Tashin Farashi Ne Ya Sa Mu Shiga Yajin Aiki



Download 141,07 Kb.
bet1/6
Sana02.03.2017
Hajmi141,07 Kb.
#3696
  1   2   3   4   5   6
rahoto: Tashin Farashi Ne Ya Sa Mu Shiga Yajin Aiki —Shugaban Masu Burodi Na Kano

Daga Mustafa Ibrahim Tela, Kano

Kungiyar masu gidajen Burodi a Kano, karkashin Shugabancin Alhaji Lawan Mai Turare, wadanda kuma suka kammala yajin aiki na kwana uku a matsayin gargadi, sakamakon tashin gwauron zabi da kayan samar da burodi suka yi, ta bayyana cewa wadannan kaya da suke hada burodin da su, sun yi wani irin tashin farashi ne, wanda wasu ma sun nunka a kan yadda aka sansu.

Shugaban kungiyar, ya bayyana haka ne ga manema labarai a ofishinsu da ke Kano cikin makon da ya gabata, wanda ya ce wannan dalili ne ya sa suka shiga yajin aikin na gargadi. Inda ya ce akwai kuma dalili na biyu, “kuma mun lura samun wannan farashi na kayan yin burodi ya sa batagari a cikinmu sun fara sa sinadarin Potassium Bromated mai cutar da lafiyar dan Adam a cikin ayyukansu,” in ji shi.

Alhaji Mai Turare ya ci gaba da cewa, yanzu a wannan kungiya tasu suna da mambobi sama da 1,200, kuma kowane gidan burodi akalla mutane 50 ne ke samu aiki. Don haka akalla matasa sama da 60,000 na samun aiki a karkashin wannan kungiya ta masu burodi ta Kano.

Shi kuwa Alhaji Aminu Dan Hassan Hamdala ya bayyana cewa tun yana yaro bai san wata sana’a ba, sai harkar burodi, ita ce sana’ar mahaifinsa, ita ce sana’arsa shi kansa da ’ya’yansa, kuma suna da makarantar Nazare, Firamare, har da Sakandare da Jami’a a aikin burodi. A nan suke horar da matasa wannan sana’a, su fito su samu aikin da suke dogaro da kansu.

Ya ci gaba da cewa, kuma 1984 yana sayen Fulawa bahu 300 a kan N17 da Kwabo 42 a ko wane bahu, to amma yau ga abin da ta zama. Don haka suna neman dauki daga gwamnatocin tarayya da na jihohi, domin babu wata Hukuma, ko ma’aikata da ta kai su daukar ma’aikata.


rahoto: Jami’ar Jihar Kaduna Ta Samu Tallafin Motar Kashe Gobara

Daga Musa Danmahawayi, Kaduna

Ranar Juma’ar da ta gabata ne attijirin nan mai taimaka wa al’umma, Shugaban Kamfanin DIALOGUE LTD da ke Kaduna, Alhaji Mahdi Shahu ya mika makullen wata babbar motar kashe gobara ga Hukumomin Jami’ar jihar Kaduna a harabar Jami’’ar da ke kan titin Tafawa Barewa, Kaduna.

Da yake mika makullan motar, Alhaji Mahdi Shehu ya bayyana cewa ya yi tunanin bayar da wannan mota ce sakamakon wata gobara da Jami’ar ta yi a kwanakin baya, inda sai da motar kamfaninsa ta taso daga nisan duniya don ta agaza wajen kashe gorarar, wanda inda suna da tasu, ba sai an jira wasu ba, “don haka ne na ga ya kamata a taimaka masu da tasu ta kansu,” in ji shi.

Alhaji Mahdi, wanda ya yi suna wajen bayar da irin wannan tallafi, ya ci gaba da cewa ya bayar da wannan tallafi ne domin taimaka wa Jami’ar wajen magance asarar rayuka da dukiyar Malamai, dalibai da sauran kadarorin Jami’ar.

Ya ci gaba da cewa, duk a tsawon wannan lokaci, bai kamata ba a ce Jami’a kamar KASU ba ta da motar kashe gobara, wacce ya ce Jami’a ce mai dauke da al’umma da dukiya masu yawan gaske.

