MUGUN MAFARKI
‘’ Balaraba yaya jikin ina fatar dai da sauki. Domin jiya naga abin ba dama amma yanzu naga har wankin kaya kike’’. Balaraba tace. ‘’To malam yau kam gaskiya kalau nake ji amma gidan nan dai ne hankali na yaki ya kwanta tun mafarkin nan’’. Ke dai balaraba kin faye tsoro kamar farar kura daga mafarki kawai sai ki mayar da abu danzane haba ina dadin haka. Kin ga nima kokari ki ke ki sani cikin wani hali, amma ina ganin abin da zai fi kyau shine ki je gida ki kwana yau. Saboda haka je ki shirya in kai ki gida’’.
‘’Kai Abubakar ni bazan je ko ina in bar gidan nan ba. Duka abin da zai faru sai dai ya same mu anan, amma kamar yadda na fada maka ina da fargaba’’. Abubakar yace to Allah ya kawo mana sauki domin alamarin naki sai addua.
Iskan la’asar na kadawa, itace kuwa suna rausayawa, tsuntsaye suna ta faman shawagi a sama. Wurin yana cike da itacen gwaiba wadanda sun yi yaya duk sun nuna sun yi jazur gwanin shaáwa. Tsuntsayen nan kuwa suna ta faman ci suna kuka mai dadi, kanshi mai dadi yana bugun hancin duka wanda yazo wurin. Ga iskan mai sanyi domin wurin korama ce ta ratso karkashin wadannan itacen gwaiba. Gafen wannan koramar kuwa kwadi ne ke faman kuka wadan sun su kuwa suna ta kokarin kama kwarin da ke kan korayen ciyawar dake nan domin su ci. Tsuntsaye irin su ladin kogi, dake sauka domin shan ruwa kuwa sun dauke wa Zayyad hankali domin kyawon gashin jikinsu, hakan har yasa yayi nisa daga inda iyayen sa suke zaune a gindin wata gwaiba.
Balaraba yau dai sai yi wa Allah godiya domin lallai kin warware, tsoro ya fita gashi kuwa wallahi ba wasa ba kyawon ki kawai nike gani kwanakin nan. Kai na iya zaben mata sai da yi wa Allah hammadala’’. Balaraba ta na murmushi tana kashe wa mijin ido domin dadin kalamin na sa, tana cewa. Kai dai malam baka gajiya da waddannan kalamai naka. Har ka tuna mini da lokacin da kake zuwa gidan mu da laasar, kana jin tsoron iso wa domin kar baba ya kama.
Suna cikin zancen su, sai suka ji zayyad ya kwala ihu. Uwar ta ruga a guje mijin yana a bayan ta, suna isa sai suka zayyad da wani tsuntsu ruwan kasa mai katon kai da manyan idanu yana kallon su. Kai ashe ma mujiya ce ya gani yana kwala ihu hakanan kamar wanda aka cirawa idanu. ‘’To ai kai malam bai taba ganin irin wannan tsuntsu ba kuma kai ma kasan bata da kyawon gani’’.
Yanzu kuwa ai sai mu tafi gida hakanan tunda magariba tana karatowa. Bayan sun isa gida suka kare sallah sa’anan suka ci abinci, daga nan kuma suka shiga kallon talabijin. Abubakar yana zaune kusa da matarsa yana faman gyangyadi har da minshari sai matar ta bashi shawarar cewa yaje ya kwanta a daki tunda kallon ba dolle ne sai yaga fim din da ake na karshe ba. Abubakar kuwa bai musanta ba nan take duka suka kashi wuta kowa yaje ya kwanta. Can da sulisin dare sai matar ta ji wasu abubuwa suna fadowa daga katangar gidan tif-tif, tif-tif. Nan da nan ta tayar da mijin tace da shi ya saurara domin tana jin wani abu da bata taba jin ya faru a gidan ba. Abubakar ya hauta da fada cewar ita dai tsoron tsiya Allah ya yi mata.
