‘’Balaraba kinga shekara da shekaru bamu samu haihuwa ba, amma tunda yanzu Allah ya nufe mu wannan shekarar har kin samu ciki to sai mu yi wa Allah godiya



Download 75,59 Kb.
bet4/6
Sana02.03.2017
Hajmi75,59 Kb.
#3698
1   2   3   4   5   6

JINYA


Su chukuma da yan uwansa sunyi sa’a wata motar abokin emeka tana tafe sai ta hadu da su sunyi wannan hadari, sai aka kwashe su zuwa asibiti inda aka yi wa chibuzo dinki a kan shi da ya fashe, chukuma kuwa an kwantar da shi. Emeka shi Allah ya yi mishi gyadar dogo domin ko kujewa bai yi ba, saboda haka shi ke faman zurga-zurgar sayen maganin chukuma da kuma gyaran motar su da ta lalace.

Emeka ya ga likita na wucewa sai yace. ‘’Dokta! Yaya jikin abokin nawa ne’’? wane abokin ka? Inji likita. Emeka yace wanda muka samu hatsari satin da ya shige. Likita yace. ‘’Ayya don Allah kayi hankuri domin ban gane ka bane, abokin ka yana nan yana samun sauki. Yanzu haka nas-nas suna can suna sa mishi jini, amma nan da kwana hudu zai warke tangaram domin kada ka ji wani tsoro. Amma fa matsala daya ita ce, idon sa na hagu ba zaya rika gani sosai ba. Kasan cewar gilas din motar ku da ya tarwatse ya bata mishi kwayar idon’’. Emeka yace. ‘’babu kome idan dai zai rika gani ko da dushi-dushi ne.’’

Bayan sun kare zance da likita nan da nan aka bari Emeka yaje gadon da abokin sa ke kwance domin ya ganshi kuma ya bashi yan kayayykin marmari da ya sayo mishi.

‘’allo emeka harka iso naga alamun baka gajiya da zurga-zurga’’. Emeka yace. ‘’To chukuma ya aka iya, ga wadannan kayan marmari ka dan taba. Yanzu nake tare da dokta yace mini yace mini idon ka na hagu baya gani kwarai’’. Chukuma yana faman shashafa idon da aka like da auduga da filasta. Yana fadawa emeka cewar a halin da yake ciki duhu ka wai yake gani da idon. Dayan idon kuwa gashi nan jawur kamar barkonon. Abin ka da wahala nan take gashi har ya rame kamar wanda yayi jinyar wata biyu.

Emeka yace wa chibuzo to kai ai naka yana da sauki dubi wancan mutumin.’’ Ya nuna mishi wani dake kwance akan gado mai lamba goma dake karshen dakin yana faman nishi mai karfi domin zafin ciwon. Kuma gashi likitoci duk sun zagaye shi ana yi mishi allurai a ka kuma sashe cikin wani tanti domin ya samu isashen iskan shaka.

‘’Emeka shin wai yaya motar ne, ko an samu janyo ta daga dajin kuwa’’? ‘’E! Ai tun wancan satin na sa aka janyo ta daga can, gobe ma zasu kare gyaran’’.

Bayan an sallami chukuma daga asibiti domin samun saukin da yayi, emeka da chibuzo suka zo da mota suka mayar da shi gida. Chukuma yana zaune inda yake karbar gaisuwa daga makwabtan sa da kuma abokan arziki. Gidan na sa kuwa yana bakin titin Awolowo a anguwar ikoyi legas, kai da ganin gidan kaga alamar babban mutun wanda jama’a ke mutuntawa. Kofar gidan wani makeken kyaure ne sai kace gidan wani sarki, sa annan an bi ko ina an dabe da irin karamin bulo din nan na zamani abin gwanin ban sha’awa.

