganar kwangila da shi. ‘’to don Allah ku jirani in duba cikin littafin da muke rubuta bakin da suka sauka anan, amma tsaya mene ne sunan ka? Inji mai kula da sauke baki. ‘’suna na mista john ojo’’ inji Emeka.

Babban mai kula da bada dakuna, ganin abin dake faruwa nan take ya kira yaran sa, da ke karba bak’i ya gargade su game da abin da suke son suyi. Yace musu ‘’kai olu naga bakin ka na motsi kana son ka fadi inda mutumin yake ko. Kullum ina jan kunnen ku cewar al’adar wannan hotel din duk wanda yazo yana son ya ga wani anan hotel dole ne ya gaya muku sunan shi. Bayan haka kuma ku tabbatar kun buga tarho zuwa dakin wanda ake son a gani din, idan ya aminta da ya gansu sai ku bari su je dakin. Idan ba haka ba wata rana zaku ja wa kanku jangwam, domin ban aminta da wadannan mutane ba. Kai da ganin fuskar bakin nan kasan bata lafiya ba ce, ina tuhumar barayi ne.

‘’Ok sir, bari in buga mishi tarho’’ olu ya dauki tarho ya buga dakin Abubakar cewar ga wasu baki sun zo wurin shi game da harkar kwangila.

‘’Su wanene ke nemana yanzu?’’to ranka ya dade ina na sansu kuwa. Abubakar yace ‘’a a ina nufin menene sunan su?’’ ok sun ce a ga ya maka wai mr john ojo ko a barsu su karaso wajen ka? Abubakar yace a a ba bashi da wani abokin kwangila mai suna haka. ‘’ko yaya kamannin sa yake?’’ sai olu yace daya daga cikin su baki ne kakkaura yana da tababben hanci da tambo a fuskar sa. Abubakar ya ce bansansu kace ban sauka anan ba. Olu yace to ranka ya dade a huta lafiya sai da safe.

Oga yace bai sansu ba. To olu ka ga abin da nake gaya muku kenan domin irin haka ta taba faruwa wani ya zo neman dakin da wata mata ta sauka da cewar shi abokin mijinta ne aka gaya mishi lambar daki ashe shige yazo yi kuma ya sace mata kudi. Saboda haka muke tambayar wanda ake nema idan ya san mai neman shi kuma in ya yarda ya ganshi. Wai! Oga bari in sheda musu cewar bai sauka anan ba.

‘’Mr john babu wani mai suna Abubakar da ya sauka anan hotel din tsakanin jiya da yau, ina tsammanin hotel de rus kila ya sauka’’. Emeka ya buga tsaki yace to mungode sai da safe suka juya babu mai magana. Cikin haka sai chibuzo ya gyara murya ya soshi kansa, yace ‘’Emeka.. emeka.. can Emeka ya ansa yace ‘’menene zaka fara mana maganganun ka na banza ko?’’ kaji matsala ta da kai kenan Emeka maimakon ka natsu kaji maganar da mutum zai fada a a sai ka yi cikin shi da fada. Emeka yace to fadi maganar ka muji.

Shawara ta shine mu tafi wurin mai gasa naman can na kusa da masallaci mu tambaye shi ko ya ga wani mutum mai kama haka yazo nan hotel din, tun da dole ne yaje masallaci yin sallah domin nasan baya wasa da sallah. Ai kuwa gaskiya ne inji chukuma, domin yadda na ga yaron nan ya shiga ya dade wai suna duba sunan shi ban amince ba. Emeka yace aikin banza baka ji sun ce wai tsakanin jiya da yau suka bincika ba. To ko tsakanin shekaranjiya da yau ne... kai emeka ka bari muji shawarar chibuzo muji kila tayi amfani.

To Emeka kamar yadda nace da farko idan ya sauka wannan hotel din zai gaya mana, kaga da safe sai mu zo nan mu jira shi muga motar dai zaya shiga sai mu bishi zuwa cikin daji mutare...

‘’ka tsaya mana muji har idan ya sauka anan ko?’’ Emeka, nagaya maka katse hanzari ne bani so. Nan take chukuma ya hausu da fada cewar kada su tona asirinsu. ‘’Kuma kunsan cewar kowace shawara tana da kyawo sai idan ba a gwadata ba’’. Bayan sun k’are hayaniyar su sai su ka dunguma zuwa wurin mai nama. Da isar su wurin chibuzo ya yi cinikin tsoka mai kyau akan naira dubu da dari biyar a ka yanka musu suna ci. Emeka ya cika baki da nama sai ya tambayi mai naman cewar ‘’ don Allah malam tambaya muke ku ga wani Alhaji fari dogo mai dogon hanci da magaribar nan yayi sallah anan.