Don haka sai ya yi kira ga sauran masu hannu da shuni su ziyarci wannan jami’a domin duba irin gudumawar da za su bayar don inganta harkar Jami’ar, musamman abubuwan da za su ciyar da ita gaba, ta yadda za ta tsrre wa tsara. Wanda ya ce duk mutumin da ya san wannan Jami’a a shekaru goma da suka gabata, ya ga yadda take a yanzu, zai tabbatar da cewa an yi amfani da ilimi, da kwarewa wajen ingantata.

Da yake amsa tambayar manema labarai game da ko yana yin wadannan abubuwa ne don yana da burin siyasa a nan gaba kuwa, Alhaji Mahdi cewa ya yi shi ba ya siyasa, ba ya kuma sonta. Ya ce, “ba na son siyasaya, ba na yinta, ba kuma zan yi ba.”

Da yake jawabi wajen kabar wadannan maukullai, Shugaban Jami’ar, Farfesa Barnabas Kurid ya bayyana matukar jin dadinsu da godiya game da wannan tallafi da attajirin ya kawo masu. Wanda ya ce shi ne da kashin kansa ya yi shawarar tallafa masu, ba su ne suka meni ya tallafa masu ba.

Shugaban ya kuma bayyana cewa ba wai mota kawai Alhaji Mahdi ya ba su ba, ya hada masu har da ma’aikatan kashe gobarar da za su yi aiki da ita. Wanda ya ce zai taimaka masu wajen magance duk wa gobara da ka iya tashi a Jami’ar, duk da dai ba a fatan haka.

Daga nan sai Farfesa Kurid ya tabbatar wa da Alhaji Mahdi cewa za su ba wannan mota kulawa ta musamman don ganin tana cikin koshin lafiya a kowane lokaci.

Da yake amsa tambayar manema labarao game da yadda aka yi jami’ar ba ta da motar kashe gobara a duk wadannan shekarru da ta yi, Farfesan cewa ya yi gwamnatin jihar ta yi oda a kawo masu, kuma tana nan a hanya, za ta iso nan ba da jimawa ba.

Wakilinmu ya shaida mana cewa Alhaji Mahdi Shehu ya yi fice wajen bayar da taimako a bangarori da dama a karkashin wannan kamfani na DIALOGUE LTD, inda a ’yan kwanakin nan ma wannan kamfani ya kammala wani horar da dalibai masu shirin zana jawabawar JAMB, wanda aka gabatar da ofishin kamfanin da ke Rigasa, Kaduna, wanda yara matasa kimanin 10, 000 suka amfana.
rahoto:

rahoto:

Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola



Izala Ta Kaddamar Da Asusu A Abuja

Daga Lawal Umar Tilde, J

A ranakun Asabar da Lahadin makon da ya gabata ne kungiyar Izalatul Bid’ah Wa’ikamatus Sunnah (JIBWIS) ta kasa ta gudanar wani taron bude asusu na neman taimakon kudi don shirinta na raya ilimi, wanda ya gudana a filin wasa na kasa (Eagle Skuare) da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Cikin jawabin da ya gabatar, ta bakin wakilinsa, Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Alhaji Muhammad Musa Bello, Shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari ya yaba wa al’ummar kasar nan bisa hadin kai da goyon bayan da suke ba gwamatinsa. Inda kuma ya nuna farin cikinsa bisa addu’o’in neman zaman lafiya da inganta tsaro, da tattalin arzikin kasa da ’yan Nijeriya ke yi a fadin kasar nan. Ya yi fatan za su ci gaba da bayar da irin wannan gudumuwar.

Shugaba Buhari, ya kuma yaba bisa kokarin da kungiyar JIBWIS ke yi na tabbatar da ginin habakar cibiyar Islamiyyar. Ya kuma yaba wa Tsohon Ministan Abuja, Sanata Adamu Aliero bisa gudumuwar da ya bayar wajen mallaka wa kungiyar filin, da kuma Shugaban kwamitin ginin cibiyar, Dk. Aliyu Modibbo Umar, a kan tsayuwar dakan da yake yi don ganin an samu nasarar aiwatar da aikin.