Idan ka wuce cikin falon gidan ko ina an sa darduma mai laushi kalar ruwan rawaya, kujerun da ke ciki irin na alfarma wadanda kalarsu ta dace da dardumar da kuma labulayen falon. Su kujerun zaman an jera su inda suka kewaye falon a tsakiyar wani dan taburin gilashi ne na alfarma saman sa ba komi sai kwalaben barasa iri-iri. Gefen teburin kuwa wani kofi ne mai kyau na azurfa wanda nan ne chukuma ke faman sa tokar sigari. A bangon falon kuwa an rataye hotuna masu kawatarwa, a bangon dake tsakanin kofar dakin maigida da kicin an rataye wani agogo mai kyau.

Chukuma shi kuwa yana zaune a babar kujera kushin doguwa ya dora kafar hagu bisa ta dama a inda yake karkada ta hagun sanyin eya kondishon ya ratsa shi yana murmushi. Chukuma yana son yayi wa Emeka magana amma ya lura yayi nisa a cikin kogon tunani, can ya kira sunan sa sai da ya kadu.

Chukuma yace. ‘’ kai lafiya ina faman kiran sunan ka amma baka ji ba har kana kaduwa haka kamar wanda aka bai wa tsoro?’’

‘’Kai ai ina tunanen yadda muka samu wannan hatsarin ne da mota kuma da yadda ka samu rauni ne. Saboda haka gaskiya kashe shi zamu yi, kaga sau biyu kenan muna kuskuren shi amma karo na uku sai mun kai shi lahira. Dalilin haka har garin su zamu je mu yanka shi kamar akuya’’.

Nan take chibuzo da ke zaune akan darduma yana faman shan barasa ya ce. ‘’ ai nima ina da wannan gurin a zuciya ta domin bai kamata a barshi hakanan ba’’. ‘’gaskiyar ka chibuzo’’. inji Emeka, wanda ke faman kashe sigarin sa a cikin kofan azurfa. ‘’ abin da yafi kenan mu kashe shi domin ya hana in samu wannan kwangilar mai tsoka. Domin na so da na samu wadannan kudin na ribar kwangilar sai in shiga dillancin koken wato hodar iblis domin a gaskiya ta fi kudi. Bayan haka kasan da cewar ya kai kara ta ga yansanda, lokacin da muka yi masa raunuka, sai da na kashe kudi makuddai kafin a kashe wannan bincike na neman mu da ake ruwa a jallo’’. Chibuzo yace. ‘’Emeka kara muryar rekodar nan domin kada wani yaji hirar da muke cikin masu zuwa gaida ni’’. Suna cikin haka sai wata yarinya ta shigo duk suka yi tsit kamar ruwa ya ci su. Can sai chibuzo yace. ‘’ Helen sannu da zuwa, kai na dade ban ganki ba ina fatar kina lafiya’’?

Helen ta kada baki tace. ‘’To chibuzo kasan kayi wuyar gani domin kwanakin nan baka zama gida, jiya nema na samu labarin hatsarin motar da ka samu wai tare da wasu abokanka har an kwantar da kai asibiti’’. Haka ne Helen ai tare da wadannan ne muka yi hatsarin. Kin ga wannan katon kasan sai da ya fashe Allah ya yi mishi arziki da yanzu ya mutu’’. Chukuma yana yi wa chibuzo shegantaka. Chibuzo yace. ‘’to ai kai da za a ce gawa ta ki rami har zaka ce da na mutu’’

Helen ki zauna mana ga brandi nan ki sha. Helen ta ce. ‘’kai ai yanzu na dai na shan giya domin lahanin ta. Amma don Allah kayi hankuri ban sani ba da na ziyarce ka a asibiti’’. A a ke kuma ai ba kome, kai chibuzo karka gaji kawo maltina kwalba uku. Yaya kannan ki. Ina fatar suna lafiya’’?

‘’Duk suna lafiya, kawata ta so ta zo tare da ni amma sai baban ta ya aike ta zuwa wani wuri’’. Emeka ya kalli chibuzo yace. Kai bawan Allah haka ake, ba za ka gaya mana ko wacece ita ba sai faman hira’’. Ayya kuyi hankuri ita ce kawar olu wande ke a anguwar obalande, ai tsammanin nake kun san yarinyar. Nan take chukuma ya mika mata hannunsa su ka gaisa. Bayan ta taya su hira kussan tsawon miti talatin sai ta nemi gafarar su cewar zata koma gida. Suka rakata zuwa kofar gidan ta hau tasi ta tafi.