Yana cikin fadan sai yaji tsayawar mota a kofar gidan kuma yaji alamar mutane suna tafiyar sanda da murya na magana sama-sama. Hankalin Abubakar ya tashi sai yace.’’ Yau kuwa wane bako muka yi da tsakar dare haka? Amma idan bako ne kuwa ai sai dai ya kwankwasa gida ba dai ya tsallako katangar gida ba’’. Abubakar yana kokarin daukar fitilar hannu sai yaji ana kokarin balle kofar dakin su. Ganin haka ya rarumo wata katuwar kwalba cikin firij da suke sa zuma a ciki, ya labe a bakin kofar yana jiran duka wanda zaya shigo suyi arangama dashi. ‘’Malam don Allah kada ka yi arangama da su, domin da jin haka kasan ba mutum daya bane’’. Jikin balaraba yana makarkata domin tsoro. Abubakar yace. ‘’Ke kiyi shiru kada su ji abin da muke ciki kome ki ka gani kada kiyi wani ihu da zaya sa su san dai dai inda muke’’. Abubakar yasa hannunsa ya ture matarsa gefe daya ta fadi. Tana faduwa zaune chukuma yana balle kyauren dakin da suke ciki.
Shikuwa Abubakar nan da nan ya daga kwalbar dake hannunsa da karfi sama ya faskara ta a kan kafadar chukuma wanda yayi arziki domin saurin kaucewar da yayi da sai bisa kan kafiri. ‘’ kai! Kai! Ya karya mini hannu’’. Emeka yace. ‘’menene chukuma’’? wani abu ya buge mini kafada hannu na ya karye’’. Yana fadar haka sai ya fadi kasa domin zafin dukan ya dimauta shi. Abubakar kuwa yana labe, dama bai kunna wutar dakin ba saboda haka wanda ke wajen dakin ba zai ganshi ba. Yana cikin jiran wanda zai sake kunno kai sai kuwa Emeka ya yi kukan kura ya fada dakin da karfi. Nan take Abubakar ya rarume emeka sama, ya nuna wa Allah ya fyade abin ban za bisa sumintin daki. Dama can abubakar ya yi gasar kokuwa a nan garin yana yaro kuma jarumi ne na gaske.
Shi kuwa chibuzo yana can yana fama da chukuma bai san abin dake faruwa cikin dakin ba. Can sai yaji karar emeka yana neman yadda zai kubuta daga hannun Abubakar, chibuzo yana shiga cikin dakin sai yaji an dambara masa kulli a hanci sai da kansa ya kwallu ga bango nan take ya kwala ihu domin firgitar da yayi shima sai ya fadi yana ganin taurari. Ganin galabar da ya samu akan yan banzar sai Abubakar ya lallabo domin ya lalubo inda matar sa take su fita waje. Cikin haka bai sani ba sai yayi tuntube da emeka sai ya fadi, shi kuwa emeka dajin abubakar ya fadi kusa dashi sai ya danne shi. Ana cikin wannan kokuwar sai chibuzo ya farfado daga suman da yayi sai ya daddafa bango domin ya mike tsaye a cikin haka sai yayi karo da maballin kunna wutar lantarkin dakin nan take ko ina dakin ya haskake. Yana kyalla idon sa sai yaga abubakar ya danne emeka ya makure masa wuya. Chibuzo bai yi wata wata ba sai ya rarumo yar kujerar da balaraba ke zaunawa domin shafe-shafe da ke gaban madubi, zaya dankarawa abubakar a kai.
Ita kuwa balaraba mamaki ya kamata game da lahanin da ta ga za a yi wa mijinta. Ganin haka nan take tayo tsalle kamar damisar da taga maharba zasu halaka mata ‘ya’ya. Nan da nan ba wata-wata balaraba ta kwashe kafafuwan chibozo ta baya ya fadi kasa tif kamar buhun auduga danya, ita ma sai ta haye bayan sa tana ta faman duka kamar Allah ya aiko to. Emeka kuwa ya samu sa’ar juyewa kan Abubakar ya kuwa shake wuyansa yana kokarin kashe shi, ganin halin da mijinta ke ciki sai balaraba ta bar dukan chibuzo ta koma kokarin ta ceci mijinta daga hannun mugun mutum.