Kai oga yaya za ayi in san duk wanda ya zo sallah anan masallacin tunda ba mutun daya ya zo sallah ba. Kuma kasan nama nake sayarwa ba gadin masu sallah na zo yi legas ba. ‘’Mai nama yi hankuri ai ba fada bane tambayar ka nayi’’. Chibuzo yana cikin magana da mai nama sai ya hangi wasu yanmata su uku suna tafe wurin da suke. Dama chibuzo akwai neman mata ballantana ya hango irin nasa. Nana dan nan ya kira su domin kada Emeka ya dame su da surutansa har asirin su ya tonu,dama ransa ya baci rashin ganin Abubakar

‘’Ku zauna mana’’ chibuzo ya nuna da hannun sa inda benci yake’’. Emeka yana murmushi ya ce a yanka musu nama na naira dari bakwai, idan kuma kun kare ci sai muje cikin hotel mu hole. Kila dai yau a kawai disco?. Emeka yana tambayar yanmatan. Daya daga cikin yanmatan dake saye da wani bakin tabarau da dan siket iyakar cinyarta ta ce ta amsa mishi. ‘’E! Amma ba rawa muka zo yi ba munzo yawo ne kawai muga wasu abokanmu da kanzo da fatakwal. ‘’to ke me ne sunan ki?’’ inji Emeka, yarinyar ta amsa mishi ta ce ‘’ ni helen ake kira na. ‘’ sauran yanmatan kuwa suna ta faman hira da, daya daga cikin su da ke saye da buluwus daure da zanen atamfa ta shi tana yi wa chukuma rada a kunnen shi.

A lokacin da suke faman hira da yammatan ashe chibuzo ya hango wani tafe wajen mai naman kamar Abubakar, nan da nan sai ya juya fuskar ya bashi baya domin kada ya gane shi. Shi kuwa Abubakar ashe ya fito ne domin yana tsammanin su Emeka sun tafi tunda a dauki lokaci fiye da awa biyu. Sabo da haka ya fito domin ya sayi nama sa annan ya yi sallah isha. ‘’ yanka mini nama na naira dari biyar, amma ka d’an dumama shi don yayi zafi kafin in kare sallah. ‘’

Mai nama yace ‘’Aa wannan kamar Alhaji Abubakar?’’ ‘’Nine kuwa wallahi, Abdullahi mai nama yaushe ka baro gusau ne?’’ . abdullahi mai nama yace ‘’ai yanzu anyi shekara daya da na taho nan, domin kasan kasuwar nama tafi riba anan kudu. Amma rankaya dade yaushe ka iso legas.’’ Abubakar ya amsa masa da cewar yau da safe ya zo amma zai bargari da sassafe gobe domin yana ganin akwai masu neman sa da lahani. Bayan ya kare sallar isha ya zo ya karbi naman sa, suka yi bankwana mai nama yace mishi idan yaje gusau yana gaida kaninsa saidu.

Emeka da chukuma basu san abin da ke faruwa ba domin yammatan da suke tare sun dauke musu hankali, chibuzo kadai ya kula nan da nan da juyawar Abubakar daga wurin mai nama sai shima ya nufo mai naman ya na tambayar shi ko garin su daya ne domin yaga sun labari. Mai nama ya shedawa chibuzo cewar ai garin su daya ne kuma su makwabtan juna ne da kaninsa a GRA.

Chibuzo ya juya ya cewa sauran abokansa dacewar su tashi su tafi wurin disco kada a rufe kofar shiga. Nan da nan ba gardama suka kama hanya da su helen. ‘’ kai oga ban gane be yaya kun tafi ba ku bani kudin nama ba?’’ inji mai nama. ‘’mts wallahi mun manta ne yi hankuri’’. Inji emeka, yasa hannu aljihun wandon sa ya ciro kudin nama ya biya suka kama hanyar shiga dakin rawa. Lokacin da suka shiga cikin hotel sai chibuzo ya yo kiran emeka ya rada masa duka abin da ya faru tsakanin sa da mai nama a lokacin da abubakar ya zo sayen nama, nan take emeka ya buga ihu yace ‘’chineke’’ domin jin dadi da shirin keta.