Shi ma a nasa jawabin, Tsohon Gwamnan jihar Neja, Mu’azu Babangida Aliyu ya hori Shugabannin addini da su jefar da bambance-bambancen kungiyanci, su hada kansu waje guda don inganta karantarwar addinin musulunci a kasar nan. Ya ce, musulmai za su samu damar yi wa addinin musulunci aiki ne kawai idan suka zubar da bambancin kungiyanci, su hada hannayensu wajen raya addinin musulunci. Inda kuma ya mika gudumuwarsa ta Naira Miliyan daya, da na wadansu bayin Allah da suka bashi sako, ya mika wa kungiyar na sama da Naira Miliyan Hudu.

A Jawabinsa, Shugaban taro, Mai Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Sa‘ad Abubakar ya yaba wa Shugaban kungiyar, Shaikh Muhammad Sani Yahaya Jingir bisa kokarin da kungiyarsa ke yi na ilimantar da al’ummar kasar nan. Ya ce, hakan zai karfafa wa matasa gwiwar neman ilmin addini da na zamani.

Alhaji Sa’ad Abubakar, wanda Shugaban Sarakunan yankin babban birnin tarayya Abuja, Mai Martaba Adamu Yunusa ya wakilta, ya bukaci gwamnatin tarayya da jihohi su rika taimakawa wajen ilmantar da matasa don samun al’umma nagari da shugabannin da za su ja ragamar shugabancin kasar cikin nasara a nan gaba.

Tun da farko, Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar na kasa, Shaikh Muhamma Sani Yahaya Jingir, a jawabinsa, ya bayyana cewa kungiyar da aka kafa a shekara talatin da takwas da suka gabata, an kafata ne da manufar karantar da al’ummar musulmi ilmin addinin musulunci kamar yadda aka saukar wa ma’aiki, Muhammad .AW, kuma ta sami nasarar gina makarantun islamiyya da masallatai a ciki da wajen Nijeriya.

Daga Muhammad Maitela,Damaturu



Jigawa Ta Amince Da Karbo Bashin Naira Bilyan 2.2

Daga Munkaila T. Abdullah, Dutse

Majalisar zartarwar jihar Jigawa ta amince da karbar bashin zunzurutun kudi har kimanin sama da Naira bilyan biyu daga bankin samar da gidaje na gwamnatin tarayya domin gina gidaje dubu 1,330 a fadin jihar. Kwamishinan yada labarai, matasa, al’adu da wasanni, Alhaji Bala Ibrahim ne ya sanar da haka ga manema labarai jim kadan bayan kammala tattaunawar Majalisar cikin makon da ya gabata a gidan gwamnati da ke Dutse.

Ya ce, gwamnatin jihar za ta karbo wannan bashi ne ta hannun ma’aikatar kasa da raya birane, wanda za ta yi amfani da su wajen gina gidaje a yankunan Kananan Hukumomi 27, tare da yankunan masarautun jihar guda biyar. Alhaji Ibrahim ya kara da cewa, Majalisar ta amince da karbar filaye har hekta 224 a yankuna talatin da hudu domin gina wadannan gidaje.

Haka kuma ya ce, gwamnatin jihar ta ware kimanin Naira Milyan N2.2 domin biyan diyyar wadannan filaye, tare da ware sama da Naira Milyan guda domin amfani da su wajen kulawa da wannan ayyuka.
Fahimta Fuska: Sheikh Ibrahim Khalil

A aiko da tambaya ta wadannan imel: shafinfahimtafuska@yahoo.com ko nasirsgwangwazo@yahoo.com ko kuma sakon ‘tedt’ ta wannan lamba domin Malam ya amsa tambaya: 08039382831.



Malam, Ina so ka yi ma na bayani a kan rayuwar Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.

Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi daya ne daga cikin manyan malamai na Nijeriya da su ka bayar da gudunmawa a bangaren addini da bangaren rayuwa ta al’umma. Kuma malami ne wanda bai damu da duniya ba, kuma ba mai kwadayi ba, ba mai girman kai ba. Sannan kuma malami ne wanda ya ke da kishin al’umma da kishin kasa da kishin addini, wanda kuma ya ke yin abu iyaka gaskiyarsa, imaninsa, fahimtarsa da yardarsa. Kuma duk abinda ya yi imanin ya yarda cewa Allah Ya na so, to shi ya ke bi. Ya na da kiyaye dokoki da ka’idoji. Misali; kowacce kasa wajibi ne ya zama ta na aiki da mazhaba. Nijeriya mazhabarta Malikiyya ce. Don haka alkali dole ya yi shari’a da mazhabar Malikiyya. To, Malam Abubakar Gumi har ya mutu ba ya sabawa mazhabar Malikiyya a fatawa, saboda shi ya yi Grand Khadi. Don haka a matsayinsa na Grand Khadi abinda a ka san shi da shi, shi ne dole ya tsaya a mazhabar kasa; ba kamar ragowa wasu malamai ba wadanda su ba Grand Khadi ba ne kuma ba a ba su mukami na Grand Mufti ba. Marigayi Janar Murtala ya ba shi mukamin Grand Mufti; kodayake ba a kai ga rantsar da shi ba Murtala ya rasu. Don haka ba a kai ga rantsar da shi ba. To, amma hakan bai sa ya kauce daga bin ka’ida ta malamai ba a kasar nan. Don haka wani malami ne wanda ya kamata malamai sun yi koyi da shi. Kuma rayuwarsa cike ta ke da alheri da albarka, wanda za a yi fatan ta nasu ga ’ya’yansa da jikokinsa, kamar yadda wannan albarka ta nasu ga Musulmin Nijeriya har da ma Kiristoci da gwamnatocin Nijeriya da ma Nijeriya gabadaya. Dukkansu sun ci riba, kuma ya nuna wa mutane hakan a fili ko daga lokacin da a ka ba shi kyautar girmamawa ta Sarki Faisal a kan ya nuna kyakkyawan misali, inda ya nuna wa duniya cewa duk alherin da ta samu na kasarsa ne, ba nasa ne shi kadai ba, kamar yadda Sha’arawi shi ma ya nuna haka a kasarsa Misra. Don haka Malam Abubakar Gumi wani mutum ne wanda ya ke abin koyi ga malamai da kuma duk wani mutum wanda ya sami wani mukami a gwamnati ko a rayuwa, ta addini ce ko ba ta addini ba, ya na da kyau ya yi koyi da Malam Abubakar Mahmud Gumi, saboda a kowane bangare na rayuwa da ya sami dama, ya yi bakin kokarinsa. Don haka sai dai mu ce Allah Ya saka ma sa da alheri, Allah kuma Ya yarda da shi, Ya kuma albarkaci bayansa.



Malam, ni na kasance budurwa, amma duk wanda ya zo wajena da nufin aure ni, bayan an kwana biyu sai ya gudu. Na je gurin masu magani, sun ce wai bakin aljani ne ya ke bi na a ruhi; wai amma sai an zubar da jini, sannan zan rabu da shi. Ni kuma gaskiya Ina tsoron yin shirka. Don Allah Malam a taimake ni ko da wata addu’a ne da za ta iya taimaka mi ni.

To, karya su ke! Babu wani bakin aljani tare da ke, kuma kada ki yarda ki amince da wata magana irin wannan. Babu wannan maganar. Kawai abinda ya ke afkuwa shi ne, abubuwa guda biyu za a gaya mi ki. Na daya dai, mafi yawan lokaci, mutanen da su ke zuwa su kan zo ne da niyya iri-iri. Wasu su kan zo da niyyar za su yi auren, kuma a shirey su ke su yi, amma daga baya wasu dalilai su zama sun fi karfinsu; ko daga iyayensu ko daga canjin rayuwa ko wani dalili. Na biyu; a wasu lokuta, masu neman auren ba su kai su yi auren ba ko ba su da iko da za su iya yin auren, amma saboda su na sha’awar yin auren sai su ce za su yi. Don haka idan sun fara neman auren, sai dole ta sa su janye, don kuwa ba su da ikon yi, kamar rashin sana’ar kirki ko kuma muhalli ko ba su da wadata. Wasu lokuta kuma fajirci su ke sha’awar yi da budurwa. To, idan ya zamana fajircin bai samu ba, sai su gudu. Wasu lokuta kuma kawai so su ke yi su yi budurwa. Shikenan idan su ka fara tafiya kuma sai su hango wata budurwar. Sai su jefar da wannan su je su kama watan. Don haka ba maganar aljani ba ce. Abinda ya fi mi ki sauki shi ne, ki je ki sami iyayenki su yi mi ki addu’a, kuma ki dage zikirin Allah, kamar istigfari bayan sallar Asuba da istigfari bayan sallar La’asar. Ki nace da yawan wannan har Allah Ya kawo mi ki miji nagari.