Bayan sun dawo cikin gidan sai suka cigaba da hirar da suke kafin wannan yarinyar ta shigo. Suka yanke shawarar cewar abin da ya fi shine kawai su je har garin su Abubakar su kashe shi su kuma kwashe duk kayan dake gidan sa. Amma chibuzo ya bada shawarar cewar kafin su tafi garin ya fi kyau su je su samu mallam Abdullahi mai nama domin yayi musu misalin gidan shi a can. ‘’Emeka yace kai chibuzo baka da mantuwa, kasan cewar ni har na manta da mallam Abdullahi mai nama’’. Chibuzo yace. ‘’Haba Emeka! Ai bai kamata ka manta da irin wadannan mutanen ba. Katuna ranar idan da bamu ji yana hira da Abubakar ba da mu gane kome game da shi ba’’.

Bayan kwana bakwai chukuma ya samu sauki kwarai sai suka kama hayar zuwa federal palace hotel domin su ga mallam Abdullahi mai nama game da shirin su na samun cikakken labari game da Abubakar. Koda suka isa hotel din sun iske Abdullahi yana ta fama da gashin nama, ga mutane sun zagaye domin yadda yake gashin naman sa yasha banban da sauran masu gashi. Adalilin haka yasa yake da masaya da yawa. Gashi sayar da naman ya karbe shi, domin idan ka ganshi zaka yi tsammanin wani shahararen dan kasuwane. Yasa takalma bakake masu kyau suna faman kyalli duk da yake cikin dare ne, domin irin takalmin nan ne da ake sa tsumma kawai a share kura. Gashi dai ya fito gwanin shaawa idan ba ka iske shi yana sayar da nama ba, kayi tantamar cewar dan fawa ne.

‘’Malam ina shaawar yadda kake direshi ka fito cikakken bahaushe dan majalisa’’ inji wani bayarbe cikin masu sayen nama yake yabawa da Abdullahi ke sa sutura. ‘’Abdullahi ya yi murmushi yace. ‘’ nagode dan uwa sai dai ba dan majalisa bane mai sayar da nama ne’’. Duka mutanen da ke wurin su ka fashe da dariya. Abdullahi yana dago kansa sai suka yi ido biyu da chibuzo wanda ke faman dariya game da amsar Abdullahi. Abdullahi yace. Kai dan ibo daga ina kwana barkatai bani ganin ka da kai da abokan ka, ko lafiya? Mallam Abdullahi ai wallahi mun samu hatsarin mota ne kwanakin baya sai da a ka kwantar da chukuma a asibiti. Assha! Allah ya kare gaba chibuzu. Inji Abdullahi. Chibuzu ya kira Abdullahi gafe ya rada masa cewar yana son ya ganshi bayan mutane sun rage domin yana da wata matsala da yake son ya taimaka mishi akai. Abdullahi ba gardama yace Allah ya sa zai iya taimakawa.

Chibuzo ya sayi nama ya koma cikin hotel inda yan uwansa suke a zaune suna jiran. Yana isa sai Emeka ya tarbeshi yana tambaya cewa. ‘’yaya mutumina ko ka samu wani takamammen bayani yadda zamu same shi kuwa’’? kai kuwa emeka ka cika garaje! Ai kai irin wannan lamari sai da dubara kafin ka yi wata tambaya game da Abubakar, domin kaga sai ya fari tuhumar akwai wani abu a boye. ‘’To amma me ka keyi tuntuni a wurin?’’ inji emeka. Chukuma da ke fama da busar sigari yana saye da wani bakin tabarau ya sa hannu ya karbi kunshin nama daga chibuzo.