Emeka yace ‘’haba chibuzo yaya baka gaya mini ba domin in ganshi kafin ya mutu gobe?’’. chibuzo ya bude baki yace ‘’Kai a wannan kuskuri ne babba na san halin ka domin garajen ka da doki, sai ya gane komai ya lalace kuma ka san yansanda suna neman mu tun wancan lokacin. Amma bayan an kare rawa zan sheda maka abin da yace. Chukuma da ganin emeka da chibuzo suna rada sai kuwa ya baro su helen, yana tsammanin ana son a yi mishi wata makarkashiya ce game da yammatan.

‘’Emeka wallahi munyi dace domin yammatan masu ganewa ne, kuma sun ce daga garin jos suke amma suna sana’a ne anan ni dai na kama mai saye da atamfa’’. Emeka haushi ya kama shi yace ‘’ kai banza ne, ba abin da kasa a gaba sai yammata kaga ta wannan hanyar zaka tona mana asiri. Kunya ta kama chukuma sai susar kansa ya ke yana yak’e ‘’. gaskiya emeka bazan tona asirin mu ga yammata ba. To kabari zamu sheda maka abin da ake ciki, idan an kare disco zamu je mu tsotsi kwalaben giya hudu-hudu kafin kaji labarin da kyau.

Bayan an yi nisa da disco, sai chibuzo ya kira sauran yan uwan nasa suka je gafen da ake sayar da barasa suka sha tatil kamar yadda suka alkawarta ma ransu kafin su je wurin yin mugunyar shawarar su. ‘’ to helen, sai da safe kenen gobe sai mu hadu anan ki gayawa sauran abokan ki da karfe tara na yamma. ‘’ ita kuma ta amsa ok chukum sai gobe.’’

Chibuzo ya fedewa abokan sa biri har wutsiya, sa’annan suka shiga shawarar da zata fi dacewa. ‘’ chibuzo kasan abin da za a yi anan shine tunda yanzu karfe biyu da rabi na dare me zai hana mu tsaya a nan mai makon muce muje gida mu shiryo kaga anan gari zai waye, kuma shi yace da asussuba zai bar garin nan.’’ E, gaskiyar ka emeka, amma tunda motar tawa tana da karfi ai sai muje mu dauko bindigar chibuzo sai mu bishi a baya. Tunda kome tsiya ‘cherokee jeep’ tana dasawa da kowace irin mota.’’ Bance a’a ba chukuma mu gwada amma kashe shi zamu yi sa’annan mu dauke kome cikin motar mu k’onata, da ga nan mu je garin Gusau gidan sa mu sace kome da ke ciki.’’

To ai ba kone ta kawai ne ba, kafin a kona motar zamu ture ta gafen hanya mu birkice ta sai mu sa shi a chiki mu daure da belt din direba a cinna mata wuta. Kaga idan yansanda sun zo bincike sai su yi tsammanin hadari yayi yana bacci motar ta kama da wuta.’’

Nan da nan suka yadda da shawarar chibuzo, suka fashe da dariya harda taffa hannuwa. Chukuma da emeka suka shiga mota zuwa dauko bindiga shikuwa chibozo a kabar shi a bakin hotel din domin ya ko da zaya ga fitowar abubakar sai ya sacce iskar tayar motar kafin su dawo. Kafin karfe uku da rabi na safe sun riga sun dawo kowa ya nemi wuri ya zauna ana jiran gogan ya fito daga cikin hotel.

‘’Emeka tunda yana hana maka samu kwangila yakamata idan muka same shi sai ka mammare shi sa’ilin mu wulakantar da shi kafin a kashe shi.’’ Gaskiyar ka chukuma domin duniyar nan ba wanda na tsana in gani kamar shi, ya hana mini cigaba ko ta ina wannan shegen mutum.

‘’Kai ku duba kamar ga shi nan fitowa zai shiga mota.’’ Emeka ya ce ‘’ Lallai yanzu na yadda chibuzo kana da kula kwarai, ba irin da ba da ka ke kamar wani soko.’’ Emeka ya ce. ‘’ mu tsaya har ya shiga mota idan ya fita sai mu bishi da mota a gindi- a gindi har mu isa daji sai chukuma ka wuce shi a guje, idan mu ka sha gaban sa, sai kai kuma chubuzo kayi maza ka diro daga mota ni kuwa sai in nuna mishi bindiga wand dolen sa ya tsaya cik.’’

