HAIHUWA
Ayyururui!!! Allah mai iko, yau Balaraba ta sauka. Sannu kiji barka da sauka, inji kishiyar uwar ta wadda ta karbi haihuwar kafin arbiki tazo. Kinga har yanzu arbiki bata iso ba Allah yasa lafiya. ‘’Assalamu alaikum!’’.. kekuwa arbiki ana ta jiranki shiru kamar an shuka dussa, ko lafiya. Yi hankuri ýar uwa wallahi tasi tayi wuya domin yan rod safti suna taron abubuwan hawa yau. Kinsan direbobin basu kula da motacin.
Ta sauka lafiya ko? E yanzu tunda Allah ya kawoki sai ki yankewa jinjiri cibi. ‘’To yar uwa masha Allah, jinjiri kuwa kyakkyawa kuma fari, kai wannan sai yayi hanci mai kyawo. Balaraba, sannu da kokari ko don naga murmushi take, da gani haihuwar tazo da sauki’’. Wa ya gayamiki yarinya tayi awa daya tana nakuda hankalin gida duk ya tashi ai ba domin motar makwabcin mu ta lalace ba da tuni muna asibiti. Kai sannu Balaraba inji arbiki ta rike baki tana juyayin abin da rashin samun tasi da ya hassadar.
Kishiyar uwar balaraba taje dakin uwar balaraba, domin su aikawa iyayen Abubakar cewar an haihu. ‘’to kekuma kande, sai kinzo kin tambayeni ai kome kika zartar yayi.’’ Aa kaji balki ai shawara dadi ke gareta, amma bari in kira yarannan kofar gida su kai sako. Kai Ibrahim ibrahim ibrahim! Na am kai idan kuna shegiyar kwallon nan baku jin kira ko kadan. Kashirya kaje gidan su Abubakar ka sheda musu cewar yayar ka ta haihu. To gidan Abubakar ko inda babansa yake? E inda baban sa yake amma mamar sa zaka gayawa. Kace namiji aka samu kuma ta haihu lafiya kalau a gida.
Malam kaji balaraba ta haihu? Munkai ga jika yau .Aa namiji muka samu ashe nakai ga abokin dambe ko me ki kace sa’a . wai ga shi kuwa Abubakar baya nan idan ya samu wannan labari nasan dariya daga kunne har kunne. To malam ai gashi bai dawo daga Ibadan ba. Kinsan kuwa cewa yayi shekaranjiya talata zai dawo Allah yasa lafiya. Ai malam sai dai ayita sha’ani wai an cuci bakauye. Ke! bashi ba, kin kuwa ba yaron nan tukuici? Aa ai na manta wallahi. Kai Ibrahim amshi tukuici ladar fadin haihuwa.
Inna na gode! Aa ga shegantaka karba mana! Baban Abubakar ya daka masa tsawa sa’an nan ya karba. To Ibrahim ka shedawa kande, cewar ina nan zuwa yanzu. Malam zan shirya inje kafin azahar na dawo. Kila ba domin nasan ke da dawo wa wannan gida sai bayan magariba ko isha. Bayan saa ta tafi ganin jariri baban Abubakar ya zauna cikin irin kujerar nan ta tsofaffi da ake hadawa da gwado a kishin gida a ciki. Yana kwance yana sauraron labarun karfe goma shabiyu na rana da ga rediyon kaduna, har bacci ya kwashe shi har goron dake hannun sa ya fadi. Wurin daukar goron daya fadi awakin gidan suka ture dan tsohon rediyon nan da nan shi kuma ya farka.
Kai wadannan shegun awaki basu barin mutun shakat, su ture wannan su ture wancan kayi kora har ka gaji. Yasa hannu ya dauko rediyon yayi burkuta har ya gaji bai kama tashoshin rediyon ba. Kai wadannan awaki da masifa suke,rediyon nan yau shekarar sa talatin kenan. Yanzu indan ka sayi wani sabo bashi da karko kaman wannan,Allah ya kawo yaron nan ya kai shi wurin gyara.
