FARIN DOKI
Zayyad yace. ‘’Inna sa’a, lokacin komawa makaranta ya matso kusa domin yanzu sauran kwana bakwai’’. Inna sa’a tace. Ai kuwa hakanan ne d’annan ai rannan kafita kawun ka Ibrahim ya zo na bashi takardar makaranta ka yace baturen makaranta ya rubuto da a saya maka littafan karatu da rubutu kafin ranar komawa hudu ga wata amma baka sheda mini ba. Kila tsammanin kake kwaleji kamar makarantar firamare ce?’’ zayyad ya amsa cewa. A aha inna sa’a, ai bani son in wahalar da ke ne, shi ya sa ban sheda miki ba domin akwai sauran litattafan da kika saya mini a wancan hutun ban bata su ba,sai dai na karatu ne bani da su ’’.
Zayyad cikin ajin su duka shi ke yi musu na daya, domin Allah ya bashi basira da hazaka kwarai da gaske fiye da shekarun sa, shi yasa yake da farin jini ga dalibai da malaman makarantar. Kuma abin mamaki shine duka makarantar babu mai dogon hakuri da juriya irin wanda Allah ya hore masa. Amma abu daya dake ci masa tuwo a kwarya shine talauci domin tun lokacin da aka kashe masa uba babu abin da ya mallaka sai kangon gida.
‘’inna kinga shi yasa lokacin da nake aji uku na shawarce ki da in sayar da gidan baba domin ki samu jari mai tsoka ni kuma in samu isassun kudin da zan shiga makarantar jamia kin ce baki yarda ba’’. Kakar zayyad ta ce. ‘’kai dan yaron nan in banda rashin hankali ranar da ka girma ka zama wani abu a nan garin, wane gida zaka nuna kace ga gidan ubanka. In banda shegantaka kai da ke aji hudu yanzu kana maganar jamia’’. Habawa inna sa’a ai yafi kyau mutum ya kudurta abinda yake so ya zama tunda wuri, hala ma dai baki ji maganar da a ke cewa yaro nemi kudi tun abin saye bai zo ba? Yaro ina zan san wannan maganar kuwa. Yanzu dai ba zan bari ka sayar da wannan gidan ba sai dai ka sa yan haya amintattu. Zayyad yace. To amma ke kuwa inna, ai wanda ke ciki yanzu baya da kirki domin ke da kanki ke cewar ya kan share wajen wata goma bai biya ko sisi ba. Kuma duka yayansa sun zane gida da rubuce-rubuce kamar gidan arna. Amma gwanda kika sheda mini niyar ki, kinga kafin in koma makaranta sai in sheda mishi da ya kwashe komatsan sa ya bamu gida. Dama ance gari da yawa maye ba ya ci kansa ba, mutane da yawa suna neman wurin haya kamar suyi ihu, amma shi ya samu yana wannan rashin hankali. To wallahi idan wani gidan ne ko kuwa ince idan ba don ya samu irin ki ba da sai na kai shi kotun ‘yan haya dama naji ance alkalin irin su yake nema, wadanda ke mayar da gidan wani nasu’’.
Kakar zayyad ta ce da shi. ‘’Zayyad ai hakuri zaka yi dama kawun ka ke kula da gidan babu ruwan ka da korar sa. Bari dai in kwashi abinci kaga yana batun ya kone’’. Zayyad ya leka tukunya ya na faman tawayen cewar shi ba zai ci tuwon gero domin ya gaji da cin shi hakanan. Kakar ta lurad da shi da cewar yayi hankuri idan gari ya waya tuwon shinkafa zata rika dafa mishi har ya koma makaranta. ‘’zayyad kasan abin da nake so da kai shine kana da hankuri kuma ka san ance mai hankuri yakan dafa dutse, kuma hankuri abin manzon Allah ne. Ka tuna fa Allah ne ya samu cikin wannan halin, yanzu ba irin lokacin da ubanka ke da rai ne ba, Allah ya jikan su’’. Inna sa’a na fadan haka nan take sai ta fara rusa kuka shima zayyad ya kama mata. A haka dai ta dawo tana rarrashin zayyad tana fadin. ‘’haba baban mai gida sha kurumin ka bar kuka Allah zaya fidda mu wannan halin wata rana.