Emeka karfi ne dashi kuma ga karfin hali kamar barawon dake sata a gaban alkali. Ganin balaraba tayo tsinke wurin mijinta sai emeka ya fita batun mijinta ya tashi tsaye ya kwashe ta da mari sai da hakorinta ta na tauna ya fado kasa, kafin kace kwabo balaraba ta wuntsile gafe daya tana ganin taurari. Shi kuwa gogan naka chukuma ya farfado dama ba gani yake sosai ba sai yayi karo da balaraba ya fadi a kan ciwon sa sai da ya kwala ihu domin radadin fama ciwon da yayi. Emeka Allah ya bashi galaba a kan Abubakar a inda ya daba masa kulli a idon sa sai da ya galabaita. Nan take suka haye kansa shi da chibuzo suka danne suna ta duka. Ko da matar ta farfado taga halin da ake a ciki sai ta kwatsatsa ihu na neman taimako amma ina, da wuya mutum yaji ana ihun barawo har a kawo dauki sai da mutum ya kara kargame gidansa.
Chukuma yana mikewa sai janyo gyalenta da ke kan gado ya cusa mata a baki domin kada ma aji ihunta, daga nan suka jawo ta da mijinta a tsakar gidan. Nan suka gaya mata cewar idan suka kara jin ihunta zasu kashe ta nan take. Yana kare gaya mata haka sai emeka ya yi fito da baki sai ga wasu mutum biyu sun tsallako katanga, dama dabarar shine su biyun dake waje domin su kula da abin da zai faru ne a waje ko da rana zata baci gare su. Da shigowar su sai suka bankare Abubakar a ka daure hannunsa ta baya, daga nan suka fitar da wata doguwar wuka irin ta yan barno tana faman kyalli idan an haska ta. Balaraba na ganin an fitar da wannan wukar sai ta bude baki zata kwala ihu, bata san lokacin da emeka ya kwashe ta da mari ba sai da bakin ta ya bare da jini.
‘’Idan kika sake bude bakin ki zamu kashe mijinki, yar iska kawai mai taurin halin tsiya’’. Balaraba tace ‘’don Allah kada ku kashe mini miji’’. ‘’Rufe mana bakin ki’’. Inji wanda ke rike da wuka a hannun sa. Ku tambaye shi inda mabudin gidan yake sa anan ya kuma nuna mana inda yake ajiye kudin sa domin munsan akwai kudi masu yawa domin baka dade da karbar kudin kwangila ba. Idan kuwa baka kai cek din kudin banki ba sai ka bamu shi yanzu, ko ka rubuta mana wani domin mu kyale ka da ranka, idan ba haka ta gagara to kayi da tsiya. Abubakar ya amsa ya ce. ‘’bansani ba barayin banza macuta kawai da ba za su samu ceton manzo ba’’. Gaskiyarka zaka san cewar macutan banza muke idan muka kashe ka da matarka, daga bisani mu kone gidannan.
Ganin abin da ke gudana hankalin balaraba ya tashi kwarai, ta roki mijinta da ya rubuta musu wani cek, amma yayi tsaye yace ba hakanan ba domin da ganin su tasan babu jinkai a garesu. Idan ya rubuta musa sun karbama daga karshe kashe su za suyi. ‘’Kai malam don Allah ka tuna da cewar yaron nan zayyad zamu barshi maraya kenen kuma zaya wahala’’. Abubakar ya gaya mata da cewar ai Allah ne ya kudurta haka ta faru, saboda haka shi zai kula da yaron har ya rayu ya zama mai amfani ga alumma idan ya jure wannan wahalar. Chibuzo ya yunkuro a fusace yace malam ka gaya mana abin da zai amfane mu ba waazin ka na banza muka zo nan musha ba. Ina fatar ka fahimci abin da muke nufi bamu da sauran lokacin da zamu bata akan ka. Da balaraba ta matsa wa mijinta ganin kada ranta ya kara bacci a wannan halin sai ya kira wanda ke rike da wukar yace dashi da ya je kan talabijin da ke cikin falon a gefen dama zaya ga mabudin daki, idan ya bude dakin mai gida za ya ga fotfoliyon a ciki zasu ga cek din kwangilar da ya yi bai ko kai shi banki ba, da niyar sa sai gobe.