Bayan sun kare cin nama sai chibuzo ya tashi tsaye yana mika. Emeka kuwa sai kallon kwalbar giyar sa yake. Chukuma yace. ‘’kai lafiya ka tashi tsaye haka kamar wanda cinnaka ya ke cizo’’? lafiya kalau chukuma, ina son in koma in gani ko mutane sun raga domin yanzu karfe daya da rabi na dare. Sabodahaka ku jira ni ina zuwa. To Allah yasa muyi sa’a. Chibuzo kuwa ya yi sa domin mutum biyu kawai ya iske mace da wani saurayi. Bayan sun sayi naman sun tafi sai chibuzo ya matso kusa da mai naman.

Abdullahi yaya kasuwar yau? ‘’Kai dan ibo ai yau kasuwar sai da hamdalah’’. Chibuzo yace ‘gani na dawo game da taimakon da nace ina son ka taimaka mini dazu’’. Aff ai kai chibuzo kasan ni har na shafa da maganar. Amma menene ina fatar lafiya dai ko? Inji Abdullahi. Suna cikin maganar sai wani yazo sayen nama bayan an yanka masa ya tafi sai su ka cigaba.

‘’Abdullahi don Allah ina son kayi mini kwatancen gidan Alhaji abubakar ne domin zanje Gusau domin wata muhimmiyar kwangila da aka bani ta gyaran gidan ruwan garin. Kuma kaga tunda abokin mu ne ya kamata ace in sauka wurin sa domin ya nuna mini wurin da samo mini leburori masu aiki’’. Abdullahi yace gaskiyar ka kuwa, amma ban gane wani Abubakar kake nufi ba’’. Chibuzo yace haba kai kuwa wannan dan kwangila fari wanda ke sauka nan hotel din idan yazo nan legas. ‘’Oho na gane, amma ka ke cewa matsala gare ka, ai ni ina tsammanin wani abune mai wuya. Ai daka je gusau babu wanda bai san shi ba domin mutun ne mai kirki kwarai Allah ya hore masa mutane domin taimakon da yake’’. Jin haka chibuzo kamar ya take kan jariri domin jin dadi. Ya koma ya samu yan uwansa da suke dokin suji yadda alamarin ya kasance. Bayan ya zayyana musu yadda suka kaya da Abdullahi sai suka je wurin mota suka kama hanya zuwa gida.



Download 75,59 Kb.

Do'stlaringiz bilan baham:
1   2   3   4   5   6




Ma'lumotlar bazasi mualliflik huquqi bilan himoyalangan ©hozir.org 2024
ma'muriyatiga murojaat qiling

kiriting | ro'yxatdan o'tish
    Bosh sahifa
юртда тантана
Боғда битган
Бугун юртда
Эшитганлар жилманглар
Эшитмадим деманглар
битган бодомлар
Yangiariq tumani
qitish marakazi
Raqamli texnologiyalar
ilishida muhokamadan
tasdiqqa tavsiya
tavsiya etilgan
iqtisodiyot kafedrasi
steiermarkischen landesregierung
asarlaringizni yuboring
o'zingizning asarlaringizni
Iltimos faqat
faqat o'zingizning
steierm rkischen
landesregierung fachabteilung
rkischen landesregierung
hamshira loyihasi
loyihasi mavsum
faolyatining oqibatlari
asosiy adabiyotlar
fakulteti ahborot
ahborot havfsizligi
havfsizligi kafedrasi
fanidan bo’yicha
fakulteti iqtisodiyot
boshqaruv fakulteti
chiqarishda boshqaruv
ishlab chiqarishda
iqtisodiyot fakultet
multiservis tarmoqlari
fanidan asosiy
Uzbek fanidan
mavzulari potok
asosidagi multiservis
'aliyyil a'ziym
billahil 'aliyyil
illaa billahil
quvvata illaa
falah' deganida
Kompyuter savodxonligi
bo’yicha mustaqil
'alal falah'
Hayya 'alal
'alas soloh
Hayya 'alas
mavsum boyicha


yuklab olish