Bayan hankalin ta ya kwanta ta kwashe tuwo, ta yo kiran zayyad dake garka da yazo ya dauki na sa. Ya zauna yana faman cin abinci yana kada kansa sai yace. Inna yau miyar nan taki tafi kowace dadi kamar miyar naman zabo’’. Kai zayyad ai daddadawa ce kawai sai naman kaza da nayi miya da su. Wace kaza kenan? Kazar da kace tana yawan damuwar ka da kyarkyara safe. Lallai kaji dadin abincin nan nawa, gashi har kana faman santi har da kada kafafuwa kamar wani maigida. To inna ai kema kinsan maigida nake.
Inna sa’a kin kuwa san har da nace na gaji da cin tuwon geron hakanan. Kin ga idan na koma makaranta jibi, duka zan rasa irin wadannan kayan dadi domin a makaranta idan aka yi mana miyar kuka kamar an kwaba lalle. Kisan irin lallen nan da kika kwaba ranar nan, ai in gaya miki miyar babu dadi ba dadadawa ai ance mahaukaci yaci kashi’’. Inna sa’a tace kai zayyad kaji tsoron Allah, ku da ake yiwa miyar dage-dage mai dadi a makaranta. Wai! Inna sa’a domin ban gaya miki yadda tuwon yake ba, shi kunu idan aka yi mana shi sai dai muyi ta faman bacci a cikin aji. Ke dai inna ayi ta shaani wai an cuci bakauye.
Kaga lokacin babanka Allah ya jikansa, yana makaranta su har da kaji a ke yanke musu kuma a basu kifin gwangwani har yakan zo nan gidan da sabulu har da bargo wallahi sai kace wadanda da ke gidan iyayensu. Zayyad yace. Kai lalle garin dadi yana nesa wai ungulu ta leka shadda’’. Kai wannan labari naka idan nabiye maka babu ranar da zamu tashi nan, je ka wanke hannun ka in aike ka gidan su murja, ka karbo mini kudin da ta ranta gareni’’. To inna kada kiga na dade domin zan biya in ga mustafa game da tafiyar mu makaranta’’. ‘’Kai lafiya naga mustafa ya daina zuwa nan gidan wajenka, jiya nake son in tambaye ka ko kunyi fada ne domin yaron da kan zo nan gidan fiye da maya hudu a yini, gashi har ya share kusan bakwai daya....’’ zayyad yace. kai inna ban karbi nunfashin ki ba na manta in sheda miki cewar yayi yar rashin lafiya ne. Zazzabin maleriya ya kamashi’’. To zayyad sauro ne a garin gashi kamar kasa’’.
Bayan zayyad ya sha ruwa sai yayi wanka ya ci kwalliya sai kama hanyar zuwa wajen baban abokinsa mustapha, zayyad dai yaron ne dogo siriri gashi kuma kyakkyawa hanci har baka ga iya magana kamar dan siyasa domin ko kana cikin bacin rai ya zo wuri idan ka saurare shi to kuwa ya saka murmushi. Gashi kuma akwai iya ba da dariya ga jama’a, shi yasa Allah ya hore masa farin jini ga yara da manya. saboda haka shugaban makarantar su yayi shawara da sauran malamai aka yi wa zayyad shugaban dalibai tun yana aji hudu, kuma wannan bai kawo tashin hakali daga manyan daliban makarantar ba wandada ke aji biyar da aji shida. A lokutta da dama daliban makarantar sukan so suyi tawaye game da dakunan kwana ko abinci, amma da yayi musu jawabi mai sosa rai sai su lura da abin da yake fahimtashesu sai su fasa nan take. Shi kuma nauyi sa ne nan take ya samu shugabannin makarantar ya mika koken su kuma da gaggawa a share musu hawayen su, ganin wannan hali na sa yasa sauran dalibai sukan yi mishi kirari da cewar zayyad, yaro mai halin manya.