Bayan an dauko jakar fotfoliyo, nan take a ka yi mata daya-daya suka tabbatar da abubuwan dake ciki daidai suke sai kuma suka shiga kwasar kayan gidan, dama ashe suna tafe ne da motar katako wadda ake kira a hangi biri. Bayan sun sace muhimman kayan gidan sai kuma suka juya kan Abubakar a inda suka danne shi, bakin kato ya darzaza masa wukar nan mai kaifi a makogoro, ko ina ya yi faca-faca da jini kamar an yanka saniya. Ganin wannan bala’i sai balaraba ta bude baki zata kwala ihu amma ina, katon banzan ya toshe mata baki da tsumma, ai kuwa nan take chibuzo ya dankara mata kulli a baya ta fadi. Da faduwar ta kasa sai Chibuzo yace shegiya ta cika surutu amma kaga duka daya ta fadi ta mutu.
Emeka, ganin ta fadi bata motsi sai nan take ya ummurce su da su nemo wani yaro da yaji balaraba da mijin suna fada, wanda ke cikin daki. Bakin kato da ya kashe Abubakar har lahira ya shiga daki-daki amma bai ga zayyad ba. ganin zasu bata wa kansu lokaci har asuba tana batun karatowa har a gane abin da suke ciki sai kowanen su ya fita ya haye mota suka tafi suka bar gidan rufe da balaraba da gawar maigidanta kwance cikin jini.
Kai lafiya wannan yaro cikin daji kai kadai tunda uwar safiya kamar takadari? Da alama gudowa kayi daga gidan ku, yaya aka yi duka jikinka ka kukkuje kamar wanda ya fado akan jaki? Kai! Yaro baka jin magana ne ko kuwa kurma ne ni ke magana dashi? Kai watakila dai wannan yaron dai yaji tsoro ne, Allah dai yasa ba yayi gamo ne da jinnu ba.
‘’Hamza, hamza zo nan ina ganin ga barewar nan da ta tsere.’’ Kai hamisu ai yanzu bata barewa nike ba, domin gani anan da wani karamin yaro da na tsinta a karkashin wannan iccen maje. Hamisu yace. Ai kuwa bamu ga ta farauta ba sai mu koma garin can da muka baro da dare mu kai wa yansada wannan yaron domin su nemi iyayen sa, kada wani naman dawa yayi masa lahani.
Koda mafarauta suka iso gari da zayyad, hantsi ya riga ya fito mutanen gari sun fara kawo da komowa kamar yau da kulum. Mafarautan suna cikin tafiya da zayyad sai su ka hadu da Ibrahim kanin uwar shi zayyad. Mamaki ya kama ibrahim ganin ga dan yayar sa tare da mutanen da bai sani ba kuma gasu rataye da bindigogi da kuma baka. Ibrahim bai warganta ba yace. ‘’Kai malamai lafiya na ganku rike da wannan yaron tunda safe haka? Ko ya tsokane ku ne’’? hamza yace ko kasan wannan yaron ne. E wallahi ni kawun sa ne domin kanen uwar sa nake, kuma ga gidan mu can inda kaga yaran can sun taru. Yana nuna musu da yatsan sa. To samari mun tsinci wannan yaron ne can kusa da tungar buda tun da asuba sakaliya kuma mun yi mishi tambayoyi amma ya kyale mu saboda haka muke ganin babu shakka wani abu ya bashi tsoro da ganin idanun sa watakila ko yayi gamo ne da jinnu cikin dare. Ibrahim yace. To ai sai mu isa gida a sheda wa magabata. ‘’ai tunda ga ka kuma kai kawun sane ba sai munje ba, dama niyarmu mu kai shi ofishin yansanda damin su nemi iyayensa.