Maroka sun taru, jama’a cike manya manyan yan kwangila duk sun hallara da masu rike da mukaman siyasa domin radawa jaririn da aka haifawa Abubakar suna. Maroka kuwa kasuwar su kawai suke ci. ‘’ Allah ya raya mana jariri dan manyan yan kwangila, Allah yasa ya gaji ubansa da kyauta da fara’a da haba haba da mutane. Barka da zuwa alhaji idris dan kwangila na hannun daman alhaji Abubakar. Allah ya ja zamani da daukaka, duk attajirin da kenan kuma ban samu kwabo gare shi ba to kuwa ko wuta ta barshi. Ni malam musa sarkin marokan garin Gusau kwata, ina rokon alhaji Abubakar da ka bani kyautar mota....
A saurara jama’a, sunan jariri Zayyad! Allah ya raya mana zayyad, yaro mai kama da ubansa... fatiha amin amin. Fatiha baki daya Allah ya dayyaba shi. Bayan an kammala zanen suna mutane da sauran abokan arziki suka rika duraroya domin taya Abubakar murna, amma sai mamaki ya kama su domin rauni da ke fuskar sa.
Alhaji Abubakar lafiya me nake gani haka a fuskarka? Ka samu hatsarin mota ne? Alhaji idris ai barayi ne an fashi suka rutsa da ni a daki da nake sauka a Ibadan. Ya sheda musu duk yadda a kayi sa’annan. Jama’a ina mika godiya a gareku kan girmama wannan gayyata da na yi muku wajen adduar radin sunan dan da aka haifa mani saboda haka sai kuma mu dunguma mu tafi wurin cin liyafa da aka shirya muku a gidan mahaifi na a unguwar toka.
Bayan an kara didima maroka sun watse sai mahaifiyar Abubakar ta aika masa ta neman shi nan take ta haushi da fada da cewar ‘’ to ai ga irinta nan da nike gaya maka cewar ni legas din nan kulum ina ji cikin rediyon malam cewar ana cigiyar mutane saboda yawan yankan kanu da suke to gashi kama da yanzu sun fille naka. Yanzu ji irin wannan raunuka da ka samu. Abubakar ya sunkuyar da kansa yana mai sauraron mahaifiyar shi. Ke ish.. ish.. kai wannan shegiyar akuya a kwai banna. Abubakar ya tashi ya kora awakin waje. ‘’ba haka shegiyar akuyar ta ture mini rediyo ya lalace ba’’
Sai da na fada maka tun farko da cewar ka tsaya nan gida da kwangilar ka amma ka ki maganar mu,to yanzu ji irin wannan barna. Kuma kasan kai kenan dan guda-guda sai kuwa wannan jikan nawa... ‘’ inna abin da Allah ya kawo ko da ina gida zai faru’’! to Allah ya sawwaka kuma ya kare gaba amin. Abubaka ya dauki izini daga baban shi ya tafi gida domin ya huta.
Lokacin da zayyad ya cika wata uku da haihuwa iyayen balaraba suka mayar da ita gidan mijinta, a inda duka mata da mijin suna cikin fara’a shikuma zayyad yana da koshin lafiya har ya san yayi dariya idan aka yi mishi wasa. Nan take matar ta shiga kikkimtsa gida domin duk gidan ya fita da ga yadda ta barshi kafin ta je haihuwa.domin mijin nata ya kasa share gidan tun da ta tafi haihuwa komai na gidan dake waje yayi kura.
Abubakar kana cin abinci kuwa naga tangarorin nan duk da kura kamar inda aka yi yakin badar. Ai ina na ga lokacin dafa abinci, hotel na ke zuwa in saya in ci ko kuwa inje gida wurin inna. Yana bata labari yana rungume da zayyad yana yi mishi tawai, shi kuwa dariya yake ta faman yi.
Kai! kai! Mmn. balaraba karbe shi, karbe shi! Hala dai yayi maka fitsari? Kai in fitsari ne da sauki, zawo ya fetso mini dubi ya b’ata mini farar shaddar da nake son inje wurin aiki da ita. Balaraba kuwa dariyar maigidan nata take, ganin yadda ya murtuk’e hancin sa domin tsamin zawon yaron. ‘’Ki karbe shi mana kina ta dariya gashi har ya yi mini bulbuli, kai amma kina k’ok’ari ai duk k’arni nake. To ai wannan shine wahalar zama uwar kenan, kai ma ka d’and’ana kaji yadda raino yake.