Zamantakewa: Ina Amfanin Karfin-Gwiwa?

-Farfesa Salisu A. Yakasai

Sau da yawa, mutane kan dauki karfin-gwiwa a matsayin wani ma’auni da ake bukata a lokacin da ake cikin tsananin damuwa ko tashin hankali. Wato kamar dai a lokutan yaki ko kuma aukuwar wata annoba ko ibtila’i (jarrabawa). To amma kuma a gaskiya lamarin ya wuce haka, hasali ma batun ya wuce yadda muke tunani. Kai lamarin karfin-gwiwa wani alheri ne na yau da kullum. Ashe kenan karfin-gwiwa ba ma kawai daya ne daga cikin alhaire-alhaire ba, sai dai a ce alheri ne da dan’Adam yake tare da shi a muhalli da yanayin da ya dace. Abu ne mawuyaci ka aiwatar da wani abu na alheri ba tare da samun karfin-gwiwa ba, saboda mutumin da yake damfare da karfin-gwiwa ba ya da-na-sani a rayuwarsa. Wannan shi ne alkiblar tattaunawarmu ta yau.

A duk lokacin da na yi tunanin mutanen da karansu ya kai tsaiko a rayuwa (wato mutanen da karfin-gwiwarsu ya yi tasiri sosai a rayuwarsa), to mutum guda tilo da kan fado mani shi ne Wingston Churchill. Tun yana yaro karami ya shaki iskar samun daukaka a rayuwa. A lokacin da kuma yake makaranta, yakan amsa fatawoyin abokanan karatunsa game da makomar duniya. Ga misali, Churchill yakan ce yana hasashen duniya za ta samu kanta cikin canje-canje daban-daban da suka danganci tashin hankali da gwagwarmaya da kuma yake-yake. Ya ma taba fada karara cewa London za ta shiga mawuyacin hali, kuma za a kai mata farmaki, shi kuma zai samu daukaka a yunkurinsa na kare martabar London.

Wannan buri cikin gudummawar da zai bayar domin gina kansa da kuma al’ummarsa ba karami ba ne. Bayan faduwar kasashen turai a hannun ‘yan-nazi, sai da Ingila ta ci gashin-kai har na tsawon shekara biyu a karkashin jagorancin Churchill. A fili ya kalubalanci Hitler cikin goyon bayan al’ummarsa, duk kuwa da irin barazanar da suka fuskanta ta jefa bama-bamai da kuma mamaya. A shekarun alif dari tara da talatin kafin yaki, Ingila ba su da wata dabara face ta farantawa Hitler, amma kuma a fili Churchill ya kalubalanci hakan. A shekarun alif dari tara da arba’in kuwa, a lokacin da aka tunbuke shugaba Chumberain daga ofis, sai Ingila ta nemi wani jagora nagari domin ya maye gurbinsa. Mutumin da ya dace ya dace ya dare mulkin shi ne Halifad, to amma sanin cewa ba shi da karsashin da zai jagoranci Ingila a yaki sai ya hakura. Nan take sai aka kira Churchill domin cike gurbin.

To amma kuma don me aka zabo Churchill ya zamo shugaba? Shin don me mutane ke ganin ya dace da ya jagoranci kasar da take ganin karshenta ya zo? Ya dai riga ya samu karbuwa a tsawon shekaru da suka gabata, saboda haka an gwada karfin-gwiwarsa a lokuta daban-daban, kuma sakamakon hakan ne ya tabbatar da himma da kwazonsa da kuma jajircewarsa. Dangane da burin yin fice a rayuwa kuwa, tun a lokacin da yake dan makaranta ya kasance dan gwagarmaya da son samun nasara a dukkan abin da ya sa a gaba. Daga nan kuma sai ya shiga aikin soja, ya kuma sami nakaltar makamar aikin sosai da sosai. Babban burin da ya dade a birnin zuciyarsa shi ne zama dan siyasa kamar yadda mahaifinsa ya yi, to amma da farko burinsa shi ne ya yi fice a aikin soja. Hakan kuwa aka yi domin babu matsayin da bai hau ba a cikin kayan sarki.