Zayyad yana isa kofar gidan su murja, domin karbo sakon da kakar sa ta aike shi, sai ya hango abokin sa mustapha, yana tafe da sauri da ganin mustapha ya matso kusa dashi yana neman ya wuce sai ya jawo wuyan rigar mustapha, wanda ya juyo a fusace da ganin zayyad sai yace. ‘’Wallahi kayi arziki, da niyar in dankara maka kulli nake domin a zato na ina tsammanin barayin nan ne da nake jin labarinsu’’. Zayyad yace.’’ Ai na hango ka tun daga nesa amma hankalin ka baya tare da kai kamar wanda yayo gudun bashi shi yasa na finciko wuyan rigar ka. To ai nima na gan ka amma ban yi tsammanin kai ne ba domin irin wannan shiga taka kamar wani baban dan kasuwa, kodan ance yaro mai halin manya. Kai amma wallahi babbar rigan nan taka tayi maka kyau kwarai ji yadda ka cika fuska, wanda bai sanka ba sai yayi tsammanin wani attajiri ne’’. Kai mustapha! Banda kara gishiri kai dai kana zolayata ka ke domin ka shammace ni’.’ Mustapha yace. ‘’kai malam ba haka bane ai gaskiya a fade ta, amma ina zaka je ne haka?’’ zayyad yace. Wallahi nan gidan zan shiga in karbo sako daga nan wurin ka dama zan je domin har na gayawa inna sa’a, har ta tambaye ni game da kai cewar yau bakwai daya rabon ka da gidan mu domin na manta ban gayamata game da rashin lafiyar ka ba’’. Mustapha yace kai nayi murnar da ka manta domin da tana iya cewar sai ta zo ganin yadda na kara ji, kuma ga wurin da nisa’’.
‘’Amma gaskiya kasamu sauki ba kamar ranar da na zo ganin ka ba. Bari in karbi sako sai ka rakani gidan kanwar uwata in yi mata bankwani domin komawa makarantar mu jibi’’. ‘’ wallahi nima maganar da ke cikin zuciya ta kenan game da komawa makaranta mu domin yakamata mu koma da wuri kada a samu cikin ma su lattin zuwa makaranta’’.
Bayan zayyad ya karbi sako, sai suka kama hanyar gidan su gwaggon sa suna ta faman zancen duniya. Hanyar da suka biyo kowa a kwai kwatar da ta ratso hanyar sai mutum ya tattaka wasu duwatsu da aka ajeye domin a tsallaka, kuma a kusa da wurin ne gidan aminin baban zayyad yake wato Alhaji sani. Gidan sani yana cikin gidajen da ake alfahari da su a duka garin, gashi gidan sama ne mai hawa daya mai fenti fari ko ina gidan an shuka furannin kallo abin gwanin sha’awa. Tagogin gidan duka na gilashine irin wadanda ake turawa gafe sai su bude. A kofar gidan kuwa akwai wani farin doki kosasshe an daure shi a gidin bishiyar mangwaro wadda ke bada inuwa mai sanyi ga tsuntsaye suna faman kuka iri-iri. Kusa da dokin wasu ‘yanmata ne su biyu suna tsaye suna labari. Daya daga cikin yanmatan tana saye da bakar abaya gata doguwa ce madaidaiciya sannan kuma gata fara, kwayar idanunta farare kamar madara ga gashin kai kamar aljanar ruwa domin bata saye da adiko ga kanta. Hancin wannan yarinya har baka gata da hakora farare da kuma wushirya da ya karamata kyawo. Tana wasa da gyale da ke daure a dan stukaken kwankwason ta, a hannun kuwa tana daure da agogon zinari kai da ganin wannan yarinyar kasan yar mai halice. Da ganin wannan yarinyar dai kasan ta yo rikiya ne kofar gida domin ta raka daya yarinyar da ke saye da atamfa.