Bayan ya wanke jikin sa ya sake sabon shiri, ita kuwa ta cigaba da bai wa zayyad mama. Kingani wato da gangan ki ka miko mini shi babu nafkin ko? Ki yi sauri kinga har karfe tara da rabi ta yi na kuwa sheda miki cewar karfe goma ake nema na. Ki lallashe shi ya fara kuka. Balaraba ta ce kai yi shiru dan samari. Ta karbe shi daga hannun uban tana yi mishi tawai ta na waka ‘’kai yi shiru dan fari abin so ne... ‘’ kin mutu in su inna suka kama ki kina yi mishi waka kin shiga uku, wato baki kunyar shi ko?’’ haba Abubakar ban ji kunyar fadan sunan ka ba zanji kunyar kiran da ai tun a gida na fada wa su baba cewar wannan al-adar mutanen zamanin da ne. Kai dai a sauka lafiya, kuma kar ka manta ka sayo multibait d’in. Wane iri? yana tambayar ta bayan har ya kai kofar gida. Na ruwa mana kana tsammanin na kwayoyi ai zayyad ne zan baiwa.
A lokacin da zayyad ya kai shekara uku, kullum yana tare da baban sa, domin idan ya dawo daga tafiye tafiyen da yake yana kawo wa zayyad biskit, chakula da sauran kayan wasa na yara irin mota mai tuka kanta. Balaraba tace Abubakar ka gani yanzu yaron nan har magana yake yi kwarai. Ai balaraba abin har ya bani mamaki domin tsaran sa har yanzu basu iya magana ba. Uban ya daga murya ya kira zayyad wanda yake tare da kawun sa Ibrahim. Kai zayyad ina uwarka? Gatanan. Zayyad ya nuna wa baban sa inda uwar ke zaune. Baba! Ina mota na? Kaje daki ka dauko tana na saman gado. Wallahi mallam yaron nan ya yi kama da kai. To ai dama bahaushe yace kyayon da ya gaji uban shi.
Abubakar wai yaya batun gonar ka? tun da a kayi shuka ban kara jin kayi maganar ta ba, lafiya dai ko? Lafiya mana balaraba, kesan da cewar yawace yawacen nan sun hana mini inje in zagaya. Na hannunta kome a hannun malam tanko, shi na baiwa kudin noma da sauran ayukka, amma gobe ranar lahadi zan je in ganewa idanuna halin da gonar ta ke ciki. Da gari ya waye, sai ya kama hanyar zuwa gonar tare da matar sa inda ya gane wa kansa halin da gonar ke ciki. Nan da nan dashi da matar suka yi mamakin yadda amfani ya fara samuwa.
To masha-Allah! Ai kuwa alkama ta yi kyau dube yabanya stanwa shar da gani inshallah za a samu ido mai kyau. ‘’to Allah ya sa balaraba, domin abin tsoro shine ruwan da suke yin ranko, a wani lokacin ma basu bayar da ruwan sam. Muje in kai ki wurin yar gidan ki masara’’. kai- kai! Abubakar wallahi malam tanko bai cuce ka ba samun wanda zai yi aiki tsakani da Allah wannan zamani yana da wuya kamar haka. Ke kuwa naira dubu ashirin na bashi domin kar a samu cikas ga aikin. Duk da haka wallahi yayi adalci kwarai da gaske, kai dai ba ka hadu da yan zamani masu ido a keya ba.
Ni fa kasan jaraba ta da masara dole sai na k’alla domin na gasa in ci. A a muci dai! domin nima ina so, amma kiyi sauri domin kin san ina da bako, Alhaji sani zai kawo mana ziyara. ‘’kai na san shi kuwa?’’ kwarai ki ka san shi wanda na gaya miki ya ara mini taya ranar da tayi mini faci. ‘’ ai kuwa na tuna wanda ya baka gudumuwar raguna biyu lokacin sunan zayyad’’. Tabbas shi ai ke san yaro na ne a da amma yanzu abokina, domin ni na sa shi a hanyar sanaar kwangila kuma na hada shi da mutanen kirki. Kin ga yanzu tun da akwai abota ba safai a kan gane sai idan in shi ya fada.