Abubakar yana duba madubin motar sai ya lura da wata mota ja tana biye da shi. Bayan kamar minti talatin kuma yaga motar ta kara matse wa a gindin motar sa. Ganin halin da wannan motar ke ciki sai ya san kila wadannan mutane da ke cikin motar bana lafiya bani. Nan take ya canza giyar motar sa ya kara wuta ya zura a guje. Su emeka kuwa suka ce da wa Allah ya hada su ba da shi ba. Abubakar ya lura tabas motar sa ake bi kuma kila da mugun nufi, nan take ya kara take totur din motar sa yana gudu akan dari da tamanin malejin motar sa. Chikin wannan halin ya chimma wata mota a gaban sa kuma a wancan gafen ga babar motar tantebur zuwa. Ganin wannan halin na gaba kura baya sa yaki, sai rutsa sakanin motar da ke gaban sa da tantebur din wanda nan take ya yi fitar kutsu. Shi kuwa diraban babar motar tatantebur din sai zagin sa yake tsammanin irin direbobin nan ne masu tukin ganganci.

Motar su emeka da ta suka zo domin suma su ratsa kamar yadda gogan yayi ai kuwa sai direban tantabur din da ke dauke da shanu tayi cikin su dole suka saki hanya sitiyarin motar su ya kwace wa chukuma,ta nufi gada da su . Amma da yake direban barayi ne sai ya ciyo kanta, ta sake kwacewa ta nufi irin tubalinnan na gafen hanya da ke nuni da nisan kilomita anan ne motar ta banke shi. Galashin motar da bankar wannan tubalin nan take ya fashe ratsa-ratsa a fuskar chukuma, shi kuwa chibuzo da ke zaune a gafen diraba da bindiga, kan shi ya bugi karfen da ke tsakanin gilas din gaba da gafen kofar mota. Wannan mummunan dukan ya sa kan shi nan take ya fashe sai jini ke zuba tararara.

Bayan abubakar, ya sha da kyar ya isa gida matar tayi murna da zuwan sa ta karbar masa kayi ya ci abinci sai ya ce. ‘’Ke balaraba, a yau sa’a nayi Allah yayi mini gyadar dogo’’ sai matar tace. ‘’A a mai gida takobin mata ko lafiya?’’ abubakar ya ce ai ina tsammanin barayi suka biyo su yi mini fashi a hanyar legas.’’ Balaraba ta ce. yan fashi fa ka ce Abubakar?’’ ‘’E, to balaraba idan ba yan fashi ba mota ce ke bina a gindi- a ginda babu alamar inda ta fito kuma idan na kara gudu su kara, amma Allah cikin ikon sa nayi musu fintinkau.’’

‘’ to mallam zuwa legas din nan dai ba dole ne ba, haka shekarun da suka wuce kaje suka yi maka duka ko ina jikan ka dawo da rauni na yi ta faman jinya. Ka tuna fa ko inna sa’a ta shawarce ka da ka daina zuwa wannan kasar anna. Ni dai wallahi bana son ka kara zuwa.’’ Abubakar yace to balaraba can dai ne ba ki son na je ko? Insha Allahu bazan kara ba, ko banza a kace jiki magayi domin da kyar na sha wannan karon.’’ Bayan Abubakar ya sha hura mai sanyi sai matar ta ce masa. ‘’ Abubakar, inna ta kawo zayyad domin zata je bukin aure kuma zata yi kamar kwana uku. Domin haka ta kawo shi kada ya rasa zuwa makaranta, yanzu haka ya fita zuwa wasa a makwabta.

Balaraba da mijinta suna zaune a tsakar gida suna hirar su, sai abubakar yace kai balaraba ni kuwa kwanakin nan wani haske kawai nake ganin kina yi, na lura idan kina da ciki kyawon ki yafi fitowa kwarai.’’ Sai balaraba ta ce ‘’ to ka fara kenan’’. Abubakar ya kallon matar sa da sha’awa sai yace ‘’ to balaraba ai gaskiya a fade ta’’.

Bayan sun ya kare ba’a da matar sa sai ya ce mata ‘’yau ya kamata ki shirya mu je gona da yamma domin ki ga yadda waken nan ya yi kyau’’. Sai balaraba ta amsa masa da cewar ‘’wallahi kuwa ko banza yau ina son in sha iska’’. Abubakar yana murmushi sai ya ce ke balaraba, ina ganin wanan watan ake sa ran haihuwar ki ko?’’ sai balaraba ta amsa ma sa da cewar ‘’kai wannan mutum akwai kwankwanto wato har kana kidaye da watan da zan haihu? To ai ke yana da kyau miji ya san lokacin da matar sa zata haihu idan tana da ciki haka yana nuna kaunar da ke tsakanin su.