Zayyad da abokin sa suna tafe suna hira, sai mustapha ya ke gayawa zayyad cewar. ‘’wannan gidan yana da kyau kai da gani kasan akwai kudi a nan, ko dai irin maaikacin bankin nan ne’’? af kai baka san Alhaji sani ba? ‘’Ai inna tana gaya mini cewar babban abokin baba na ne amma daga rasuwar uba na yayi kamar bai san mu ba. Ka manta wanda nake gaya maka cewar abokin baba na wanda ya dauki nauyin bukin haihuwata amma yanzu ya yada mu’’. To to ai kuwa na tuna a makaranta kana bani labarin har ina mamaki’’. Inji mustapha yana fada yana rike da baki domin ta’ajibin wannan gidan da ya gani, sai yace. ‘’to amma zayyad ka taba zuwa wurin shi kuwa’’? to kai mustapha ai idan kaga mutum yana jin warin mutane sai kayi nesa da shi yanzu haka idan ya ganni zai ce kai zayyad ne yaya inna tana lafiya shikenan fa babu kari. Amma akwai ranar da matar shi ta taba aika wa da inzo, da na je kuma aka yi kamar ba a san inda na fito ba, abin ya kona mini rai na. Kasan abin mamaki wallahi ake gaya mini cewar wallahi baba na ne ya sa shi a hanyar kwangila har ya gawurta, wasu ma sun ce ai yaron sane. Domin a Alhaji sani na Abubakar ake kiran sa’’. ‘’A a shine ai kuwa na san wannan sunan, amma yaushe ya gina wannan gidan? Mustapha ance duka bai fi wata shida da gina shi ba yanzu ma iyakar sa wata daya da rabi da tarewa cikin gidan. Kai mustapha don Allah dobi yadda dokin can ya koshi har yana.........
‘’Ashsha zayyad hala dai baka lura da wanna kwatar bane’’? wallahi mustapha ai hankali na ya dauku ga dokin can ne, kaga dole na katse maganar da naka domin kawai sai naji kafa ta cabal cikin kwata. Kai dubi duka takalma na sum baci oo! Kai har da wando na ma duka ya kwaso kwata abin gwanin kazanta’’. Suna cikin wannan halin ashe yanmatan nan dariyar su suke suna tsammani ko wurin kallon sune suka fada kwatami. Mustapha yace ke dariyar me kike je ki kawo mishi ruwa ya wanke jikansa, zayyad kaga yarinyar nan yarfara akwai dariyar keta gare ta dobi yadda take faman kyalkyatawa’’. Zayyad yace. ‘’Don Allah yanmata a taimaka mana da ruwa in wanke jiki’’.
Yar fara yarin yar dake dariyar su ta je famfon da ke bakin garejin motar babanta ta debo ruwa a bokiti sai tayi kiran kawarta. ‘’hafsatu zo ki kai musu ruwan nan domin ina jin kunyar wanda ya fada kwata dinnan’’. Hafsatu tace ke kaji abin mamaki bayan kin gama dariyar shi saannan ki ce wai kina jin kunyar shi, kodai kin son shi ne ya kwanta miki’’? ke don Allah rufa mini asiri kada ki kai ni inda ‘yan kuda ke salati, jakkai na amada mutane na lailaha-illallah. Ni dai gaskiya yayi kama da wani yaro da babata ta aika ya zo gidan mu lokacin muna tsohon gida, amma kuma wannan kamar yanzu yafi da kyau’’. ‘’To kawo in kai mishi naji kamar dayan yana kiran shi zayyanu’’. Ta tattaka ta je wurin da su ke tsaye tace. ‘’to zayyanu ga ruwan ka wanke jikin ka kaji’’. Mustapha yace wa yarinyar. ‘’ke wa ya gaya miki cewar sunan sa zayyanu? Zayyad ne sunan shi, kin ji ko yammata’’. Zayyad ya karbi bokiti ya wanke kwatar da ta bata mishi jiki sai kuma suka yi godiya suka kama hanyar zuwa gidan gwaggon shi.