Ibrahim ya kama hannun zayyad ya isa gida dashi wajen kakarsa ya sheda mata duka yadda mafarauta suka tsinto shi a daji shikadai kuma gashi baya iya magana kuma baya gane kowa. Mamaki ya mamaye inna Sa’a kakar zayyad game da wannan alamari. Nandanan ta cewa ibrahim da bai ga ta zama ba sai ya ruga a guje yaje gida balaraba ya tambaye ta abin da ya samu zayyad haka. Bayan ibrahim ya tafi ya tambayo game da zayyad, ita kuma inna Sa’a ta shiga lallashin jikanta tana kuma yi masa yan adduoi tana cikin haka sai ga ibrahim ya dawo a guje ya fado cikin daki a rude jikin da yana kaduwa kamar wanda yayi ido biyu da mutuwa zata dauke shi.
Lafiya ibrahim me ya sameka haka ka fado cikin gida babu sallama kamar wanda aka kora. Yaya sakon da na aike ka? Ibrahim wace. Wallahi inna Sa’a abin da ban tsoro’’. Yana fada yana kuka jikin sa na ta kaduwa. Sai tace. ‘’To kayi shiru hakanan kabar kuka, dama nasan halinta idan ran balaraba ya baci. Hala ta koro ka ne ko?’’ ba haka nan ne ba ai duka sun mutu. Sun ye me? Inna an kashe su ne domin na iske gidan......
Inna sa’a ta buga kalmar shahada ta ce yau kuwa sun shiga uku. Kafin kace kwabo gida ya rude ko ina sai kuka kake ji na take maza suka yo dauke domin suji abin da ke faruwa. Ko da aka je gidan Abubakar aka iske gawar sa kwance cikin jini ga matar gafen sa Allah cikin ikon sa ko da aka duba sai aka ga ashe ita tana numfashi sama-sama. Ganin halin da balaraba ke ciki, makwabbacin su nan da nan ya dauko motar sa a inda a ka dauke ta zuwa asibiti ta samu kulawar likita domin a ceto rayuwarta. Bayan likitoci sun yi iyakar kokarin su nan aka samu ta farfado acikin wannan halin kuma sai nakuda ta kama balaraba. Ta haifi ya mace amma bayan yan sa’oi sai ta ce ga garin ku, domin likita ya lura da faduwar da uwar tayi, yayiwa jinjirar rauni mai illa ga zuciya.
Bayan an dawo daga jana’izar Abubakar da jaririya da aka haifa a ka kuma yi dace da hankalin zayyad ya dawo a sakamakon magungunan da likita ya bashi wadanda ke gusar da dimauta. Dattijan anguwa da yansanda suka shiga cikin gida inda inna sa’a take zaune da zayyad da kawunsa domin a tambayi zayyad ko yana da labarin abin da ya faru domin ya taimakawa ‘yansada ga bincikensu kafin balaraba ta samu sauki. Zayyad ya zauna cikin tsanaki yayi bayani yadda barayi suka shiga gidan su cikin dare balaraba ta tashe shi daga bacci kuma ta sheda mishi da cewar ya tsere waje tare da laluba bango lokacin da ake faman damben daure babansa. Bayan ya fito kofar gida sai ya hadu da wani da yake cikin wata katuwar motar katako ya biyo shi da gudu da wuka a hannun sa. Allah ya taimake shi ya tsere amma daga nan abin da yake iya tunawa shine yana cikin gudun ne yayi tuntube da wani kututturun itace ya fadi ya buga kansa a kan wani abu kamar dutse shikenan sai dai da sanyin asuba ya ga kansa kwance a gindin wani baban itace, kuma kanshi yana ta ciwo baya iya bude bakin shi yayi magana. A wannan halin ne waddan mutanen suka same shi.
Do'stlaringiz bilan baham: |