Ba yan sun koma gida suna cikin hira sai suka ji sallama, Abubakar ya amsa sallamar ‘’yace wanene?’’ Alhaji sani ne. A a kai da nake ta jira tun karfe biyu sai karfe uku da minti goma sha biyar. Wallahi ina kallon wani katun ne har lokaci ya kure ko da na farga karfe uku ta riga ta yi. Balaraba kawo mana hura domin ga Alhaji sani ya iso. To mallam ai kuwa na riga na dafa muku abinci. Nan take ta shirya teburin cin abinci inda ta jera tangarori masu kawa cike da shinkafa, salad, alkaki, nama soyayye da kuma soyayen kwai. Sa an nan ta a jiye kwalin lemon ‘’five alive’’ domin su sha. To bissimillah Alhaji sani ga abinci nan an shirya. Nan take ta kunna musu satalait domin suyi kallon labarun BBC.
Abubakar Allah ya kashe ya baka, don Allah ji yadda matar nan ke kulawa da kai, ga ladabi. kuma uwa uba, ga ta iya abinci. Ni tuntuni na san ba banza nake ganin ka kamar wani dan bature ba dubi jikin ka lukyu-lukyu fatar ka tana sheki. Kai Alhaji sani, har yanzu baka da ranar da zaka dai na santi. To ai gaskiya a fade ta wannan ba santi ne ba. Abubakar ya fashe da dariya bakin sa cike da suyayyen naman kaza. Bayan sun kare cin abinci Alhaji sani ya yi sallama da balaraba shikuma Abubakar ya raka shi waje inda ya shiga motar sa ya tafi.
2Suna tsakiyar hira da matar sai a ka dauke wuta lantarki can kuwa zayyad ya rusa kuka domin duhu.
Kai yi shiru gani nan bari inzo kaji. Ke tsaya kada ki ture shi wajen garaje cikin wannan duhu, ki laluba gafen talabijin dinnan akwai tocila sai ki haska. Kai yan NEPA mutanen banza ne, ana zaune kawai sai su dauke wuta ba dalili. Ke balaraba ina ki ka sani tunda ba aikin ki bane, ki kasan wata kila naurorin tiransifomar sune suka samu yan matsaloli ko kuma gidan wani yana cikin hatsari da dole sai an dauke wuta. Suna cikin maganar sai aka mayar da wutar ko ina ya haskake, har hasken ya kashe wa Abubakar idanu
Kai maigida dubi wani marmadi da kake da ido kamar wanda yayi wa sarki karya asiri ya tonu. Kai wannan shi ake cewa taka tudunka ka hangi na wani, yanzu ke banyi dariyar yadda ki kayi da na ki idanun kamar a baiwa kyanwa kwaya. Kai malam wace irin kyanwa. Balaraba ta matso ta rungume mijinta tana shash-shafa gashin kirjin shi da ya yi liyaliya. Don Allah dubi yadda inyamuran banzan nan suka bata maka fuska gashi ina sun fuskar nan taka har dai gashin bakin nan da saje. Abubakar ya yi murmushi yace ki kyale yan banzan barayi. Balaraba tana hamma tace wa mijinta malam bari inje in kwanta domin bacci nake ji. Ke kullum ga ki nan kamar kaza shiga bacci da wuri.
Abubakar ya kira dan sa domin ya raka shi domin ya sayo burodi tsallaken titi. Suna cikin tafiya shi kuwa zayyad tambayoyi kawai ya ke yi. ‘’baba wai me yasa mashin da keke suke tafiya basu faduwa? Kuma gasu taya biyu ne da su. ‘’Kai zayyad bansan yadda zan amsa maka wad’annan tambayoyi naka ba, yaro da tambayar kwan-kwanto, ka bari idan ka kara girma zan amsa maka wannan domin ansa ce da ke bukarar sanin kimiya kaji ko! ‘’ me a ke nufi da kimiya kuma baba? Haka dai yayi ta fama da tamboyiyin zayyad har suka dawo gida.
Do'stlaringiz bilan baham: |