‘’Wallahi hafsatu, ni dai ban taba ganin yaron da ya jefa ni cikin kogin tunani irin kamar shi ba’’!. ‘’Aha, aha.. aha.. nikan nasan ruwa basu tsami banza da na ce son shi kike me ki ka ce’’? ke ni dai hafsat bana iya kananan maganganun ki, ki ta shi in raka ki kada ki dade gashi magariba tayi karato’’. Bayan ta raka hafsat ta dawo cikin gida tana taimakon mai yi musu girki zuba miya ga abinci da karewa sai ta shirya domin tayi wanka tana daure da zani a kirjin ta domin bata saye da riga sai tawul din wanka da ta yafa a kanta. ‘’ke nafisa ina ki ka je ki dade tun dazu’’. Nafisa ta juya ta amsa wa babar ta cewa. Ai baba naje rakiyar hafsat ne kofar gida’’. To shi zaya sa ki je ki zauna kuma bayan kisan nace zan aike ki, kuna can kuna faman ba’a da ‘yan samarin ku ai ina ganin ku ta tagar dakin malam’’. ‘’A aha baba ba samarin mu bane wani yaro ne da ake kira zayyad kuma ina tsammanin nasan shi domin ya taba zuwa wurinki a tsohon gida’’. Aa nafisa, ko dai zayyad na gidan Abubakar ne idan kika kara ganin shi kice ina neman shi kinji ko. Idan kin kare wanka ki kayi sallah ina son ki je gidan malam musa ki karbo atamfar da aka saya domin bukin binta ya tashi jibi za a daura aure’’.
GASAR CIN KOFI
Bayan su zayyad sun koma makaranta da wata daya sai maikatar ilimi ta jaha a karkashin jagorancin kwamishinan ilimi ta shirya gasar wasa kwakwalwa a tsakanin makarantun jihar domin cin kofin shugaban kasa. Wannan gasar dai manufar ta shine domin a tsamo daliban da ke da hazaka ta fanin kimiya domin a samu cigaba ga fanin ilimin kimiya a jiha. Zayyad dai yana daya daga cikin dalibai hudu da aka zaba su wakilci makarantar su. Saboda haka an gayyaci makarantun da suka zama na uku zuwa nabiyar domin su gane wa idon su yadda gasar zata kaya a ga wanda zaya dauki kofin shugaban kasa.
Cikin makarantun da aka gayyata akwai kwalejin kimiya da fasaha ta gimbiya maryam, ita ce kuma ta zo ta hudu a gasar kuma a wannan makarantar ne Nafisa sani take. Duka makarantun da aka gayyata sun zazzauna sun jiran a fara gasa tsakanin makarantar da zayyad ke wakilta da makarantar kwalejin kimiya da fasaha ta gwammanatin tarayya. Bayan dalibai sun zauna da sauran manyan baki da aka gayyata can sai duriyar jiniyar motar gwamna ka ke ji, cikin minta daya sai ga motar da tawagar sa sun iso wurin gasar. Da isowar gwamna ya gaisa da manyan sarakunan gargajiya da sauran makarban gwamnati sai aka busa take kasa duka wanda ke cikin wannan baban dakin taro ya tashi tsaye domin girmamawa. Bayan an kare taken kasa sai aka bude taro da addua daga baban limamin gari sai gwamna ya fara jawabin sa kamar haka.
‘’Assalamu alaikum, sarakunan gargajiya, kwamishinoni, mayan daraktoci, malaman makaranta da sauran mayan baki maza da mata. Ina mai matukar farin cikin yi muku maraba da zuwa ganin wannan gasa domin kara hazaka tsakanin yanmakaranta da kuma cusa kauna ga daliban mu domin shaawar ilimin kimiya da fasaha. Wannan gasa itace ta farko a wannan jihar kai har ma a wannan kasar baki daya.
Abin alfahari ne ga kowace kasa mai tasowa ta ga ta samar da masana ilimin kimiya da fasaha domin samun ci gaban wannan kasar. Duka wadannan mayan kasashe da muka ji irin su Amurka, Ingila, rasha da faransa ta irin haka ne suka fara har suka zama abin da suke a yau. Saboda haka naga ya kamata muma mu fara domin mu sami masana akan wadannan fannoni, idan haka ta samu kunga zamu rage dogaro ga kasashen turai da sai sun kera ababe saannan mu saya a wurin su kuma da tsada. Hasali ma wadannan naorori da muke saye basu dace da yanayin kasar mu ba. Kunga shi yasa su ke saurin lalacewa sai dole mun koma musu domin neman kayan gyara.
Wannan gwamnati tawa zata bude makarantun kimiya guda uku, biyu na maza da daya ta mata bayan wannan muna da kudurin buda jamiar kimiya da fasaha a shekara mai zuwa domin cigaban yaran mu
Do'stlaringiz bilan baham: |