Bayan mai gidan ya farka daga bacci sai suka kama hanyar zuwa gona kamar yadda suka zanta. Zayyad yana zaune a gidan baya ya mayar da fuskar sa baya yana kallon motacin da ke wuce wa ta gilashin baya yana faman wakoki. Ita kuwa uwar sa tana zaune a gaban mota a kujerar fasinja. ‘’ rakumi-rakumi zololo! Mai da gaban ka zuwa adar mota ta tafi ta barka, balaraba dubi rakumi tara da jaririn shi. Kai dubi bakin shi yana kumfa balaraba ko yana hauka ne?’’ Abubakar ya dubi dansa yana dariya yace ma sa. ‘’ to me ya dameka da bakin shi yana kumfa? Dama kai yake so ya kama domin kana yi wa inna sa’a barna da yawa’’. Zayyad ya ce. ‘’To ai baba na dade banyi mata barna ba kuma dama bazan kara ba’’. ‘’Karya kake sai na kai ka ya cije ka.’’

Sun isa gonar suka iske masu aiki suna ta faman noma domin yawan ruwan da ake yasa ciyawa tana kokarin mamaye waken da aka shuka. Gashi kuwa waken sai yado yake domin taki da maganin kwarin da aka sa mishi. Bayan sun kare zagayen gonar suka juya zuwa gida, bayan sallar magariba su ka ci abincin yamma nan da nan balaraba ta fara bacci ta bar mijinta da dansa suna kallon talabijin. Abubakar ya shimfede dansa yana batun ya kwanta sai kuwa yaji ihun matar sa. Ya fada dakin ta tare da zayyad a guje ya iske ta na zufa kamar wadda aka kara bakin wutar gashin naman ragon layya. Abubakar ya kama matarsa ya rungume yana tambayar ta lafiya amma ta kasa amsa masa, sai jikin ta ke faman bari kamar wadda sanyi ya kama.

‘’zayyad bude firij ka dauko ruwa da moda in baiwa uwarka ta sha’’. Bayan an kawo ruwan sanyi ta sha hankalinta ya dawo jikin ta. Sai tace. ‘’ wallahi mafarki nayi munje daji da kai sai ga damisa tazo zata cinye zayyad, kai kuwa sai ka kamata da dambe.... ‘’to ki bar kuka mana.’’ ‘’To mallam. Kamar yadda nake fada, can sai damisar ta rikede ta koma wani bakin kwado kato idon sa kamar wuta kana ta faman fada da shi. Kuna cikin fadan sai ya cije maka kafa har ta tsinke da ga jikin ka’’. Abubakar yace to balaraba ya isa mafarki ne kawai kike kila kin cika cikin ki da abinci da yawa. Ko kuwa baki kwanta daidai ba. Idan kina kuka haka kamar wadda a ka yi wa aiken mutuwa, ai ko jinjirin da ke cikin cikin ki shima ya wahala’’.

Abubakar ya juya zai fita sai matar sa ta ce. ‘’kai Abubakar ina zaka je? Gaskiya ba zan barka kaje ka barni ba domin ina jin tsoro kwarai’’. Mijin ya ce Balaraba. ‘’To ai ba wani wuri zan je ba, gida zan rufe na manta ban rufe ba har na yi niyar kwanta wa’’. Bayan mijin ya ta fi rufe gida sai zayyad ya ce wa mamar sa. Balaraba me ya sameki kike kuka, ko jaririn da ke cikin ki ne ya cije ki’’? balaraba ta ce kai! wallahi ba ka gajiya da tambayoyin ka na rashin dalili. Wa ya gaya maka jariri yana cizo’’? zayyad amsa ya ce. ‘’A gidan su haliru na ga dan tsiton yaron nan ya ciji mamar shi lokacin da yake shan mama’’.

Balaraba haka dai ta kwana a zaune domin hankalinta ya tashi da wannan mafarkin har sai da aka yi kiran asalatu ta samu ta yi bacci. Da gari ya waye Abubakar ya kai zayyad zuwa wurin kakarsa domin ta aiko cewar ta dawo.