Duk abin da zai aiwatar, yakan tunasar da kansa cewa “Na kuduri niyyar yin wannan aiki iyakar yina, idan ban samu nasara ba, to da alama ba zan kuma samun nasara a kowane aiki ba”. Wannan wata hikima ce ta kara samun kwarin-gwiwa a cikin ruhi da jiki duka. Ta hakan ne kuma cikin jajircewarsa a dukkan lamuran da ya sa gaba, ya yi samun nasara har karansa ya kai tsaiko. Wannan ne ma dalilin da ya sa yakan tunasar da kansa cewa “Na fi damuwa da burin yin suna cikin kwarin-gwiwa fiye da komai a duniya”.

Daga baya ne ya bar aikin soja kuma ya shiga kogin siyasa. A nan din ma dai, haka ya yi ta fadi-tashi (yau nasara kuma gobe faduwa), har dai lokacin da ya zamo shugaba a shekara ta alif dari tara da arba’in. A nan ne kuma mutane suka san cewa ba su yi zaben tumun-dare ba. Wato suna da yakini dangane da irin himma da kwazo da kuma jajircewarsa. Hasali ma, rayuwarsa kacokan ya salladar da ita ga burin da ke cikin zuciyarsa, kuma karsashinsa ya tabbatar da nasararsa.

Gaskiyar maganar ita ce, daga na gaba ake gane zurfin ruwa, wato dai akwai abubuwa da yawa na izina da za mu amfana da su daga tarihin rayuwar wannan bawan Allah. A tattaunawarmu ta gaba, za mu yi kokarin gano dalilan da suka mutum kamar ni da kai da ita da su zamu bukaci karfin-gwiwa!



08035073537, 08154615357 (Tes kawai) Syakasai2002@yahoo.com
Masu Tsauwalawa Don Cin Riba Sun Fada Kwata, A Yayin Da Darajar Naira Ta Karu

Taskirar Babban Banki

Tare Da Abdulrazak Yahuza Jere

Akwai karfafan alamomin da ke nuna cewa kokarin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ke yi na daidaita darajar naira ya fara haifar da kyakkyawan sakamakon da ake tsammani.

A makon da ya gabata, wani jami’in CBN ya nunar da cewa matakan da bankin ya dauka ya tarnake kasuwar canji tare da gasa wa masu boye kudade sai sun yi tsada su fitar su sayar aya a hannu.

Dama CBN ya jaddada cewa masu tsauwalawa don cin riba ne suka haddasa tashin farashin canjin daga waccan makon da ya gabata wanda ya dankwafar da naira zuwa kusan naira 400 a kan ko wace dala.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya soki ‘yan cin riban wanda suka hada baki da ‘yan canji don su kassara kokarin da bankin yake yi na inganta darajar naira, kana ya yi gargadin cewa irin wadannan mutanen za su gamu da gamonsu idan kasuwa ta yi halinta. A makon da ya gabata, ya bayyana cewa darajar naira ta fadi ce ba domin bukatar aini da ake da ita a kan kudaden waje ba, sai don bukatar son rai ta ‘yan cin riba, wadda galibi suka tafka asara saboda karuwar darajar naira cikin hanzari.

A farkon makon da ya gabata, darajar naira da ta kasance 367 kan ko wace dala ta karu inda dalar ta ragu zuwa 350 a ranar Talata, sannan ta koma zuwa 305 a ranar Laraba. An samu gibi sosai tsakanin farashin sayen dalar da na sayarwa a ranar Laraba. Masu canjin kudi sun rika sayen dala a hannun mutane a kan naira 270 su kuma suna sayarwa akalla naira 305.

Wani dan kasuwar canji ya yi bayanin cewa an samu babban gibi tsakanin farashin da ake saye da wanda ake sayarwa ne saboda kokarin da ‘yan canjin ke yi na rage asara.

Ya ce “Mutane sun sayi dalar a kan farashin naira 370 amma kuma sai ga shi suna ta tafka asara. Sai dai da aka hada waccan dalar mai tsada da wacce aka saya a kan naira 270, sannan aka daidaita farashin sayarwa ya koma naira 320. Don haka har yanzu suna faduwar naira 15 a kan ko wace dala idan aka sayar a kan naira 305.

Koda yake dalar ta kara tashi zuwa naira 350 da maraicen ranar Alhamis, naira ta kara samun tagomashi inda a karshen mako dala ta fado zuwa naira 315.

Da suke lissafa asarar da suka yi, masu sayar da dala da dama sun amsa cewa sun sayi dala a kan naira 380 tare da sa ran cewa za su sayar a kan naira 400, kawai sai reshe ya juye da mujiya.

Masu fashin baki kan harkokin masana’antu sun ce zai yiwu matakan da babban bankin ya dauka a baya-bayan nan ne suka sa aka samu wannan ci gaban. Daya daga ciki shi ne matakin wallafa dukkan hada-hadar sayar da kudaden na waje da ta gudana a tsakanin bankuna domin tabbatar da gaskiya da rikon amana. Mataki na biyu shi ne babban bankin ya tsaftace ayyukansa wanda ya sa aka samu saukin karancin kudi a bankuna da aka kitsa cewa za a samu a wancan makon na sama. An ce matakin ya sanya naira ta dan yi likimo.

Har ila yau, akwai matakin da CBN ya dauka na ci gaba da sayar da dala ga masu karatu da zuwa jinya a waje wanda a baya aka yada cewa an hana sayar musu a bankuna, abin da ya haifar da tsoro da fargaba ga masu wadannan bukatun. Wani dalili da masu lura da harkokin da ke kai-komo a kasuwa suka bayyana da ya kara wa naira daraja shi ne tsadar da kayan da ake shigo da su daga waje suka yi da kuma raguwar cinikinsu, kasancewar ‘Yan Nijeriya da dama sun koma wa amfani da kayan da ake sarrafawa a gida. An ce wannan ya kara haifar da faduwar dala. Wakazalika, kafe kai da fata da gwamnatin tarayya ta yi na kin karya darajar naira duk da kahon zukar da aka kafa mata daga sassa daban-daban ciki har da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), shi ma ya agaza wa farfadowar darajar naira.

A cewar wata majiya daga babban bankin “manufar CBN ita ce ya tabbatar da cewa banbancin da za a samu a tsakanin farashin dala na gwamnati da na kasuwannin bayan fage bai zarce naira 3 ba, don haka muna son ganin farashin dala ya koma naira 200 a kasuwannin bayan fagen saboda za a ci gaba da kokarin rage wa naira nauyin da ke kanta. CBN yana da karfin da zai yi hakan sannan zai dauki wasu matakai na kudi yayin kasafta jarin da za a kebe wa manufofin kudi na gwamnatin tarayya don karfafa kin karya darajar naira. Hukuncin da gwamnatin tarayya ta yanke a yanzu shi ne ba za ta rage darajar kudin ba. Kauyanci ne wani ya kai dala gida ya boye yana jira ta kara tsada ya fitar, saboda za mu iya tabbatar muku da cewa daga yanzu darajar naira ta dinga karuwa kenan.”

Zuwa yanzu, a kokarin da CBN yake yi na shawo kan matsin da ake samu wajen kawo kaya, ya kebe sama da dala bilyan 11.7 domin tallafa wa sashen aikin gona, da kanana da matsakaitan masana’antu, da sarrafa kaya a gida da sauran su. Wannan ya rage cinikin kasuwannin bayan fage daga wajen masu sayayya da dalar kai tsaye tare da tilasta wa sauran masu amfani da dalar kaurace musu, abin da ya haddasa cunkoson dala a kasuwannin na bayan fage.

An lura cewa kayan da ake sarrafawa a gida tuni suka maye gurbin galibin kayan da ake shigo da su daga waje da ke lankume kudaden na waje da muke da su inda ake tsumin abin da ake da shi a hannu da kuma raguwar bukatar dala wadda ita ke kara karya darajar naira. Wannan na zuwa ne daidai lokacin da CBN ya ba da umurnin wallafa yadda aka tafiyar da canjin kudaden waje ga masu amfani da su kai tsaye. Tun a lokutan baya wannan ya sanya bangarorin da ke habaka tattalin arziki da wadanda ke bukatar biyan kudin makaranta da na asibiti a waje suka rika samun canjin kudin a farashin gwamnati.