‘’salamu alaikum’’! wa’alaikum salam, aa Abubakar! Ka dawo daga legas domin kafin inje buki ance mini ka tafi legas’’. ‘’naam inna shekaranjiya na dawo da yamma’’. Zayyad ya ga kakar sa yaji dadi yace. ‘’sa’a me kika sayo mini? Kinga tunda kika tafi balaraba duka na takeyi ko ban yi laifi ba’’. ‘’kai rufe mana bakin ka’’. Inji Abubakar yana hararar zayyad. ‘’yaki ya rufe muku baki, yaro da bakin sa yaki fadin abinda aka yi mishi dubi yadda yaro yabi ya rame kwana hudu kawai. Idan zan sake irin wannan tafiyar da kai zan tafi’’. ‘’ke kuwa inna daga kwana hudu sai ace yaro ya rame, yaron ne ya cika kiriniya na ji ma ance idan kika aike shi sai yaga dama yake zuwa’’.

Inna sa’a ta ce. ‘’kai! Bashi nake tambayar ka ba, yaya legas din ina fatar lafiya? Abubakar yace ‘’lafiya kalau inna’’. Ita kuwa balaraba fa? Ina fatar kalau take ko dan yanzu tana cikin watan ta, kila yau ko gobe’’. Abubakar ya ce to inna lafiya hakanan’’. ‘’Kamar yaya hakanan an taba lafiya hakanan’’? abubakar ya dukar da kansa yana wasa da danmakullin motarsa. Sai ya Abubakar ya kwashe komi ya gaya wa uwar game da mafarkin da matar sa ta yi jiya, sa’annan ya sheda uwar sa cewar yanzu haka tana can tana fama da dan zazzabi.

Inna sa’a ta ce wa Abubakar. ‘’to dannan Allah ya sauwaka, yanzu idan zaka tafi sai ka biya gidan malam nagwamatse ka karba mata rubutu ko ma menene Allah ya kare mu. Kuma ka tabbatar da kayi sadaka. ‘’Abubakar yace. To inna bari in tafi sai dai bazan dawo da yamma ba’’. To naji amma kafin ka tafi gobe sai kaje da yaron nan don ka biya masa kudin makaranta. ‘’ inna wane kudin makaranta kuma ake bukata yanzu?

‘’ to ka tambaye shi kaji mana’’. Abubakar yace kai wane kudin makaranta ake so? Aa baba hedimasta yace inzo in karbi kudi naira dari biyar domin cika fom, wanda zan dauki jarabawa tare da yan aji shida’’. Abubakar mamaki ya kamashi yace. ‘’To amma ajin ka nawa da zaka yi jarabawa da yan aji shida?’’.

Zayyad yace. ‘’Baba aji hudu nike yanzu’’. Inna bari gobe zan je dashi inji abin da ake ciki.





Download 75,59 Kb.

Do'stlaringiz bilan baham:
1   2   3   4   5   6




Ma'lumotlar bazasi mualliflik huquqi bilan himoyalangan ©hozir.org 2024
ma'muriyatiga murojaat qiling

kiriting | ro'yxatdan o'tish
    Bosh sahifa
юртда тантана
Боғда битган
Бугун юртда
Эшитганлар жилманглар
Эшитмадим деманглар
битган бодомлар
Yangiariq tumani
qitish marakazi
Raqamli texnologiyalar
ilishida muhokamadan
tasdiqqa tavsiya
tavsiya etilgan
iqtisodiyot kafedrasi
steiermarkischen landesregierung
asarlaringizni yuboring
o'zingizning asarlaringizni
Iltimos faqat
faqat o'zingizning
steierm rkischen
landesregierung fachabteilung
rkischen landesregierung
hamshira loyihasi
loyihasi mavsum
faolyatining oqibatlari
asosiy adabiyotlar
fakulteti ahborot
ahborot havfsizligi
havfsizligi kafedrasi
fanidan bo’yicha
fakulteti iqtisodiyot
boshqaruv fakulteti
chiqarishda boshqaruv
ishlab chiqarishda
iqtisodiyot fakultet
multiservis tarmoqlari
fanidan asosiy
Uzbek fanidan
mavzulari potok
asosidagi multiservis
'aliyyil a'ziym
billahil 'aliyyil
illaa billahil
quvvata illaa
falah' deganida
Kompyuter savodxonligi
bo’yicha mustaqil
'alal falah'
Hayya 'alal
'alas soloh
Hayya 'alas
mavsum boyicha


yuklab olish