Masu fashin baki kan harkokin masana’antu sun kuma bayyana lamarin a matsayin wani abu da za a yiwa masu kamfanonin sarrafa kaya a cikin gida albishir da cewa kakarsu ta yanke saka. Masu kamfanonin sun nunar da cewa manufar da aka bullo da ita a kan kudaden na waje ta yi tasirin da ya rubanya ayyukansu saboda karuwar bukatar kayan da suke sarrafawa a kasuwa.

Masu fashin bakin suka ce “Tun daga lokacin da CBN ya bullo da manufar takaita amfani da kudaden waje, cikin jin dadi ayyukan kamfanoni na gida suka karu daga kashi 50 zuwa 70 a cikin 100. Wannan ya kara ba su damar fitar da kaya masu yawa zuwa waje wanda ake sa rai ya taimaka wa Nijeriya wajen samun karin kudaden na waje.”

Har ila yau, masu fashin bakin sun bayyana cewa manufar ta kuma taimaka wa masu kamfanoni na gida fahimtar bukatar gaggawa da ake da ita ta fadada ayyukan kamfanonin nasu saboda rububin kayansu da ake yi. Bisa yadda farashin mai ke farfadowa sannu a hankali da kuma karuwar kudin asusun ajiyar kasa na waje, ana sa rai martabar naira ta dawo. A makon da ya gabata, asusun ajiyar kasa na waje ya karu daga dala bilyan 27.789 zuwa dala bilyan 27.807, ma’ana an samu karin dala milyan 18. Har ila yau, kamar yadda bayanan da suka fito daga CBN suka nunar, farashin mai yana kaiwa wuraren dala bilyan 32.89.

Ko Kun San?

Asalin Sunan Birnin Tokyo

Ko kun san cewa asalin sunan birnin Tokyo da ke cikin kasar Japan shi ne - Edo?

Rayuwar Rikakken Giwa

An bayyana cewa rikakken giwa ba ya isa tsalle sai dai rausaya. Kuma ba ya iya cin wani abu a bainar jama’a sai bayan saura sun yi

Zuciyar Dan Adam


Masana sun kiyasta zuciyar lafiyayyen dan adam na bugawa sau dubu dari a kowace rana. Har ila yau, tana bugawa sau milyan 35 a shekara. Saboda haka, cikakken dan adam din da ya samu kyakkyawar rayuwa, zuciyarsa za ta iya bugawa sau bilyan biyu da milyan dari biyar, kafin ya mutu.

Wanne Jinsin Sauro Ke Cizo?


Masana sun tafi a kan cewa a cikin jinsin sauro, mace ce kadai ke cizon dan adam. Ta kan yi amfani da jini ne kawai don ta kyankyashe kwanta. A yayin da namiji kuwa ke shan furanni don rayuwa.
Domin Tuntuba: 08033225331

Download 141,07 Kb.

Do'stlaringiz bilan baham:
  1   2   3   4   5   6




Ma'lumotlar bazasi mualliflik huquqi bilan himoyalangan ©hozir.org 2024
ma'muriyatiga murojaat qiling

kiriting | ro'yxatdan o'tish
    Bosh sahifa
юртда тантана
Боғда битган
Бугун юртда
Эшитганлар жилманглар
Эшитмадим деманглар
битган бодомлар
Yangiariq tumani
qitish marakazi
Raqamli texnologiyalar
ilishida muhokamadan
tasdiqqa tavsiya
tavsiya etilgan
iqtisodiyot kafedrasi
steiermarkischen landesregierung
asarlaringizni yuboring
o'zingizning asarlaringizni
Iltimos faqat
faqat o'zingizning
steierm rkischen
landesregierung fachabteilung
rkischen landesregierung
hamshira loyihasi
loyihasi mavsum
faolyatining oqibatlari
asosiy adabiyotlar
fakulteti ahborot
ahborot havfsizligi
havfsizligi kafedrasi
fanidan bo’yicha
fakulteti iqtisodiyot
boshqaruv fakulteti
chiqarishda boshqaruv
ishlab chiqarishda
iqtisodiyot fakultet
multiservis tarmoqlari
fanidan asosiy
Uzbek fanidan
mavzulari potok
asosidagi multiservis
'aliyyil a'ziym
billahil 'aliyyil
illaa billahil
quvvata illaa
falah' deganida
Kompyuter savodxonligi
bo’yicha mustaqil
'alal falah'
Hayya 'alal
'alas soloh
Hayya 'alas
mavsum boyicha


yuklab olish